chapter 8

1.1K 83 1
                                    

Lantana tana gama fadawa laure yanda zasuyi sukayi sallama,yanda tabar Maryam haka tafito tasame ta,

Maryam tace,to ya'ya sai anjima,

Ko kallon arziki bata samu daga gurin lantana ba,

Itah dai,tunda lantana ta shigo gidan gaban ta yake dukan uku uku tarasa dalili.

Shiru da Maryam taji laure bata fito ba shiyasa tayi tunanin ko lafiya,tana zuwa bakin kofar tayi sallama,amma shiru saitayi tunani bari ta shiga tana shiga tasami laure azaune amma ko kifta ido batayi

Dasauri ta nufi gurin tace, ya'ya har saida takira ta sau uku sannan tayi firit ta dawo da alamu tayi zurfi cikin tunani,
Laure ta dubeta tace lafiya kika shigo min daki?

Maryam cike da mamaki tace, ya'ya dama najiki shiru ne shiyasa nace Bari naduba ki

Laure cikin tsawa tace,rufe min baki munafuka makira annamimiya azaluma ina ruwan ki da rashin fitowa ta ko zaman ki nake,to kafin na rufe ido na na bude kibace min dagani,

Maryam wanda tuni hawaye ya gama bata mata fuska haka taja kafarta tafita, tanajin laure tana cewa, ALLAH ya tona asirin ki keda iyayanki.

Tunda ta shiga daki bata kuma fitowa ba ,koda taji shigowar malam bata fito ba dan gabaki daya atsorace take

Malam tun yana daurewa har yakai ga tambayar laure yace,naji shiru yarinyar nan bata fito ba ko dai bata da lafiya ne?

A a lafiyar ta lau, nikaina banason zaman dakin da take yawan yi Amma idan nayi mata magana saita nuna itah tafison zaman daki.

To ai shikena tunda haka take so,nikam yau bakaramar gajiya nayi ba bara naje na kwanta saida safe, to ALLAH yatashe mu lafiya malam

Cikin sauri malam yanufi dakin dan agaskiya ba barci yake ji ba kawai dai haka Nan yaji baiyarda da maganar laure ba,

Yana shiga yatarar da itah azaune yace , Maryam lafiyar ki kalau kuwa ko akwai inda ke miki ciwo?

A a babu inda kemin ciwo.

To meyasa baki fito munyi hira ba?

Babu komai barci nake jine.

To babu damuwa saida safe.

Ba'afi mintina biyar dashigar malam dakin maryam ba,

Maryam ce tafara jin ihun dafarko ta dauka ko amakota take ji saida takasa kunne saita ji muryar laure aikuwa bata yi wata wata ba ta tashi malam jauro.

Cikin firgita yatashi Yana tambayar ta lafiya,

Kamar ihu nake ji Yana fitowa daga dakin ya'ya shiyasa natashe ka, cikin saure ya nufi dakin laure, yana shiga yatarar da Laure sai shure shure take,

Yace subhanallah meke faruwa cikin kuka tace,ciki na malam zan mutu,

Nandanan ya dauko koryar dake dakin yafara mata addu'ar Yana to fawa,Yana gamawa yatallabo kanta Yana bata ta na sha, Maryam tana daga gefe tana mata sannu,

Ganin tasamu sauke yasa malam ya mike yace,to ALLAH yakara sauki Bari muje mudan kwanta,cikin kuka laure tace, wallahi Ni Kam tsoro dakin Yake bani,malam dazaka yimin alfarma daka bar Maryam ta kwana dani,

Laure kin wuce alfarma aguri na, yajuya yana kallon Maryam yace , maryam kitaya ta kwana sai ALLAH yatashe mu baijira mezata ce ba yafita,

Ba'afi mintina biyar da fitar malam ba laure ta watsake barci harda minshari
Itah dai batace komai ba tasamu guri tayi kwanciyar ta,

Haka dai laure taci gaba da ciwon cikin karya har girki yafita ahannun maryam ranar da zata karbi girki haka tayita kaiwa da komowa tana habaice habaice,

KARSHAN WAHALA 2019Where stories live. Discover now