Chapter 1 page 84

182 15 1
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 8⃣4⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*FATIMA MUHAMMAD SANI (ZarahArkel)*
*HALIMA MUHAMMAD SUNUSI (Barrister S@dy)*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*Hakuri da Juriya Online writer's (HAJOW)*✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Dedicated to *Hakuri da Juriya Online writer's Fans* (Allah bar zumunci da kauna)
Wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin masoyan Association din mu wato *HAJOW*


Ana idar da isha'i ya koma waya yai mata bata jima ba ta fito ya kalle ta yace
"Kinyi sallah?"
"Nayi;"

"Me kika roka mana "
Murmushi tayi. Shuma yayi yace
"Kenan baki min addu'a ba. Dan ban kai matsayin ba ko?"

"Ba haka bane Kabir ai kana da matsayi mai girma a waje na ka min abinda ko wani dan uwa na bai min ba abinda masoyi ne kawai zai min bayan nan kana bani kulawa da son ganin farin ciki na kaga kuwa dole ba baka ."
Yai murmushi yace
"Wacce iri kikaii min?"

"Nace Allah buda maka ya baka mace tagari mai son ka ya baka farin ciki yasaka gama da duniya lafiya."
Ido ya lumshe yana murmushi yace
"Nagode sosai. Kema Allah baki abinda kika nemar min."

Tai murmushi tace
"Nagode"

Baba ne ya dawo yai parking motar sa. Gaban Halima ne ya fadi duk da tasan Kabir ba saurayin ta bane amman tasan zata sha fada in ta koma. Ga mamakin ta da yazo zai shiga sai taga Kabur ya karasa da sauri ya durkusa yana gaishe shi.

Hannu ya mika masa abinda ya bata mamaki sosai kenan ta tsaya tambayar kan ta anya wannan kuwa Baba ne. Har suka gama gaisawa Kabir ya dawo ta bishi da kallo.

Yai murmushi yace
"Baba ya dawo ko? Ya kamata ki koma gida."
Ya bude mota ya dauko kayan ciki ya mika mata yace
"Gashi ba yawa. Ki kula da kan ki. Allah kara sauki."

"Amin nagode sosai Kabir Allah saka da alheri ya kiyaye hanya "
"Nagode sosai Halima sai da safe."

Ta juya ta shiga ya bita da kallo sannan ya juya ya shiga mota ya bar wajen.

Tana shiga ta ajiye kayan da ya bata ta bude tana kallo. diba tayi ta bawa Umma da yaran sannan ta debi nasu ta kira Hajara da sakina da Hafsat suka ci bayan sun gama ta koma daki ta kwanta.

Yana komawa daki ya shige sannan ya wuce da ya kwanta yana lumshe ido. Allah ya daura shi akan mahaifin Haima yace nan da sati biyu ayi auren. Ido ya bude yaba fadin
"Allah ka mallaka min Halima da Sadiya."

Waya ya dauka ya fara neman layin Halima har ta kwanta taji jarar wayar ido ta bude ta dauka Kabir ta gani sai ta saki murmushi dan yadda yake bata kulawa tana jin dadi sosai.

Ta dauka ta sa a kunne tana fadin
"Sannu ka koma gda lafiya?"
"Alhamdulillah daman na kira naji kin shiga gida lafiya."

Tai dariya tace
"Lafiya lou yasu Mami?"

"Suna lafiya."
"Masha Allah."

"Me kike?"
"Ba komai na kwanta zan bacci ne?"

"Kace da wuri kike bacci!"
"To me zanyi?"

"Hira mana!"
"Da wa?"

"Samarin ki!"
"Hmm Kabir kenan ai ni yanzu ban da samari dama can ba kula su nake ba bare yanzu. Isma'il ne kadai kuma  kaga yanzu bama tare."

"To shikenan ki bani labari!"
"Wanne iri?"

"Akan ki."
Tai dariya tace
"Ni har wani labari ne dani. Ban da kawa jo daya fa."

WANNAN RAYUWAROnde histórias criam vida. Descubra agora