Chapter 1 page 42

241 20 3
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 4⃣2⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*FATIMA MUHAMMAD SANI (ZarahArkel)*
*HALIMA MUHAMMAD SUNUSI (Barrister S@dy)*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*Hakuri da Juriya Online writer's (HAJOW)*✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Dedicated to *Hakuri da Juriya Online writer's Fans* (Allah bar zumunci da kauna)
Wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin masoyan Association din mu wato *HAJOW*



Ummu ce zaune gaban ta peppersoup ne da Anty Zainab tai mata sai wani cup da aka markada kankana aka zuba mata madara da zuma.

In kaga Ummu yadda tayi haske ta kara cika fatar ta kamar ka taba jini ya fito tayi kyau sosai dan tin da ta gama exam ba inda take zuwa ta dauki hutu a gun aikin ta. Kamshi na daban jikin ta ke fitar wa saboda tsumin turaren da ake mata da gyaran amare

Bowl 🍜 din da pepper soup din ke ciki ta ja ta fara ci kamar bata son taci. Anty Zainab ce ta shigo hannun ta rike da cup 🍵 wanda ta tsumi ne a ciki sai tashin kayan kamshi yake. Tana ganin Anty Zaunab ta bata fuska tace
"Amman Anty ni ina zan kai dukka wadan nan?

"Cikin ki kuma na fada miki har romon ki shanye shi tas kinji ko?"
Fuska Ummu ta bata tace
"So kike na zama narkekiya ko?"

"A'ah so nake kawai ki rikita Muhammad!"
Kai Ummu tayi kasa dashi. Anty tai murmushi ta ajiye tace
"Ki maza ki cinye mai gyara na nan zuwa."

Fuska Ummu ta kara batawa bata ce komai ba. Kadan taci pepper soup din sannan ta dauki hadin kankanar ta sha ta ajiye. Ji tayi cikin ta yayi masifar cika har kirji dan haka sai ta dauke tsumin ta ajiye a karkashin gado sannan ta rufe sauran papper soup din ta fita da cup din da ta gama dashi. Dauraye shi tayi sannan ta ajiye a mazaunin sa.

Daki ta koma ta fara cire riga dan wanka zatayi sai jin wayar ta tayi tana kara dauka tayi taga mai kira sai ta saki mumushi ta kai wayar kunnen ta.
"Assalamu alaikum!"

Ta fada cikin muryar ta mai dadi da kwantar masa da hankali.
"Wa'alaikum salam My wife ya kike ya gida?"

"Alhamdulillah ya kake?"
"Lafiya. Ya shirye shiryen tarbar mijin ki?"

Murmushi tayi tace
"Ni ba wani shirye shirye da nake?"
"Really?'

Ya tambaya shiru tayi yace
" kenan ni ba aji dani da ba za ai min shirye shiryen tarba ta na ko? Ni kam nan ina nan ina ta dauki da Allah Allah jibi tayi na taso. Ni kam wane irin bakin jini gareni yayar taki kanwar ma ga alama nan."

"Kai Yaa Muhammad ni na fada maka bana son ka."
"Ga alama nan!"

"Wannan ba alama bace ka dawo mana mu xauna a gida daya anan zaka shaida da abinda ni bazan iya fada maka ba!"
"Saboda me?"

"Kunyar ka nake ji."
Murmushi yayi yace
"Ummu kenan. Acan din ma kunyar ce zata hana ki ki min abinda zai sa na tabbatar. Ki saka a ranki da zuciyar ki ni mijin ki ne kuma sirrin ki wanda baki da kamar sa to daga nan zaki samu ki saki jikin ki dani. Dan Allah a dan rage kunyar nan kada ta cutar da mijin nan naki. Ni ban da buri da ya wuce nazo naga Ummu na kwana nake mafarkin ki na yini tunanin ki ina son ki Ummu ban san lokacin da son ki ya gama cafke min zuciya ta. Nai miki alkawarin faran ta miki a ko wanne hali Ummu. Abba uba ne a guna wanda lokacin da ya banke ban yi zaton zan so ki ko zaki kula ni ki amshi auren mu. Sai abun ya ban mamaki duk da nasan wacece ke sam halaiyar ki ba irin ta Rukayya bace. Ke yarinya ce mai hakuri da nutsuwa da amfani da ilimin ki. Tin ina auren Rukayya nasan da wannan lokacin da xaki kira kina ban hakuri akan abinda tai min banda zuwa gaishe da Hajiya ta da kai mata alherai ni kai na baki kyale ni ba haka nan yar mu yadda kike sonta da yiwa mahaifiyar ta nasiha. Ummu tin a lokacin na fara jin wani abu a tare dake da na rasa ko na menene. Daga baya da na zauna na fara wadan nan tunanin naji na kara aminta dake da nustuwa da auren da Abba yai  min dake. Ta bangare na baki da matsala dan sai abinda kike so zan miki dan haka ki kwantar da hankalin ki Ummu. Ina sonki a cikin zuciya ta. A kwanakin nan na fara wani tunani wallahi Ummu tin kan na ce ina son Rukayya a rayuwar mu kike burge ni da ban sha'awa saboda yadda kike daban a cikin yan gidan ku. Sai da na auri Rukayya take kara bani labarin kyawawan dabi'un ki. Hakika ke macen da za ai alfahari da ita ce. Kuma Allah miki albarka ya bani ya'ya masu irin dabi'un ki Amin. Ina son ki ummu har ban son iya adadin sa ba. Wallahi ban tabai wa wata ko wani irin son da nake miki ba a yanzu. Ina son ki Ummu kece hasken idaniyya ta."

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now