Banda salati da sallallami babu abinda suke anan ne innar Jameel ta basu labarin halakar dake tsakanin Jameel da *SAFNAH*kuka sosai *SAFNAH* take Jin Jameel Dan uwan tane.

Shikuwa murna da farin ciki baxasu misaltu agunsa ba, Dan gani yake kamar burinsa ta gama cika.

Bangaran afeeya da *NASIR*kuwa gani suke kamar halakar su zata iya samun matsala Dan Haka kallo daya zaka musu kasan cewa suna cikin matsanan cin damuwa.

Tashi*SAFNAH*tayi ta rungume inna wato mahaifiyar Jameel tana kuka Mai cin rai rarrashin ta tashiga tare da bubbga bayan ta.

Saida komai ya lafa ,sannan Inna suka yiwa iyayan afeeya da iyayan *NASIR*godiya kan dawainiyar da sukayi da *SAFNAH*

"Babu Komai mom tace .

Shikuwa kawu hassan Wanda ya kasance kani ne ga mahaifin *NASIR*cewa yayi," babu komai yiwa kaine domin kuwa muma munzu da namu rokun irin ne.

Dago Kai Jameel yayi cikin sauri idon sa akan kawu Hassan jira
Yake yaji abinda zaice da Kuma amsar da innar sa zata bayar.

Da murmushi afuskar innar jameel tace," ai kunfi karfin rokon komai agon mu, domin kuwa mun riga mun zama daya.

Murmushi kawu Hassan yayi yace,"muna godiya da irin karamcin da kuka nuna Mana ALLAH ya kara zumunci.

Suna cikin haka alhasan ya shigo Wanda kanin innar Jameel ne Wanda suke uba daya,Zama yayi Inna tayi masa bayanin halin da ake ciki.

Cikin sakin fuska sukayi musabaha sannan ya bukaci Jin abinda suke nema agunsu.

Murmushi kawu hassan yayi yace,"to dama dai bawani abubane I'lla auran *SAFNAH*da muke nemarwa danmu *NASIR*farin ciki sosai Inna da maimuna sukayi gabaki daya gidan duk Wanda ka kalli fuskar sa zaka tabbatar Yana cike da farin ciki Amma banda mutum uku.

Jameel ji yayi kamar ana sara mishi Abu atsakar ka da sauri ya rike Kai Yana duk wata addu'a da tazo bakin sa,Saida ya shafe tsawan mintina ahaka sannan yasamu komai ya daidaita.

Afeeya na lura da yanayin da yashiga Dan idonta na kansa, mummy ta yiwa alama sannan suka tashi suka nufi Bayan gidan suna zuwa ta fashe da kuka.

Rarrashin ta mummy ta shigayi tana cewa,"menene afeeya meya sakaki kuka?

Kara rungume ta tayi tana cewa,"mummy shikenan Jameel bazai aure Ni ba wallahi nasan baxai aure ni ba.

Shiru mummy tayi tana nazarin yanda zata bullowa lamarin.

Zare jikin ta tayi daga jikin afeeya ta nufi cikin gida Bata kaiga karasawa ba suka hadu da daddy Yana niman su,jansa tayi gefi tace, daddyn afeeya gara mu tafi gida tunkafin afeeya ta jaza Mana abin kunya agarin nan.

"Kamar ya ban fahimce ki ba?

Kuka itama ta fashe dashi ta labarta mishi abinda ke faruwa.

Rarrashin ta yayi yajata suka nufi inda afeeya ke zaune tana risgar kuka.

"Rarrashin ta suka shiga yi sannan ta tashi suka shiga daki,kayan su suka dauka.

Jameel kuwa tunda yaga duk kansu sun tashi shima yatashi yabi Bayan su duk da matsanancin ciwo da kansa keyi,duk abinda ya faru akan idonsa ne ganin sun shiga daki yasa ya nufi inda kowa da kowa yake.

KARSHAN WAHALA 2019Where stories live. Discover now