Chapter 1 page 33

257 17 1
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 3⃣3⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*
*

***
Zaune suke a falo suna hira. Yaa Suleiman da Anty Zainab sai Ummu. Yaa Suleiman ne ya kalli Ummu yace
"Amarya ki rubuta duk abinda kike so dan a fara tanadar miki bai fi wata uku ba mai gidan ya dawo ko?"

Fuska ta boye a tafin hannun ta. Yai murmushi yace
"My D kiyi total na bada kudi kan wani month din akara siyowa. Dan Ummu kamar 'ya tace ni zan mata komai. Abba yai min kawaici akan ta sosai."

Murmushi Anty Zainab tayi tace
"An gama Oga. Allah ya kara budi."

"Amin My D. Dazu ai munyi waya da Muhammad din. Kullum sai yai min godiya da yadda na rike Ummu. Haka addu'ar sa bata karewa ga Abba dan yace ya dauki Abba amatsayin uban da ya haife shi dan ya masa abinda bai taba zato ba yaso shi ya bashi ko wacce dama. A yanzu ne yace shi kuma lokacin da zai saka masa insha Allah."

"Allah sarki Muhammad kenan kullum maganar sa kenan karamcin Abba. Haka Shi Abba yake ya fison ku ma akan mu."
Anty Zainab ta fada.

Gwalo Yaa Suleiman yai mata yace
"Yeee mun kwace musu Abba."

Dadiya Ummu tayi tace
"Mun bar maka tinda muna dakai."

Yai dariya yace
"Tinda kuna dani ba kuyin kukan komai."

Murmushi tayi tace
"Allah Yaa Suleiman na dauke a matsayin uba ji fa abinda kake min. Ni ban maka kallon Yaya domin kamin komai ba abinda zance sai dai Allah yayi tukwici da gidan Aljanna. Allah ya biya ka ya bani ikon faranta maka kamar yadda kake mana Ni da Iyayena da Anty nah."

"Kar ki damu ai nauyi nane "
Ya fada yana murmushi. Haka suka cigaba da hirar su har goma kowa yayi daki dan ya kwanta.



*
Yadda Muhammad yake yawan kiran Ummu da kulawar sa a gare ta sai yake burgeta tana jin dadi dan in har bai kira ba har shiga damuwa takeyi. Wasa wasa dai sun shaku da junan su. Dan ma Ummu akwai kunya in yana mata wasu maganganun ji take kamar ta nitse sai tai ta mamaki daman haka Yaa Muhammad yake.

Ita kam Anty Rukaiyya mai ya kaita rabuwa da wannan mutumin mai mutunci,  sanin ya kamata,  hankali,  nustuwa,  ilimi tana mamaki dan ya iya soyayya tin a yanzu ina ga mutum yana tare dashi.

Ido ta lumshe tana mai fadin
"Kaddarar su kenan. Allah ka daura mana abinda zamu iya. Ina fatan mutuwa ce zata raba ni da miji na. Allah ka ban ikon yin biyayya a gare shi da Iyaye na."

A hankali ta hude idon ta. Dakin ta kalla sai kuma Mike a hankali tayi ta shige bandakin dakin ta. Wanka tayi ta fito daure da Alwala. Tana fitowa ta shafa turare ta saka kayan baccin ta. Kan gado ta hau ta dauki hisinun musilim tana karantawa.

Karar wayar ta taji ko bata tambaya ba tasan ba mai kiran ta a wannan lokacin sai Muhammad wannan yasa ta gyara zama sannan ta dauki wayar ta kara a kunnen ta.
"Yan mata nah!"

Ido ta lumshe tace
"Uhmm Yaya nah ina yinI?"

"Lafiya Alhamdulilah ya ckul din?"
"Alhamdulillah!"

"Anyi fixing time table din ne?"
"Eh nan da one week zamu fara exam with in two week mun gama dan ma sun saka mana interval."

"Masha Allah ana ganawa sai ki zauna jiran Ango kenan!"
"Hmmm!"

Ta fada kawai. Murmushi yayi yace
"Da ina tunanin kan na dawo ki tare amman menene shawarar ki?"

"Yaya na duk yadda kace yayi ai."
Ta fada tana kwanciyya duk da bata so hakan ba.

Murmushi Muhammad yayi yace
"Yan mata nah kina burge ni da wannan saukin kan naki. Da wasa nake. Zan var ki ki huta wato nima na dan yi sati sai mu tare ko?"

WANNAN RAYUWARUnde poveștirile trăiesc. Descoperă acum