Chapter 1 page 97

146 13 0
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 9⃣7⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*FATIMA MUHAMMAD SANI (ZarahArkel)*
*HALIMA MUHAMMAD SUNUSI (Barrister S@dy)*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*Hakuri da Juriya Online writer's (HAJOW)*✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Dedicated to *Hakuri da Juriya Online writer's Fans* (Allah bar zumunci da kauna)
Wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin masoyan Association din mu wato *HAJOW*

A gida Kabir kuwa Sai da aka kai Halima sannan aka kai Sadiya wanda haka ya nuna Halima ce uwar gida. Sai wajen sha daya ya shigo gidan. Daki Sadiya ya fara shiga tana zaune a gefen gado. Ta yaye mayafin tana sakar masa murmushi tare da gaishe sa  ya amsa yana fadin
"Barka da zuwa gida."

"Nagode amma bani aka fara kawowa ba."
Kai ya gyada yace
"Nazo naga lafiyar ki sannan na kawo mili kaza kici ko?"

"Nagode!"
"Kiyi hakuri Sadiya."

"Haba miji na ba komai Allah bamu zaman lafiya."
"Amin!"

"Amman kayi kyau angon mu nima ranar da zaka zo min irin wannan shigar nake so."
"An gama amaryata amman ai kin fini yin kyau."

"Anya kuwa kagan ka kuwa?"
Yai murmushi yace
"Kada dai ki fasan kai."

"Ai gaskiya ce."
"Hmm to nagode."

Tai murnushi  yace
"Tin da rana daya aka kawo ku,  za a raba kwana zuwa kwana bibbiyu ba sai anyi sati sati ba yayi?"
"Ka je mata da maganar in ta yadda ba matsala."

"Shikenan sai da safe ko?"
"Allah bamu alheri."
Ya mike ta taso ta rakashi har ya fita ta maida kofa ta rufe daki ta koma sai taji shaidan na son mata huduba da sauri tayi addu'a ta zauna taci naman ta ta koshi sauran ta saka a firijn sannan ta shiga ta wanke bakin ta tai wanka ta fito ta saka kayan bacci ta kwanta taba addu'a.

Yana shiga bangaren Halima ya rufe kofar. Sannan ya nufi dakin da take. Nan yaga ba kowa. Ajiye ledar hannun sa yayi ya mike ya juya zai fita ta fifo daga bandaki dan ita ta gaji da jira ta zata ma ba zai shigo mata ba tinda ance su biyu ne kila yana wajen dayar. Dan haka sai ta tsaya cak ganin sa a dakin ya juya mata baya  gaban tane ya hau dukan tara tara.

Kallon sa ta tsaya yi. ta zubawa bayansa ido, tundaga kan kwantacen gashinsa har zuwa kafarsa. Bata san lokacin da ta furta
"Woaw ba. Taba fadin shin wannan shine miji na?"

Shima jin bude kofar shi ya tsayar dashi. Jin shiru kuma yasa ya juyo,  toxali yayi da iya tsaye a bakin bandakin tai masa kyau  wani irin murmushi ya sakar mata. Halima ta nuna sa da yatsa tace
"Kabir kaine? Kai ka rako angon nawa to yana ina?"

Bai ce mata komai ba in banda murmushi da yake yi, gaban Halima ne ya dinga bugawa da sauri da sauri sai ta fara leke ta ina zata gano angon nata bayan nan me yasa ya bar Kabir ya shigo har dakin auren su ko dan bata da daraja. Ganin baya gano kowa ba gashi ba mayafi a jikin ta yasa ta juya zata koma bandakin da sauri yace
"Halima."

Ya kirata da voice dinsa mai dadin sauraro.  Cak ta tsaya tayi saurin juyowa tana kallon sa, yace
"Ba sai kinje ko ina ba. Nine dai mijin ki Kabir da kika sani ninr mijin ki?"

Kai ta hau girgizawa tana fadin
"Joke aside please waye miji na duk sunki su fada min kai nasan zaka fada nin."
Murmushi yayi daya kara fido da zahirn kyaunsa, ya taka ya je gabanta, hannun ta ya kamo ya shigo da ita dakin ya zaunar akan gado.

"Ki yadda dani Halima kamar yadda kika yadda dani to nine mijin ki. Nine!"
Da sauri ta mike ta fara ja da baya,  hawaye na zubo mata tace
"No is not possible u cant be my husband!"

WANNAN RAYUWAROpowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz