Chapter 1 Page 36

241 19 1
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 3⃣6⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*
*


Tana shiga dakin ta samu Mama zaune a falon ta. Zama tayi a kasa tana fadin
"Mama ina yini?"

"Lafiya lou. Me zan samu ne?"
"Mama ni ban da komai dan yaushe rabon da na fita ma."

"To meyasa baza kije ki samo ba. Itama Fauziyyan naga yanzu ta daina fita. Daga Farisa sai Sakina da Halima da Hajara ke nemo mana kudi amman ku biyun nan kun daina fita to saboda me?"
"Mama mu makaranta ma zamu koma."

"Waye zai dauki nauyin karatun naku?"
"Mu mana."

Tsaki Mama tayi tace
"Allah bada sa'a."

"Ina Halima?"
Hafsat ta tambayi Mama.

"Tana daki!"
Mikewa tayi tai cikin dakin. Mama ta bita da kallo.

A kwance ta samu Halima. Halima na ganin Hafsa ta mike zaune. Hafsa ta zauna a gefen ta tana kare mata kallo. Gani tayi tayi kiba da ita har sheki take yi ga yadda ta cika kamar me. Wannan yasa Gaban Hafsa ya fadi domin suma fara bin mazan su duk sunyi irin wannan kyan.

"Zauna mana Anty Hafsa."
Halima ta fada. Zama Hafsa tayi tace
"Ya jikin?"

"Da sauki."
"Allah kara sauki."

"Amin amman ya naga..."
Sai kuma tayi shiru tace
"Ina kike zuwa yawon barar ne?"

"Kasuwa da wajaje."
Kallon ta Hafsa ta tsaya yi tace
"Daga yau kada ki kara zuwa barar nan ki san yadda zaki ki daina dan ba girma da mutuncin ki bane ki zauna bakin da Allah ya tsaga ba zai rasa abinda zai ci ba kinji ko?"

Kai ta gyada tace
"Amman kinsan Halin Mama ko?"

"Ba tana riga ku fita ba da ta fita kar kuje in ta dawo kuce baku samo komai ba."
"Shikenan!"

Dakin Hafsa ta  fara bi da kallo idon ta ya fada akan ledar da aka kawo mata fruit yanzu. Ledar ta janyo taga abubuwa a ciki tace
"Wannan fa?"

"Abokin saurayi na ne ya kawon kayan dubiya."
"Saurayi kuma a ina kuka hadu?"

"Kasuwa!"
"Da gaske yake?"
Hafsa ta tambaya.

Kai ta gyada tace
"Yazo gun Baba ma amman bai bashi dama ba wai nayi yarinya."

Kai Hafsa ta girgiza tace
"Allah ya kawo mana karshen *wannan rayuwar* ta cikin gidan nan. Daman Baba ba yadda zai ba tinda ko babbar mu Anty Fauziyya bai yadda ba bare kuma Yaya Saki da Yaya Farisa."

"Nima na fada masa haka amman yace zai jira har lokacin da Baba ya yadda."
"Ya dabiun sa suke?"

Gaban Halima ne ya yanke ya fadi ciki inda inda tace
"Yana da hankali da nutsuwa Hajara ma ta san shi"

Kallon ta Hafsa take tace
"Shikenan ki rike mutuncin ki dai kada ki soma nuna son abun duniya."

"Insha Allahu!"
"Yanzu ya jikin kinje asibiti?"

"Jiya yazo munje har da Hajara."
"To Allah kara sauki kina shan maganin."

"Insha Allah."
Ta mike tana fadin
"Bari naje ana  kiran sallah magariba kema ki tashi kiyo alwala kizo kiyi sallah."

Mikewa tayi suka fita tare sukai alwala kowa yayi daki. Mama kuwa tana ganin fitar su ta dinga harara Hafsa tana fadin
"Kin kwaso halin Jummai dai kin koma dakin ta sai kace ita ta haife ki."

Halima da ta shigo taji Mama na maganar bata tanka mata ba ta shige daki tana fadin
"Mama ke da ba halin ki ba bayan duk girman kine yaran gidan."

Hafsa na shiga daki ta fara tunani rayuwa wai yau Mama ke nuna baa son su karo karatu gwara su na yawo su samo kudi bayan sam tasan Mama bata da son kudi kamar kishiyoyin ta. Ko da yake *Wannan rayuwar* ta cikin gidan su ta isa ta sa Mama son kudi ko ta halin yaya ne.

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now