Chapter 1 page 52

231 20 2
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 5⃣2⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*FATIMA MUHAMMAD SANI (ZarahArkel)*
*HALIMA MUHAMMAD SUNUSI (Barrister S@dy)*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*Hakuri da Juriya Online writer's (HAJOW)*✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Dedicated to *Hakuri da Juriya Online writer's Fans* (Allah bar zumunci da kauna)
Wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin masoyan Association din mu wato *HAJOW*



Hafsa na shiga daki ta dauki wayar da Ahmad ya bata wanda yanzu ita kadai take kunnawa dayar tana nan a kashe. Missed call ta gani ko ba a fada ba tasan ba me kira sai shi.

Murmushi tayi tana girgirza kai sai kuma ta fara neman layin Anty Fauziyya. Ringin daya, biyu aka dauka.
"Assalamu alaikum!"

Fauziyya tayi sallama.
"Wa'alaikun salam. Anty Fauziyya ina yini?"

"Hafsa lafiya kou ya kuke ya gida dasu Umma da Baba da kannena? Na ta kiran wayar ki a kashe dan Allah ki kunna ina neman ki muna gaisawa ina jin yaya kuke kinji?'
"Kai Anty Fauziyya duk missing din mu kike ni gani nake duk wanda ya bar gidan mu ba zai kewar sa ba saboda *wannan rayuwar* da muke ciki a cikin sa."

"Haba Hafsa duk lalacewa gidan mu gidan mune kuma dole nayi tin kaho da alfahari dashi. Da ace ban da iyaye fa. amman kowa yanzu yasan gidan mu da iyaye na da kanne na. Kuma alhamdulillah ba wanda zai ce ga wani abu da muka aikata ba mai kyau ba ko?"
"Haka ne. To ya kike ya gida da amarci?"

"Alhamduliah. Ina Umma,  Halima,  Hajara da kowa dai?"
"Duk suna lafiya. Halima ce ma bata dan jin dadi."

"Subhanallah me ya same ta?"
"Zazzabi ne."

"Ya salam. Dan Allah a kai ta asibiti. Ina fatan dai ba wata matsala a gidan ko?"
"Gida na nan yadda kika san shi."

"Allah taimaka to."
"Amim! Ina Yaa Muhammad!"

"Ya fita yanzu amman zai dawo."
"Agaishe shi to..."

Sallamar sa ta jiyo daga waje ta amsa tana fadin
"kinji dan halak ko?"
Kan ta rufe baki ya shigo yana fadin
"Baby ba oyoyo ko? In koma kenan!"

"No am answering call ne."
Ta fada tana mikewa. Ta rumgume shi tace
"Sannu da zuwa."

Yai kissing dinta yace
"Yauwah ya gidan!"

Waya ta kara masa a kunne Hafsa tace
"A gabana kuke soyayya ko?"

Kallon Fauziyya yayi yai mata alamar tambayatace
"Hafsat ce."

Yai murmushi yace
"Au kada muyi?"

"A'ah Yaya kuyi abarku. Ina yini?"
"Lafiya lou 'kanwata ya kike ya gida? Kullum sai an kira  ki wayar ki a kashe yau dai kin ga dama.kin kunna ta kira ki ko?"

"Ni na kira ta ai!"
"Ba wani nan ita ce ta damu dake amman ke baki damu da ita ba."

"Kai Yaya wallahi nima ina ta missing nata ka dauke min Anty na."
Dariya yayi yace
"Soon kema wani zai daike ki but kan nan sai mun fara daike ki."

Tai murmusbi yace
"Ya mutanen gidan ina fatan komai dai lafiya."
"Alhamdulillah."

"Masha Aah agaida kowa."
"Zasuji nagode."
Ya mikawa Fauziyya waya. Amsa tayi tace
"Sister ya xancen guy din nan kuwa."

"Anty Yaya na ya dawo a kula dashi anjima zan baki labarinsa."
"To amman ki kunna wayar ki."

"Ai na canja sim shine ya kawon waya."
"Da gaske?"
Ta tambaya cike da farin ciki. Sannan tace
"Abu dai na ta tafiya ko? Ina fatan kin fada masa?"

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now