Chapter 1 page 66

212 14 3
                                    


*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 6⃣6⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

Cikin gida suka dawo Hafsa ta shiga daki wayar ta tagani tana haske tana dubawa taga Ahmad ne dauka tayi tai sallama yace
"Ina kika shiga ne ina ta kira!"

"Wallahi na fita naje gun Halima ne!"
"Ohk ya jikin nata?"

"Da sauki!"
"Allah kara sauki!"

"Amin"
"Daman zan fada miki gani nan karasowa! Zan zo naga my princess naga ita me takara sannan in amshi amsa ta."

Murmushi tayi yace
"Toh Allah kawo ka lafiya."
Yace
"Amin nagode! Kin shirya kenan"

"A'ah!"
"In nazo ma kya shirya ai."

"Sai ka karaso."
Ta fada yace
"Ok!"

Mai fruit ya sama ya siyawa Halima da yawan gaske sannan ya tada mota ya nufi gidan su Hafsa yana mai jin wani farin ciki da dadi na ratsa dukkan jikinsa da zuciyar sa.

Yana kashe wayar ta mike ta canja kaya sannan ta zauna kirjin ta na dukan uku uku tunanin ta tayaya zata amshi soyayyar sa in taki kuma menene dalilin ta.

Tana zaune wayar ta, ta hau kara dauka tayi ta duba taga Ahmad ne dauka tayi yace
"Ina kofar gida!"

"Ok!"
Ta mike ta saka hijab sannan ta shafa turare ta fito. Umma ta sama tace
"Umma nayi bako bari naje mu gaisa."

"To a kiyaye dai."
"Insha Allah!"
Sannan ta fita. Yara ta gani suna shigo da bugun dankali da doya sai kayan marmari.

Kanin ta Lukman yace
"Yaya ke akace mu kawowa!"
"Ni kuma inji wa?"

"Yana waje!"
"Ok!"
Ta fada tana basu hanya sannan ta shimfida masa darduma ita kuma tayi waje. Tsaye ta ganshi jikin motar sa ya zubowa kofar gidan ido yana hango ta ya saki murmushi sannan ya fara takun sa mai kyau da nutsuwa yayo kofar gidan.

Sam bata san ya karaso ba, sai ganin sa tayi a gaban ta ba karamin kunya taji ba ta juya tayi ciki yabi bayan ta. Zama tayi a can karshen dardumar sannan shima ya cire takalmin sa ya zauna.

Kanta a kasa tace
"Ina yini?"
"Alhamdulillah ya kike?"

"Alhamdulillah!"
"Ya me jikin?"

"Da sauki!"
"Allah kara afuwa!"

"Amin!"
"Uhmm ina jin ki?"

Dagowa tayi ta dan kalle shi sai karaf suka hada ido. Kai ta dauke da sauri yai murmushi yace
"Ashe ke barauniya ce."

Da sauri tana kallon sa. Yce
"You stole my heart!"
Wata ajiyar zuciya ta saki yace
"Haka ake kin dauke tawa amman kin ki bani taki biyu ta miki yawa ki taimaka ki ban taki zan kula miki da ita fiye da yadda zan kula da tawa."

Bata san lokacin data sake wani murmushi ba tare da lumshe ido. Shima murnushin yake Yace
"Hafsa na fada miki ban taba soyayya ba kece the  first girl dana taba cewa ina so kuma kece macen da na taba  zama da fadawa ina so har nake bin ki kina gudu na. what I know is that your love change me har nake abubuwa ba tare da na sani ba. Wanu lokacin cin naji sam in ban ganki ba kamar zan mutu ne. Hafsa i love you son da ban san dashi ba da ban yadda da wani abu so kamar haka ba saibyanzu a yanzu ina jin I can do anything just to have you."

Hafsa jin maganan Ahmad take har cikin ranta da duka gangan jikinta, takan rasa mai yasa take jin sonsa da kaunar sa a ko da yaushe tana ganin sa daban a cikin mutane domin tana ganin shi yafi sauran samarinta, ita dai tasan zuciyar ta, ta riga ta kamu da sonshi ne, amma shine kadai yake magana da ita taji bata son ya Bari sannan takan sami nutsuwa Idan suna waya, takan rasa mai yasa ko wace kalma Indai ya fito daka bakinshi take jin dadinta ba, ta rasa dalilin hakan ga wani irin kwarjini da yake mata Sosai. Ba zata iya kin Ahmad ba domin yayi in ya tafi waye zai zo mata bata sani  amman kuma in suka aure ya same ta ba a yadda yai tsammani bafa?.......

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now