Chapter 1 page 11

268 23 1
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 1⃣1⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*



Karfe biyun dare taji ana shafata abinda yasa ta bude ido da sauri kenan. Wanda ya kawo ta gidan ta gani mikewa tayi tace
"Mu tafi ko?"

Idon sa dake a kankance tsabar jaraba ya bude yace
"Ina?"

"Gida!"
Ta fada a shagwabe. Fuskar ta ya shafa yace yanzu karfe biyu har da rabi ba ki bari sai gobe dazu nazo ina ta tashin ki baki tashi ba."

Kai ta gyada tana matsa karshen gadon biyo ta yayi tace
"Dan Allah kayi hakuri wallahi wajen da zafi."

Tausayin ta yaji amman kuma a bukace yake da ita. Yace
"To naji amman ki Sani ba zan miki komai ba amma duk abinda nasaki kiyi min zaki min kin yadda."

Nan ta gyada kai Dan tasan azabar da take ji a wajen har yanzu. Dole duk abinda yace tayi take masa duk da ba a son ranta take ba shi kam sai ihu yake a haka har ya samu yayi releasing. Amman fa kirjin ta kamar ya cire Dan ja bakin ta kuwa saboda kiss har zafi yake mata.

A haka bacci ya kwashe sa yana kanta itama Bata San lokacin da baccin ya dauke ta ba sai asuba sannan ta farka, ta shiga tai wanka ta Kara gasa jikin ta tafito ta tada shi tayi sallah. Tana zaune ya tashi ya shiga yai wanka ya fito daure da towel. Kai ta dauke. Ya fita tana zaune hade karfe bakwai ta mike ta fita a falo ta same shi. Kallon ta ya tsaya yi tace
"Ka kaini gida."

"Tin yanzu?"
Kai ta gyada masa.
"Zo nan!"
Ya fada yana nuna mata gefen sa karasawa tayi ta zauna. Ya ce
"Bari ki karya sai in kai ki gida kinji."

Kai ta gyada masa yana zaune ya mike ya shiga daki aransa Sam baya son ta tafi amman zai mata abinda baza taba rabuwa dashi ba. Wani Katon akwati ya janyo ya fito falon da shi. A gaban ta ya ajiye ya bude yana fadin
"Sauko kiga kayan sun miki ko a canja su."
A ranta tace wai kai baka San na tsane ka bane. Ko da yake ba laifin ka bane laifin Mama ne da tasa a kawoni nan. Yanzu Mama da kanta take son na koma karuwa. Sai hawaye ta hau zuba a idon ta.

Yana gani yace
"Haba Sugar menene ko bakya so fada min abinda kike so, gida kike so ko mota ko hajji zan kai ki fada min."
Shiru tayi ya mike ya shiga daki ya dauko bandir din kudi yan 1k guda hudu yazo ya ajiye su hannun sa dayan rike da kwallin wata sabuwar wata da a lokacin ta fito kasuwa ya ganta ya siyo mata. Ajiye mata yayi yace
"Nasa ayo min order motoci da sunzo daya taki ce. sannan akwai gidaje na da ake karasawa a rijiyar zaki in kin dawo zamuje ki zabi Wanda kike so."
Duk yana mata haka ne Dan gobe ta dawo. Yace
"Ga waya nan da number in kina bukatar wani Abu. Yanzu daga yau sai yaushe."

Shiru tayi ya ce
"Gobe inzo in dauke ki."
Dan ya kyale ta tace
"Eh."
Dai dai lokacin da akai knocking Kennan ya mike ya amso abun ya dawo ya bude musu chips ne da farfesun kayan ciki sai fulas din tea ya hada mata ya tashi ya bar ta a gun Dan ta sake taci. Ai kam ta danci Dan tana Jin yunwa bai fito ba sai sha biyu saura kuma taki ta koma daki tana zaune Dan tace bazata koma daki ya fita ta Kara kwana a gidan ba.

Kayan ya dauka yace
"Tashi muje."
Ta mike tabi bayan sa. Shi ya bude mata mota ta shiga ya zaga ya shiga suna hawa titi yace
"ina zamu?"

Fada masa tayi da aka zo unguwar ta dinga masa kwatance har sai da yazo kofar gidan sannan ta fito. Shima fitowa yayi ya mika mata da kayan yana kallon ta kasa kasa yace
"Sai gobe?"
Kai ta gyada ta juya.
"Uhmmm please Fauziyya take care kinji."

Haushi ya zo kirjin ta amman ya zatayi ya gama cutar ta Dan haka kai kawai ta gyada ta shige gidan. Dakin su ta shige ta fada gado ta sha kukan ta sannan bacci ya dauke ta.

Sai yamma su Hafsa da Farisa suka dawo Hafsa da kaya Niki Niki sai uban kudi da suka samo suka shige daki. Fauziyya suka samu tana bacci suka kalle ta suka sheke da dariya. Nan suka zauna suna maida maganar jiya da abinda ya faru. Abinda ya tada Fauziyya kenan.

Kallon su tayi sukace
"Sannu da zuwa Anty Fauziyya."
Batace kala ba. Farisa ce tace
"Me kika samo mana."
Ta janyo akwatin tana budewa tare da zaro ido tace
"Gaskiya ne Wallahi Anty Fauziyya ai daman ke daban ce irin wannan kyau da diri ai kila har da kujerar hajji aka hada miki."

Tsaki tayi ta tashi zata fita kallon tafiyar ta Farisa tayi da yake Farisa ita idon ta a bude yake tin kan ta fara bin maza yasa ta ce
"Kai sai na gyara ki Anty Fauziyya kalli tafiyar ki. Hafsa jeki dauko min ruwan zafi."

Dawowa tayi ta kwanta Farisa da Hafsa suka hada mata ruwan shiga hade da maguguna suka sa taje ta gyara jikin ta sai taji dadin jikin ta. Wani magani Farisa ta Bata guda uku daya na wankin mahaifa daya na Karin ni'ima da Wanda zai tsuke ta Bata San na menene ba tasha nan suka Samar musu abinda zasuyi.

Fauziyya ce ta dauki kudin wajen ta dubu dari ta basu tace
"Kuje ku siyo kayan abinci duk abinda Babu a siyo shi."

"Sai Hajiya Anty Fauziyya."
Suka fita komai sai da suka siyo bugun shinkafa guda hudu sannan taliya Katon biyar mai, macaroni, indomie, magi, gishiri har gas suka siyo a gidan. Sannan suka dawo nan da nan aka daura abinci a gidan yaran sai murna suka.

Sakina kuwa tana can Habee ta dauke ta zata kai ta gidan wata uwar dakin ta. Wacce wani gida ne, Katon gaske da sukaje Hajiyar Babba ce Dan ance Kawar matar gwamna ce ma haka suka zauna ta sallama Habee ta rike Sakina tace zata kai ta gida da kanta.
Wannan yasa duk abinda akai Bata gida. A jiya da Yaya Babba ta dawo taga Babu Hafsa tace tana ina sai akace Bata nan sunje unguwa da Farisa gidan yan uwan Maman ta. Wannan yasa tayi shiru.

Dukkan su wayoyin su suka kashe Dan Fauziyya daman Bata bude wayar ta ba. Suna zaune wajen isha'i sai ga Yaya Babba nan ta shigo tana kiciniyar daura abinda za'a amma sai ta tarar da abincin ta ma. Nan ta zauna tana mamakin inda aka samo abincin. A gajiye ta dawo da yara Dan haka tara nayi tai bacci inda sai a lokacin Jummai ta dawo tana shiga dakin ta ta hau washe baki. Mikewa Fauziyya tayi ta shige daki Dan bata son kallon fuskar Mahaifiyar tatama Dan komai da ya faru itace sila.

Kallo Mama ta bita dashi tana girgiza kai. Farisa ta ce
"Hajiya Mama Allah yayi albarka kinga arziki kuwa. Arziki na bin mu Ashe muna gudun sa."
Nan suka dinga Bata labari tana ta dariya da murna nan Farisa ta Bata dubu dari sannan tace ga abinda Yaya Fauziyya tayi nan sai ga Mama na fada wai dan me zata karar da kudin ta har dubu dari ita take da hakkin ciyar da yaran gidan ko me.

Haka ta tashi ta shiga dakin da Fauziyya ta shiga tayi fadan ta tagama sannan ta fito Fauziyya ko kallon ta batai ba. Suna zaune akayi kiran Farisa ta tashi ta tafi Bata Dade da tafiya ba sai aka Kira Hafsa itama ta tafi. Mama sai murna take tana jiran taji Fauziyya ta fito ta tafi taji shiru wannan yasa ta leka daki sai ta tadda ta tana bacci ma.

Tsaki tayi tace
"Shegiya mai bakin halin tsiya."
Daga haka ta wuce daki ta kwanta ita man.

Hafsat da Farisa kam sun kama kasuwanci sosai suke bin maza inda acikin sati daya har sun kware da harkar kamar ba farin shiga ba.

Kullum Kamal sai ya Kira Fauziyya wayar a kashe Dan haka yau ana magariba ya Iso unguwar sallama yasa akayo masa da Fauziyya lokacin Farisa zata fita tace
"Muje muga waye?"

Tana zuwa taga Kamal 'Babban Alhaji. Nan suka gaisa yace
"Ina ta kiran Fauziyya wayar ta a kashe Lafiya kuwa?"

"Lafiya lou! Kasan Yaya Fauziyya sai a hankali halin ta daban ne. Amman kar ka damu zan hada mata abun da sai ta neme ka."
"Nagode kanwata."
Ya debo kudin da baisan adadin su ba ya Bata. Ta amsa ta tafi shima haka.



*Toh makaranta littafin _wannan rayuwar_ anan zan tsaya na wannan satin ina fatan a cikin labarin mu dauki darasin dake ciku mu watsar da dabi'un banza. Nagode da kauna da kulawar da kuke bani akan littafin nan. Ina jiran comment dinku dan comment yayi kasa*

*Nagode taku har kullum _Maryam S Indabawa (Antty)_ nake cewa sai mun hadu wani makon in mai dukka ya kaimu.*

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now