Chapter 1 page110 End

303 20 3
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 1⃣1⃣0⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

Zaune take a falo waya Kare a kunnen ta tana fadin
"Haba Deedat mu da muke son da muje gidan Mami muyi sati kan mu taho."

"What har sati ma zaku Kara lallai Kam kina son ki ganni yanzu a Kano ko?"
"No Deedat Dan Allah ka Kara Mana ko kwana biyu ne bamuje wajen Mami bafa."

"me kuke yau?"
"Yau hutawa muke jiya sai dare muka dawo fa."

"Kinga yau kuje gidan ku gaida Mami gobe ku taho."
"Haba dai my love yau Kuma mu taho gobe please ka Kara mana kwana daya jibi mu taho."

"Na Gama Baby. Kinsan a halin da nake Wai? Wallahi am badly missing you Dan Allah ki tausaya min."
Yana fada ya kashe wayar.

Wayar tabi da kallo sai ta girgiza kai tana Fadin
"Shi Deedat haka yake sai kace bashi da wata matar."

Ta fita falo ta samu yaran tace
"Ku tashi mu tafi gidan Mami."

A guje suka fice suna fadin
"Yee zamu wajen Mami."

Suka fita. Mota ta shiga suka shiga wasu baya, sannan suka fita. Tana shiga tai parking suka fita a guje suna fadin
"Granny Granny!"

Ta fita, tana murmushi. Kan ta karasa duk sun Dane Mami. Tace
"Lalalah menene haka."

Duk mikewa sukai. Mami tace
"Ku kyale su Dan Allah in Basu hau kai na ba kan wa zasu hau haba nice kadai fa wata Rana in bana nan fa gwara su moren kwana nawane Zan tafi."

"Haba Mami ba dai yanzu ba."
Murmushi Mami tayi ta zauna tana fadin
"Ina yini?"

"Lafiya ya gida ya taro da Yan uwan ki?"
"Alhamdulillah!"

"Masha Allah. Yanzu me gidan ya Kira yace wai ki tafi gobe."
"Yanzu muka Gama waya Mami naso muyi Miki sati fa, Wai gobe ni wallahi so nake ko zuwa jibi ma."

"Yayi min magiya Dan Allah ki tafi goben ki tafi."
"Shikenan Amman ko gidan Basma banje ba fa."

"Kije kiyi booking flight din in yaso sai kuyi tafiyar yamma ko? Da safe sai kuje gidan Basman."
"Shikenan za'ayi hakan."

Haka suka yini washe gari sukaje gidan Basma da safe itama da Yar ta mace Yar Shekara uku. Tana da karamin ciki. Karfe biyu suka koma gida suka je suka dauki abinda zasu dauka hudu da kwata suka tashi.

Suna sauka yazo da kansa Dan daukar sa. Sai da Hafsat tayi mamaki da yazo da kansa Dan tasan ya matse kan sa ne kawai.

Yaran na hango shi suka karasa aguje suka rumgume shi suna fadin
"We miss you Dady."

"Miss you more My kids."
Ya dago Yana kallon Hafsa da ta tsaya kallon su ya sake su ya karasa wajen ta Yana fadin
"Na gane Daman ke ba wata kewa ta da kike."

Tace
"Saboda me kace haka?"
"Gashi Nan ko welcoming nawa baki ba, sannan kalli fa sai wani Shan kamshi kike Yi."

"Kai Deedat! Na gaji ne kawai."
"Muje na sauke Miki gajiya Dan abinda nazo nai Miki kenan."

Dan hararar sa tayi, tayi gaba suka bi Bayan sa shi da yara. Tana zuwa ya bude Mata ta shiga ya rufe ya saki murmushi tana girgiza kai.

Yara suka shiga baya ya koma ya tada motar suka fice a wajen. Suna shiga gida suka samu Hanna da yaran ta biyu a compound ana parking suka bude mota suka karasa wajen Yan uwan su a guje Suma suka rumgume juna.

Hanna ta karaso tana fadin
"Welcome sis."
"Thank you ya gida?"

"Alhamdulillah we miss you."
"Haba dai."
Yaran suka yo wajen ta a guje suna fadin
"Momy we miss you."

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: May 18, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now