Chapter 1 page 50

230 17 0
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 5⃣0⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*FATIMA MUHAMMAD SANI (ZarahArkel)*
*HALIMA MUHAMMAD SUNUSI (Barrister S@dy)*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*Hakuri da Juriya Online writer's (HAJOW)*✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Dedicated to *Hakuri da Juriya Online writer's Fans* (Allah bar zumunci da kauna)
Wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin masoyan Association din mu wato *HAJOW*




Yana karasa gida gab da magrib, dan haka yana parking yai alwala sannan ya wuce masallaci yana zuwa ana kiran sallah sai da yayi ya shiga gaba d'aya, har sai da akayi sallah isha'i sannan ya  fito ya shiga gida.

Yana shiga ya tadda su dukkan su a falo. Momy ya gaisar ya nufi dining sai da yaci abinci sannan ya taso yace
"Tashi mu tafi."

"Momy kice ya barni na kwana."
Hannah ta fada.
"Gaskiya ba zaki kwana ba kuma ko kin kwana gaskiya gobe ba zan biyo tanan ba gwara ma kije ki shirya abinda zaki dauka."

Yana fadar haka ya fice. Kallon sa sukai. Momy tace
"Kinga rabu dashi tashi kuje kiyi hakuri kinji. Yan aikin suna nan tafe."

"To Momy nagdoe!"
Suka fita ita da Basma. A cikin mota suka same sa yana shirin tada mota. Tazo ta shiga. Basma tace
"Yaya Aah kyaye to."

"Amim!"
Ya fada ya tada motar ya bar gidan. Suna zuwa gida kan ta fito ya fice ya na shiga direct gefen shi ya shiga ya fad'a toilet, shower ya saki ya dad'e ruwa yana dukanshi ba komai yake tunani ba saina gimbiyarsa ya dad'e a haka Kafin ya fito, kayan bacci ya saka, dan shirin kwanciya, kan gado ya hau ya dauki wayar sa da ya jona a charge.

Sakon ta ya gani yai murmushi sannan ya tura mata da reply kamar haka
"My Love I really miss you, komai na baki u deserve it, so ban son daka yau ki karamin godiya, love you so much!"

Tana kwamce sakon ya shigo bayan ta karanta ta saki murmushi. Ido ta lumshe lokaci d'aya kuma ta bud'e idon tare da kashe wayar dan tasan tsaf zai ce za kira.

Tagumi ta zuba tana me fadin
"Ina son ka Ahmad amman bazan cuceka ba, nasan da kyakyawan zuciya kazo min, rayuwa ta ni abun kyamace ga duk wani namiji mai kishin kanshi, na tabbata rabuwa dakai shine Alheri a tare dani, domin bazan iya fad'a maka wacece ni ba, "
Lokaci d'aya tasa hannu ta goge hawayen da ya zubo mata.

Yana tura text da ya tabbatar ta karanta ya fara  kira, amma sai me? Yaji ance number din a kashe, abun mamaki ya bashi dan yaga deliived report din da yaje. dan haka ya kara kira amma switch off, d'an shiru yayi alaman damuwa, tare da fadin
"Lafiya?"

"Nasan yanzu zai kira kuma in ya kira zai ji ba dadi shin na kyauta masa kenan in sa yaji ba dadi?"
Ta fada a zuciyar ta. Zuciyar tace
"Sam baki kyauta ba ki kunna ko da ya kira ai yaji a kunne yaji dadi ya zata bacci kike baki dauka ba."

Da sauri ta dauki wayar. Kunnawa tayi ai kuwa taba gama oprrating ta hau kara tana dubawa taga shine. To daman wa zai kira in ba shi ba. Ta fada a ranta.

"Assalamu alaikun!"
Ta fada murya a sanyaye.

Ajiyar zuciya ya sauke yace
"Wa'aialkum salam Baby na bacci kika fara ne na tashe ki?"

"Wallahi har na kashe wayar zan kwanta nace kada ka kira kaji kuma a kashe."
Murmushi yayi yace
"Amma naji dadi dan kuwa yanzu na gama kira naji a kashe amman na kasa hakura."

WANNAN RAYUWARDonde viven las historias. Descúbrelo ahora