chapter 27

815 49 0
                                    

🌾KARSHAN WAHALA 🌾

By

Safnah aliyu
Jawabi

🌽🌽🌽🌽🌽🌽🌽🌽🌽
🍎🍎🍎🍎🍎🍎🍎
🐙🐙🐙🐙🐙
💖💖💖💖
🌲🌲🌲
Bismillahi rahamanin Rahim

Mummy  ce atsiye rike da kugu tana huci.

Cike da ma'maki nake kallon ta dan aiya sanina tunda nazo gidan ko kallon banza baitaba shiga tsakanina da ita ba.

Bangama dawowa daga duniyar tunani dana shilla ba naji an bugamin abu akai ya tarwatsi min aka rike kaina nayi wanda ayanzu yake barazanar fita daga wuya na,ihun afeeya ne abinda naji na karshe.

Ashe mummy ce ta bugamin plet da gudu afeeya tazo tana jijjigani tana kiran sunana taba kaina tayi jini tagani da gudu tabi mummy wanda tunda taga nafadi ta wuce tabarni anan,adakin ta, ta same ta durkosawa tayi tana rokon ta akaini asibiti,ture ta tayi tace,"wallahi afeeya kifita a  idona karna rufe dake,domin  kuwa babu inda zanje koda kuwa mutuwa zatayi.

Jin kalaman mummy na karshe yasa afeeya fita da gudu bata tsaya ko ina ba sai gidan su rukkaiya lokacin rukaiya da aunty mama suna suyar waina ganin yanayin data shigo yasa suka tashi cikin kidima suke tambayar ta.

Lafiya afeeya naganki haka?

Babu abinda take iya cewa sai kiran sunana da takeyi,cikin kidima suka nufo gidan mu rukkaiya ko hijabi babu ajikin ta,ganin halin dana ke ciki yasa rukkaiya fashewa da kuka ganin kukan bazai amfanar dasu komai ba yasa suka kinkime ni suka fitar dani waje muna zuwa afeeya takira drive tace yafito da mota.

Basu Ankara ba saijin muryar Daddy sukayi yana cewa,"idan ka kuskura ka fitar minda mota abakin aikin ka.

Cikin haushi da takaicin wannan Sabon halin da iyayan ta suka tsiro dashi tace,"rukkaiya ku kamata mufita munime mai adaidaita.

Takai hannu zasu dauke ni kenan daddy ya janyo ta"babu inda zaki tafi tunda ba kanwar uwarki bace.

Turjewa afeeya take yana janta cikin daga murya tace,"dan ALLAH  kulamin da aminiya ta konawa ne kunema zan biya ku daga baya.

Saida suka fita suka nime mai adaidaita sannan suka nufi asibitin sanjarat  dani.

Muna zuwa aka nufi emergency dani cikin kankanin lokaci aka fito dani zuwa dakin hutu,saida na shafe kusan awanni shidda sannan na farfado,bude idona na farayi ahankali harna bude gabaki daya.
Afeeya ce zaune agefe na duk idonta yacanza laune da alama ba karamar kuka tayi ba.

Tabata nayi dan da alama tayi  zurfi cikin tunani tashi tayi da sauri ta rungumeni atare muka fashe da kuka saida muka kwashe lokaci mai tsayi ahaka sannan muka saki juna  nice nayi karfin halin cewa,"afeeya menayi wa mummy?

Cike da ma'maki take kallo na sannan tace,"meyasa baki tambaye ni laifin da kika yiwa daddy ba saina mummy?

Kasa cewa komai nayi dan gabaki daya ban shiryawa wannan tambayar ba,ganin banida niyar amsa mata saita canza akalar tambayar zuwa babu inda ke miki ciwo?

Girgiza mata kai nayi alamar babu, tashi nayi da niyar zuwa toile saiji nayi na janyo abu hakan kuwa yayi daidai da shigowar Jameel da abokin sa mustafa, cikin sauri ya rike hannuwa na yana cewa,"kikula karki jiwa kanki ciwo, dago kai nayi dan ganin abinda ya rike min hannu ledar jini na gane sarkafe ahannu na.

KARSHAN WAHALA 2019Where stories live. Discover now