Chapter 1 page 15

308 15 0
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 1⃣5⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*
*

Har tayi arbain bata da shirin komawa. Dan tace ita tafi jin dadin zaman gidan Abba kuma ya zuba musu ido dan yace baza su saka masa hawan jini ba. Da Muhammad yazo ma Hakuri Abba ya bashi yace ya zuba musu ido. Da yaga zata doshi wata hudu a gida ne yace ta hada kayan ta, ta koma dakin ta. Mama tace ba inda zata da taga Abba ya dau zafi dole ta amsa da toh. Amman Mama tace ta hada kayan ta ta tafi gidan Sailuba.

Daga can ma gidan Anty Zainab taje tai sati biyu, da taje taga a daular da suke sai zuciyar ta ta kuma kwadaita mata son kudi. Dan ko bngaren Ummu ya fi gidan auren ta. Ga Ummu na karatu ta kuma wayewa sai ta fara danasin itama karatun tayi ba aure ba. Danasani dai kala kala. A ranta kuwa ta saka ba zata kona gidan Muhammad ba. Da zata tafi Yaa Suleiman ya bata 50k Zainab ta bata 10k da kayan sakawa sababbi nata da na Baby Jannat. Ummu ta bata takalma da jaka. Sannan ta koma gidan sailuba

Muhammad ganin shiru shiru har wajen wata shida ba Rukkaya ne yasa ya tafi gun Abba. Abba yai mamaki dan gani yake ai tafi wata biyu da komawa dakin ta.

Cikin gida ya shiga wajen Mama, yace
"Binta ina Rukayya?"

"Tana gidan ta mana!"
Mama ta bashi amsa.

"Binta bana son rainin hankali ina Rukayya? Ga mijin tanan yazo yace bata koma ba. Ina kika kai ta"

Ganin Abba ya riga yasan bata nan ne tace
"Kaga Alhaji, ana dole ne?  ba'ayi ko? To dan haka Rukayya batayi dan haka ka shaida masa ya saketa in ba haka ba wallahi har kotu sai munje an raba wannnan kaddararen aure."

Abba cikin mamaki yace
"Abinda kuka zaba kenan?"

"Eh!"
Ta bashi amsa.

"Shikenan Allah ya bada sa'a!"
Ya sa kai ya fita. Mama ta hau mita daman ai shi ya cuci yar ta ya hada ta Muhammad amman ita Zainab ya bata miji mai kudi. Ni kam nace sai kace ba dariya akewa zainab din ba a da.

Abba ya samu Muhammad a daki ya kalle shi yace
"Muhammad kayi hakuri ina son ka hakura da Rukayya ka bani takardar ta, dan yanzu abinda suka fada min ko baka sake taba zasu kai karar ka kotu ba zan mata dole ta koma dakin ta ba dan nasan sam ba zakaji dadin ta ba."

Kan sa a kasa ya kasa magana Abba yace
"Amman in kaga kana so aje koto ni zan tsayaa maka."

Kai ya girgiza yace
"A'ah Abbah! Zanyi yadda kace!"
Ya mike yana fadin
"Nagode Allah ya saka da alheri."

Abba yace
"Zauna kaji!"

Zama yayi Abba yace
"Alhamdulillah. Allah ya sani ina son ka a matsayin siriki na dan haka ba zan so na barka ka bar wannan zuri'ar tawa ba. Alah yaso ina da wata yarinyar in har kan kawon takardar sakin Rukayya ka turo magabatan ka zan baka auen Uwata Ummu!"

Wata faduwar gaba Muhammad yaji  amman ya danne yace
"Nagode Allah saka da alheri."

Ya mike ya tafi a ransa sam ba zai iya bijirewa bukatar Abba ba.
(Shin me kuke ganin zai faru Muhammad zai auri Ummu kuwa? Need more comment here.)



******************************************************************************************************************************************************************************************************************************************************************

Dagowa tayi tana kallon almajirar tace
"Wacce wannan? 'Yar kice?"
Dariya tsohuwar nan tayi tace
"Bani da 'ya ko daya, nice nan!"

Zabura Fauziyya tayi. Almajirar nan ta ce
"Da farko sunana Na'ima, ni kadai ce wajen iyaye na. Sunan mahaifina Mal Alhassan da mahaifiyar ta Hadiza. Mahaifi na bai da kudi ko kadan dan yar buga buga yake yi ko dan faskaren itace dashi yake samo mana na abinci duk da haka ya tsaya tsayin daka akan yaga ya inganta rayuwar mu bama tawa wato nayi karatu a halin da muke ya sanya ni a makarantar gwamnati kuma kome aka nema zai nemo ya kai sai dai Mahaifiya ta ita kuma bata da hakuri da dangana dan duk kokarin da mahaifina zaiyi bata taba ganin yana komai duk da bamu da rashin ci wanda ita kullum burin ta taga munyi kudi.

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now