Chapter 1 page 81

195 14 0
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 8⃣1⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*FATIMA MUHAMMAD SANI (ZarahArkel)*
*HALIMA MUHAMMAD SUNUSI (Barrister S@dy)*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*Hakuri da Juriya Online writer's (HAJOW)*✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Dedicated to *Hakuri da Juriya Online writer's Fans* (Allah bar zumunci da kauna)
Wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin masoyan Association din mu wato *HAJOW*


Da dare Anty Zainab ta dawo da kayan sannan sukai sallama. Sallah sukai sannan abinci suka ci sannan ta mike ta shiga daki. Wanka tayi ta shirya cikin wasu kayan baccin ta masu kyau. Gajeren wando ne da riga marar hannu sun mata kyau kayan sun kara haska tarure take fesawa ya shigo. Tsayawa kallon ta yayi can kuma ya karasa gaban mudubi ya tsaya ta bayan ta tare da daura kan ta a kafadar ta. Hannun sa kuma ya na kan cikin ta yace
'Kinyi kyau Zuma ta!"

"Nagode!"
Dagata yayi ya zura hannun sa a aljihu ya dauko wani box mai kyau budewa yayi taga sarka ce da dan kunne har da zobe na gold.

"Ummu kin shayar dani abin da ban taba zato ba kin ban komai a duniya ki bani martabar ki shin ni dame zan saka miki?"
"Kai taso na Kawai ya ishe ni."

"Sonki dole ne a waje na Ummu amman ki fadan me kike so bayan shi."
"Ba abinda nake so miji na sai kai kadai."

"Ni naki ne Ummu."
"Godiya nake."

"Ga kyauta Ummu nan bata kai darajar abinda kika ba. amman dan Allah kiyi manage da ita."
Ido ta zaro ta amsa tana fadin
"Wow tawa ce."

Sai ta ajiye ta rumgume shi tana tsalle tare da fadin
"Ya salam!"
Ta dauki sarkar tana fadin
"Nagode Miji  Allah ya kara budi da arziki wannan ya fi min komai Yaa Muhammad!"

Amsa yayi ya dauki sarkar ya saka mata ya dauki dan kunne shima ya saka mata ya sa mata zobe take ta kara kyau ta fara walwalai. Daukar ta yayi yai kan gado da ita. A kan gado ya dire ta yana fadin
"Komai zuma ta ta saka kyau yake mata."

Murmushi kawai tayi ya janyo ta ta shige jikin ta ya fara lallubar ta. Duk da yadda take a tsorace bata nuna masa ba haka ya gama cakudata sannan ya rumgume ta yana fadin
"Zuma ta jaruma ce ina sonki."

Ajiyar zuciya ta sauke. Ya rumgume ta yace
"Muyi baccin mu ba abinda zan miki Zuma ta ki huta kema yau ko?"

Ta kara shigewa jikin sa. a haka bacci ya dauke su basu suka farka ba sai asuba.



*
Bayan sati daya.
A sati dayan da ya wuce ya nunawa Ummu kulawa sosai ga soyayyar sa duk da ba abinda ya kara shiga tsakanin su amman yana bata kulawa da soyayya kullum fadi yake ki kara hutawa Ummu na ranan kin yi kokari.

Tin da ya tafi masallaci bai dawo ba dan yana zuwa training. Sanye take da three quarter da karamar riga tana suya a kitchen kan ta sanye da hula bata ji sallamar sa ba sai kawai jin hannun sa tayi akan kirjin ta. Ajiyar zuciya ta sauke tana fadin
"Yaya na ka dawo?"

Kai ya gyada yace
"Na barki da aiki ko yau na jima!"
"A'ah ai ba wani aiki sosai."

Ta kashe gas din ta juyo ta daura hannun ta a kafadar sa tana fadin
"Muje kayi wanka ko?"

Wani kallo ya kure ta dashi har ta tsargo zata juya yabjuyo da ita yana kashe mata ido daya. Juyawa tayi da sauri tana fadin
"Gaskiya yau ka kaini na gaishe da Umma sannan na debo ya'yana!"

WANNAN RAYUWARDove le storie prendono vita. Scoprilo ora