Chapter 1 page 14

317 14 2
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 1⃣4⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*




A nan kuwa su Farisa an samu duniya ita da Hafsa sai yadda suka yi da maza don suma Samira ta koya musu bin malamai inda in sunga duk wanda suke so zasu kai sunan sa sai dai kwanan zancen.

Sakina kuwa itama ta zama yar lesbian sosai don da manyan mata take hulda ta yi kudi cikin ƙanƙanin lokaci inda nan da nan ta zama hajiya yau daga tana waccan kasar gobe tana waccan kasar ko garin.

Auwal ma ya zama ɗan shaye shaye don har da ƴar sata yake tabawa. Saboda zama da su da yake a haka suka koya masa sosai yake shaye shayen sa.

Haule baiwar Allah ita ka dai ce take zaune tana bautar Allah don cikin jikin ta har ya yi wata tara amman bata taɓa zuwa awo ba sai fama take yau lafiya gobe babu lafiya.
Duk wannan abun da ake sam Alhaji bai farga ba.


Su Fauziyya yadda suka dirji junan su ko wasu ma'auratan sai haka. A satin da suka yi ba abinda bata samu ba na daga dukiya da jin dadi sam bata da matsala duk wanda ya ganta da kamal sai ya zata matar sa ce. Don daga shi har ita kamilai ne a fuska.

Baba Jummai mahaifiyar su Fauziyya kuwa da tafiyar saudiyya yazo ta fadawa mijin ya ce Allah kiyaye hanya haka ta tattara kudaden ta ta tafi ba tare da damuwa da ya'yan ta ba.

Tin daga ranar da ya ganta ya fara yi mata magana ta tafi kullum yana layin su sai dai ko kyallin ta bai ƙara gani ba amman duk da haka yana layin nasu.

Satin su biyu sannan suka fara shirin dawowa ana jibi zasu dawo tasa aka yi mata wani dinki a ake mai da mace tamkar budurwa wanda kudi masu yawa Kamal ya biya akai mata. Kwanta ɗaya a asibiti aka sallameta inda suka shirya suka dawo da abubuwa masu yawan gaske wanda bata taɓa zaton samun su a rayuwa ba. Duk da da bata son wannan rayuwar amman a yanzu ta fara jin dadin ta amman fa a zuciyar ta don babu yadda zata yi ne. Kamar yasan da dawowar tata yana daga can nesa da gidan yaga anyi parking da ita ta shiga cikin gidan yaran suka fito suka shigar mata da manya-manyan akwati nan ta. Tana shiga dakin su ba kowa don haka wanka tayi ta kwanta dan ta samu ta huta. Sai dare ta dau wanka zata fita kenan aka aiko akai sallama da ita. A soro ta same shi. Da kallon mamaki da tuhuma ta tsaya, gaisa suka yi tana ci gaba da kallon sa dan ita bata gane shi ba, shine ya fara magana.
"Da farko sunana Muhammad ina nan ƙasan layin kune ina da yar tireda wacce nake ɗan siye da siyar wa. To ni dai..."

Sai yai shiru ɗagowa ta yi ta kalle shi a karo na biyu don har ga Allah ya yi mata kwarjini dogone bashi da jiki yana da hanci da idanu sai dai fuskar sa ba ta da haske amman hannusa da ta kalla sai taga fatar fara tas da ita. Dauke kai ta yi daga kallonsa don ba karamin kwarjini yake mata ba kanta a kasa ta ce
"Kana bukatar jari ne?"

Kai ya girgiza mata ya ce
"A'ah Fauziyya ni ke nake so, don Allah ki taimaka min."

Murmushi ta yi ta kalle shi, kamili da shi a ranta ta ce
"Ina ma Fauziyyan da ce da yau na samu miji dai dai dani amman yanzu ko na aure ka na cuce ka. Ba zan iya ba."

Ɗagowa ta yi ta kalle shi da saurin ta ɗauke ido don wani abu taga yana fita a idon sa yana shiga nata. Murmushi ya yi ita kuma ta girgiza kai ta ce
"Don Allah Muhammad ka yi hakuri."

Tana fadar haka ta shige gida da sauri, ɗakin ta ta nufa ko gaban ta bata gani, tana shiga ta faɗa kan gadonta ta fashe da kuka ba komai takewa kuka ba sai kanta don daga kallo ɗaya taji ta kamu da son sa, ba yadda zata yi saboda in ta yadda ta cuce shi daga gani kamili ne in ta aure shi ta cuce shi sosai. Ina ma bata fada wannan harkar ba da yau ta samu mijin aure amman yanzu ba zata iya ba. Tana wannan halin Farisa da Hafsa suka shigo daga yawon su. Akwatunan da suka gani ya sa suka san ta dawo da sauri suka shiga dakin a kan gado suka same ta tana kuka
"Lafiya Anty Fauziyya?"

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now