Chapter 1 page 21

265 11 0
                                    

WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 2⃣1⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*Barka da Sallah! Allah ya amshi ibadun da mukayi a cikin watan ramadan ya yafe mana. Allah maimaita mana cikin aminci ya kawo mana karshen wannan annobar. Marasa lafiya na gida da na asibiti Allah ya basu lafiya, mu da muke da ita Allah ya kara mana lafiya, wadan da suka riga mu gidan gaskiya Allah jikan su kai musu rahama mu kuma Allah yasa mu cika da kyau da imani. Amin. Yan matan mu Allah basu miji na gari tare da bazawarawa, masu mazaje Allah kara musu zaman lpy da kaunar juna. Amin.*

*Happy Eid Mubarak to all musulmin Ummah!*

Fauziyya na shiga gida ta fada dakin ta ta kara fashewa da wani kukan lallai ta bata rayuwar ta shin meyasa bata amshi kaddarar da ta same ta bayan afkuwar komai ta koma ga Allah ba? Sai ta cigaba da sabawa Allah.
"Innalillah wainna illahir rajiun! Shin da na mutu ina mai aikata zina fa? Lallai da na kasance asararriya  ta zo duniya a banza za ta koma a banza. Na kasance ƴar wuta."

Ido ta runtse tana mai daga hannun ta sama tana fadin
"Astagafurillah wa atubu'illaik! Ya Allah ka gafarta min ka yafe min ka yafe min don darajar Annabi Muhammad (SAW) Allah ya yafe min ka shirya ni ka yafen min! Astagafurllah! Astagafurullah!! Astahagafurullah!!!"

Abinda tai ta yi kenan don sam bata cikin haiyacin ta tsoron duniya da tsoron azabar Allah ta sa ta shiga tashin hankalin da bata taɓa shiga ba. Tana halin nan kanin ta Al amin ya shigo mata da kayan da ta bari a soro ko ta kansu bata bi ba. Bandaki ta shiga ta dauro alwala sannan tazo ta hau kan sallaya tana mai kai kukan ta ga rabbi samawati wal'ard akan ya yafe mata ya jikan ta ya shirya ta.

Haka tai tayi tana mai fadin astagafurullah har akai magariba ta mike tayi a sujadarta ta jima tana kai kukan ta ga Allah akan Allah ya yafe mata ya shirya ta ya tsare ya'yan al umma. Tana idar wa ta dauki Alkur'ani ta fara karantawa ko ta samu sauki yadda zuciyar ta ke mata azaba na radadin halin da ta tsinci kan ta a ciki. Wato ita tata kalar kaddarar kenan? To Allah ya bata ikon cinyewa ya shiryata.

Ranar bata kara samun nustuwar ta ba sai kai kukan ta ga Allah da take tana da na sani da nadama akan abinda ta aikata da kuma yin alkawarin ba zata sake komawa halin da ta shiga a da ba.
(Toh Allah yasa Fauziyya)

***************************
Ahmad ne zaune a gaban Dadyn sa. Dady ya kalle shi ya ce
"Yaya dai Ahmad?"

Kan sa a ƙasa ya shagwabe fuska kamar zai kuka ya ce
"Dady ji nayi wai Momy ta tsaida biki na?"

Dan Murmushi Dady ya saki ya ce
"Haka ta fada min."

Hannun Daddyaa ya kama ya ce
"Please Dady ka yi wani abu akai wallahi sam ni bana son Hannah akwai wacce nake so!"

Kallon sa Dady ya tsaya. Idon sa ne ya kawo ruwa, Dady yace
"To menene na kuka kai fa namiji ne mijin mace hudu ba zan ce a'ah akan maganar aure nan da mahaifiyar ka ba zance kai mata biyayya amman ka sani nima zan maka abinda kake so domin nima kana min biyayya. Kaje ka fara shirin bikin ka da Hannah bayan auren ku ni na yi maka alkawarin zan shige maka gaba ka auri wacce kake so kaji."

Kai ya gyada yace
"Yanzu kai mata biyayya kamar yadda ka saba Allah maka albarka."

"Amin Dady nagode!"
"Yaushe zaka tafin ne?"

"Ranar Monday zan koma!"
"Ok Allah ya kaimu!"

"Amin!"
Tashi yayi ya nufi bangaren Momy. A falo ya same ta tana kallo shiga yayi ya zauna a gefen ta ya daura kan sa a kafadar ta.

Murmushi Momy ta saki tace
"Ka dai kusa girma ka daina wadan nan abubuwan kai ba Auta ba ko Basma bata abinda kake!"

Fuska ya shagwabe tace
"Me kake so to?"

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now