Chapter 1 page 23

248 9 0
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 2⃣3⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*********************************************************************************************************************************
Haka ta cigaba da zawarci ganin Alhaji Kasim yafi wadan da ke son ta kashe mata kudi sai ta fara sauraron sa. Ba abinda baya bata ko ya siya mata. Nan ta fara jin dadin itama zatai auren gidan dadi. Uwar ta kuma tana mai yar wa da Umma habaici.

Ummu kuwa bata san wainar da ake toyawa ba. Abba dai ya fadawa Yaa Suleiman da Anty Zainab inda yace su kula da ita. Duk da service take a lokacin sauran wata uku ta gama. dan har DE ta siya zata juya masters.

Lokacin da ta gama. kan ta juya masters tace sai taje gida. Haka ta tafi wa da Yan gida tsaraba kala kala.

Zo kuga murna wajen Umma ganin yar tata dan daga gani suna lafiya gashi ta kammala degree har zata fara master. Ita dai sai godiyar Allah ya'yan ta suna cikin rufin asiri da wadata. Nan ta dinga fitar da tsaraba har da Mama da yayen ta. Da tace zata gidan Rukky ne aka fada mata auren ta ya mutu. Har da kukan Ummu.

Da dare tana daki a kwance Abba ya aiko Khalil akan ya kira ta.
Mikewa tayi ta saka hijab ta nufi gun Abba dake falon sa. Zama tayi bayan tai sama sannu.

Kallon ta yake cikin so da kauna dan duk cikin ya'yan sa tafi kowa hakuri ladabi da biyayya. Magana ya fara yace
"Allah yai miki albarka Ummu a duk cikin ya'yana ina alfahari dake saboda yadda kike min ladabi da biyayya, dan haka ganin na isa dake yasa na yanke hukunci akan ki kuma ina fatan zaki min biyayya."

Kanta a kasa ta rasa me mahaifin nata zai fada mata, gaban ta kuwa sai faduwa yake yi, nan ta daure ta amsa masa da
"Insha Allah!"

"Allah miki albarka ni nasan daman Uwa ta zata amshi abinda na zaba mata. Ba komai bane sai na daura miki aure da *mijin yayarki.* Ina fatan zaki min biyayya sannan kiyiwa mijin ki biyayya."

Duk da abin ya zo mata a bazace bata taba kawo wa da haka ba amman sai ta daure tace
"Insha Allah Abba Nagode!"

"Allah miki Albarka, ya baku kema masu miku biyayya Allah ya baki zaman lafiya da zuri'a mai albarka."
"Ameen Abba!"
Ta fada kanta a kasa.

"Tashi ki tafi Allah miki albarka!"
Ta mike ta fice ta isa daki. Ko ba a fada mata ba tasan da Yaa Mohammad aka daura mata aure. Abinda Abba ya fadamata sam bataji tana bakin ciki ba haka nan bata ji tana farin ciki ba. Sai dai tunanin ta ya tafi a tayaya Yaa Muhammad zai amshe ta.

Shin shi yana son tane ko kuwa? Ina tasan Anty Rukky yake so. Allah sarki shikenan ita ba zata aure zabin ranta ba sai Zabin Allah da zabin iyayen ta. Ba yadda zatai sai dai tana addu'a akan Allah yasa Zabin Allah da Iyayen ta ya zamar mata zabi na alheri wanda zatai alfahari dashi. Ta saka a ranta cewa zata yi biyayya ga mijin ta insha Allahu.

Sai washe gari Umma take fada mata ba yanzu zata tare ba sai Muhammad ya dawo daga karatun da ya tafi taji dadi sosai da hakan.

Kwanan ta biyu taji zaman garin ya ishe ta dan ba Rukky kuma ba Jannah dan haka ta fadawa iyayen ta suka amince dan sun san zata fi nutsuwa acan da samun kulawar yayarta.

Data koma ta samu Anty Zainab ta fada mata nasiha Anty Zainab tai mata sosai daga nan ta cire komai a ranta. Ta koma makarantar ta inda ta fara karatun ta ta samu aikin a wani private hospital take zuwa weekend tana cankasar albashin ta sai dai ta turawa Abba da Umma ko tayi alheri ga yan uwan ta. Dan har lokacin Yaa Suleiman shi ke mata komai.

Muhammad kuwa yana yawan kiran Abba su gaisa dashi dan so yake ya amshi Number Ummu amman yana jin nauyin tambayar Abba. Wata rana da sukai waya da Abba bayan sun gaisa yake cewa
"Abba ya mutan Abuja?"

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now