Chapter 1 page 41

250 19 1
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 4⃣1⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*FATIMA MUHAMMAD SANI (ZarahArkel)*
*HALIMA MUHAMMAD SUNUSI (Barrister S@dy)*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*Hakuri da Juriya Online writer's (HAJOW)*✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Dedicated to *Hakuri da Juriya Online writer's Fans* (Allah bar zumunci da kauna)
Wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin masoyan Association din mu wato *HAJOW*



Karfe tara ya iso soron gidan. Wani yaro ya gani zai fito yace
"Abokin na dan Allah kaje kacewa Baba ana sallama dashi a waje."

Bai jima ba yaron yazo yace
"Wai yace inji wa?"

"Kace masa Muhammad ne."
Nan yaron ya koma. Tare da Baba suka fito Baba yana ganin sa ya washe baki yace
"Ashe kai ne bismillah."

Suka shiga ciki. A falon Baba ya zauna a kasa. Kan sa a kasa yace
"Ina yini?"

"Lafiya Alhamdulilah ya Manyan?"
"Suna Lafiya."

"To Madallah."
Kan Muhammad a kasa yace
"Baba daman nazo tafiya da Fauziyyar ne."

Baba yace
"Ai ba matsala bari na saka a kira ta sai ku wuce."

Nan Baba ya mike ya fita yana kwalawa Yaya Babba kira
"Sa'adatu! Sa'adatu!! Sa'adatu!!!"

Yaya Babba dake daku ta fito da sauri tana amsawa da
"Na'am Alhaji Lafiya?"

Ganin har ya koma daki yasa ta shiga. Ganin bako a zaune ta samu waje ta zauna. Muhammad kan sa a kasa yace
"Ina yini Baba?"

"Lafiya lou!"
Ta amsa tana kallon mai gidan nata.

"Wannan mijin Fauziyya ne. an daura dauren goma da suka wuce daman munyi dashi zai zo ya dauke ta to Allah ya kawo shi. Ki shiga ki kira ta sai tazo su tafi."
Kallon Alhaji ta tsaya yi baki bude yace
"Baki ji bane?"

"Naji Alhaji Amman ai da ka fada tin wuri an kintsa ta ko? Kuma ai ya kamata muma mu rakata muga gidan nata ko?"
"Ke zaki fadan abinda zanyi. In ba zakije ki kirata ba sai ni naje da kai na."

"Allah baka hakuri."
Ta mike ta fita tana jimamin abun. Dakin ta ta shiga ta tadda Halima da Hajara na zaune tace
"Ku taso kuje kuyiwa Yayar ku sallama zata tafi."

"Ina?"
Suka hada baki suka tambaya a tare. Mama tace
"Gidan mijinta."

Da mamaki Halima tace
"Gidan mijin ta kuma yaushe aka daura auren."

"Hmm yanzu Alhaji ke fadain. Anyi sati ba da daura auren amman ya kamata dai ya fada mana a dan mata wani abun ko?"
"Gaskiya dai!"
Hajara ta fada.

Mikewa sukai suka karasa dakin Umma. Fauziyya da Hafsa zaune a daki duk sunyi jugum jugum bama Fauziyya da zuviyar ta ke ta bugawa. Hafsat kuma jimamin kewar yayar ta take.

Mama ta shiga dakin da sallama tana fadin
"Fauziyya! Alhaji ne yace nazo na fto dake za a tafi dake gidan mijin ki."

Hafsat ce ta rumgume Fauziyya sai suja fashe da kuka haka Hajara da Halima suka taho suma suka rumgume su suna kuka rabuwa. dan duk gidan Fauziyya ba ruwan ta kowa nata ne tana son yan uwan ta.

Sun jima suna kukan Mama na tsaye tana kallon su itama sai taji duk babu dadi dan haka tace
"Ku taso an bar yaron acan fa."

Kasa mikewa Fauziyya tayi. Tana kuka ta tunanin rayuwa. Wai daman haka ake aure ba yan war uwar ta bare na uban ta. Bama wannan ba uwar ta na da rai amman ji bata san a halin da suke ba. Tana can yawon duniya. Oh ita kam taga rayuwa. *wannan rayuwar* sam batai mata ba.

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now