Chapter 1 page 102

224 16 0
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 1⃣0⃣2⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*FATIMA MUHAMMAD SANI (ZarahArkel)*
*HALIMA MUHAMMAD SUNUSI (Barrister S@dy)*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*Hakuri da Juriya Online writer's (HAJOW)*✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Dedicated to *Hakuri da Juriya Online writer's Fans* (Allah bar zumunci da kauna)
Wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin masoyan Association din mu wato *HAJOW*

Hafsat Sallama taje tayiwa Dady ya dibi kudi Mai yawa ya bata Amman taki amsa sai da Mami da Ahmad sukai magana sannan ta amsa tana Masa godiya. Suka fito zasu tafi Basma ta rako su sannan sukai sallama. Washe gari da safe suka daga burin tarayya.



Hakika yaji dadin zuwa da Hafsa Dan kowa kan ya dawo an gama gyara gida an saka turare da yai wanka ya tafi masallaci yana dawowa za a bashi abinci taci ya koshi daga nan zata hau faranta mada washe gari kan ya tafi an gama breakfast an hada Masa ruwan wanka da yai wanka zai ci ya koshi ya tafi aiki kan ya dawo ma haka duk abinda ya kawo Mata zata amsa hannu biyu Tai Masa godiya. Haka suka cigaba da gudanar da rayuwar su a Abuja. Ya kai ta wajen Sakina sun yini Dan Sai da ya dawo ya dauko ta.

Itama Sakinan tazo Mata sau biyu, suna zumuncin su. Watan su daya a Abuja sai dai suyi waya da gida Sam yaki yaje Wanda ita ma tana Masa magana amman sai yace aiki.

Watan su biyu Basu je gida ba Sam Wanda Hannah har ta gaji tana son ta koma dakin ta Dan Sai yanzu ta gane kawayen ta zuga ta kawai suke. Taje gidan daya daga cikin kawayen ta tasamu mijin ta na dukan ta Amman duk da haka biyayya take Masa da kula da shi. Dayar baci ba Sha Amman a haka take zaune tana masa biyayya, dayar auren take so ko da waye amman mijin ya gagare ta matsala kowa da itashi. To Shin ita me mijin ta ya rage ta dashi komai akwai sai abinda ta zaba da anyi albashi xataji alert banda ya kaita shopping duk karahen wata ta siyi abinda take so.

Lallai ta biyewa zugar kawaye sun Kai ta sun baro ta hakika tayi da ta sani da tin farkon auren su ta kula dashi kila ba wani aure da zai Yi yanzu gashi saboda Bata Masa komai ko damuwa da ita bayayi. Ya zatayi.

Mami ta sama tana kuka tana Bata hakuri Mami tace
"Abinda nake so ki gane kenan tinda kin gane zanyiwa Hafsa waya duk yadda za ai suzo gida ni in nace yaushe zai zo sai yai tacewa aiki aiki."

"Nagode Mami."
Bayan sun rabu Mami ta Kira Hafsa kamar yadda suka Saba duk Bayan kwana biyu suna Kiran Junan su, bayan ta Kira suka gaisa Hafsa tace
"Mami ya gidan?"

"Alhamdulillah yaushe zaku zo me?"
"Mami Nima Ina son nazo Amman sai yace aiki Zan Karai Masa maganar."

"To shikenan. Ki gaishe shi."
"Zai ji ina Basma?"

"Ta fita!"
"Agaishe ta in ta dawo da Dady."

"Zasu ji."
Ta kashe wayar bayan sunyi sallama.

Da dare Bayan sun kwanta tace
"Deedat Ina son nai maka magana akan Abu biyu."

Kallon ta yayi yace
"Ina Jin ki."
"Akan matar ka ya kamata ta dawo dakin ta."

"Ni na kore ta in taga zata dawo Bismillah."
"Haba Deedat ya zakace haka duk da ba Kai ka Kore ta ba Amman kayi bikon ta in kana Mata wani Abu Nima fa wata Rana Sai naji zakai iyai min haka."

"No Hafsat ba xan Miki ba itama da dalili."
"To naji kayi hakuri."

"Menene na biyun?"
"Ina son muje Kano Naga Yan gida ko"

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now