chapter 1 page 5

286 22 0
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 0⃣5⃣

*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

Bayan wata daya da neman auren aka aika da kudin komai da za a bukata. Lokacin aka kai lefen Zainab kaya sunyi kyau na rufin asiri an cika mata set din akwatin ta. Aka kawo kayan abinci da kudin kayan dinki. Nan aka basu tukwici da yake maza ne zasu amsa. Sai daga baya Abba ya aika da kayan ciki. Mama sai wani dariya take wai ita a ganin ta kayan basu da yawa.

Bayan sati daya aka kawo na Sailuba kaya ne akwati set biyu an ciki har da kayan bazan da wofi, dan an kashe kudi kamar ba gobe. Umma sai murna take Mama kuwa sai yada habaici take. Umma kam bata san ma tana yi ba dan ita duk daya ta dauki yaran nasu.

Biki saura sati biyu aka kawo lefe daga gidan su Muhammad. Abba sam bai fadawa Mama da kawo kayan ba dan daman maza ne suke amsa, sai da aka kawo aka tafi Abba yasa aka shigo da kayan akai dakin Mama kayan lefen Rukayya ne, dan ko  kayan tukwici Umma, Abba yasaka dan yasan halin Mama yanzu zata iya lalata abin.

Mama ganin ana shiga da kaya ta tsaya tambayar kayan waye? Abba ne ya shiga yace
"Ga kayan auren Rukayya nan, tare zan hada su na aurar."

Nan Mama ta dinga bin kayan da kallon banza dan tin daga kallon kayan ta raina su dan ta tabbata na Zainab ma yafi su yawa da tsada ai fa nan ta hau fada dan me ba a fada mata ba, anje an hada yar ta da dan talakawa, Umma ta fara bata hakuri, amma sai tace
"Rufe min baki ai dake aka hada baki munafuka, kuma Allah ya isa ban yafe ba, tsiya akan ki da ya'yan ki zata kare ba dai ya'ya na ba."
Mama har da Kuka suka bar gun ita da sailuba. Har ta shiga daki ta fito tana fadin
"Ku fitar min kayan daga daki na!"
Ta koma bedroom fuuu.

Abba yace
"Ku kwashe kayan!"
Zainab da Ummulkursum da su Abdullahi su suka kwashe kayan, Rukaya na gefe tana ta kuka.

Abba yace
"Kiyi hakuri Rukayya ki cigaba da addu'a Allah ganar da mahaifiyar ku, Ke dai kiyi biyayya ga mijin ki.'
Su Abba na mikewa zasu fita ta rigasu fita dan tasan in mama ta kama ta dukan tsiya zatai mata.

A dakin Umma aka ajiye kayan suna bubbudawa kaya ne na rufin asiri komai an saka dai dai gwargwado, da kyar ta koma dakin Mama ai kam Mama har daki ta bita tai mata dan banzan duka.  Umma ce ta gasa mata jiki.

Umma ce ta dibar musu kayan da za'a dinka sannan ta siyo musu kayan fitar biki duk su Ukun dan Abba ma ya bata kudi da aka aikawa da sailuba nata sai suka ce basa so sunfi karfin sa. Haka Umma ta bawa Abba tace sunce basa so dan haka Abba yace ta bawa Ummulkursum tace
"A'ah ba za ai haka ba ka kai musu da kanka."

"Ajiye kayan."
Ya fada yana cewa
"Ki turo min Ummulkursum!"
Tan fita Ummulkursum ta shiga nan yace ta debi kayan ya bar mata nan tai tayi godiya sannan ta tafi. Umma bata so haka ba amman ba yadda zatayi.

Umma ita ta dauko mai musu gyaran jiki. A harkar biki Zainab tace zatai kamu da yini mijin ta yace zai dinner dan haka Rukayya ta fadawa Muhammad suma suyi dinner bai boye mataba yace bai da kudin dinner da ta fadawa Zainab sai tayiwa Mijin da zata aura magana yace kar ta damu zai hada musu dukka.

Sailuba kuwa za'ayi bridal shower, kamu, yini, lunching, dinner sam tace bazata ta hada bikin ta da su ba, dan ita duk waje mai tsada aka kama mata. Su kuma anan kwangon Abba zasuyi sai dinner da za a fita.

An kawo kati duk sunyi rabo ga kawayen su sai shirye shirye suke da Zainab ta bawa  Sailuba kati sai cewa tayi ita me zatai dasu. Itama ba basu nata zatai ba. Dan haka ta kyale ta kawai.

Ranar Talata aka fara bikin Sailuba kuma bata sanar da su Zainab ba sai yan uwan Mama da kawayen ta ne kawai suka je sukai biki suka dawo, ranar laraba ma haka, Alhamis ma haka. Sai Alhamis akai kamun su Zainab da Rukyya. amare sunyi kyau cikin wani boyel less mai tsada yellow an kama amare inda aka raba kasko da turaren wuta da humra.

Washe gari Friday akai dinner amare an masu kwalliyyar cikin wani less maroon ita kuma Ummukursum ta shirya cikin Blue kala dan tace bazata sa kaya iri daya da amare ba. A wani event Center sukayi, anyi taro lpy an tashi lafiya ranar asabar akai daurin aure inda da rana Umma tayi yinin ta. Da magariba aka kai amare gidajen su.

An kai sailuba gidan tadake rigiyar zaki gida ne kato Abba yai musu kaya bed set biyu sai falo daya da dining amman Mama sai da ta dada mata da wasu dakuna. Ita kuma Zainab aka kai ta gidan ta dake sharada inda dakunan nan kai da kai da kayan dakin da Abba yai mata. Sai Rukayya dake dan can gaba da unguwar su. Gidan haya ne su uku ne a gidan amman dakunan ta ciki biyu da falo daya dan haka aka zuba mata kayan nata Dole aka juya da dining abba yace a siyar a kai mata kudin ta. Haka kuwa akayi.

Gidan sai ya rage daga Yaya Abdullahi sai Yaa Alkasim sai Khalil, sai Ummulkursum duk gidan sai ya zamar wa Ummulkursum ba dadi, haka ta cigaba da rayuwar ta tana zuwa makaranta dan ma bata da magana da son hayaniya.

Gidan Zainab mijin ta suleiman na son ta, dan haka rayuwa suke mai tsafta da da fahimtar juna suna cin amarcin su cikin jin dadi da kwanciyar hankali kowa na tattalin kowa sam basu da matsala.

Rukayya ma haka abin yake Muhammad na son ta sam bai bata mata sai abinda take so, yake mata kullum yana tare da ita sai yamma zai fita shago yaje ya gaida hajiyar sa, itama tai ta tambayar ina Rukayya dan tana son ta sosai.

Sailuba ma tana zaune lpy tana cin amarcin ta amman sai dai ranar da ta cika sati daya yake fada mata yana da mata har uku kuma nan da gaba kadan zata koma cikin su, abinda ya tada hankalin ta kenan ta kira Mama tana kuka tana fada mata. Mama tace ta kwantar da hankalin ta kar a gida a ji har Umma tai musu dariya sannan tace mata indai da ci da kudi kar ta tada hankalin ta. Wannan yasa ta kwantar da hankalin ta tinda taga mijin nata yana ta tata.

*Na ga comment din ku da kuke cewa a dada wayan rubutun to insha Allah zamu duba in hali ya sanu zakuga kari. Masu cewa a dada kwanaki a cikin kwana biyun da ake shima zamu duba in hali ya samu zaku ga posting. Sai dai abin fa da yawa dan ina posting din wani buk din dan haka ana yin hakuri da yadda aka samu. Ina godiya da yadda kuke bamu gwarin gwiwa sai dai ina mai kara cewa nima a dada yawan comment dan comment din ku shi ke bani gwarin gwiwar ganin na faran ta muku. Taku har kullum Maryama S Inadabwa nake cewa sai mun hadu a cikin wani satin in mai dukka ya kai mu da rai da lafiya. Allah ya sada mu da alheran da ke cikin wannan satin da zamu shiga. Ameen*

FMS!!!

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now