chapter 36

759 56 2
                                    

🌲 KARSHAN WAHALA 🌲

🌲By🌲

🌲Safnah aliyu jawabi 🌲

( B*H*W*A)

Bismillahi rahamanin Rahim

Gare ku masoya na ga shafe domin ku

*Hauwa rabi'u*

*Abdullah rabi'u*

*Khalifa rabi'u*

*Umar rabi'u*

*Hanan rabi'u*

"Mustafa na fita bai tsaya ko ina ba sai gida, Yana shiga ya fashe da matsanancin kuka ,haka ya dauki lokaci Mai tsayi Yana cikin wannan halin ganin hakan bazai amfanar dashi komai ba, yasa yamiki ya nufi asibiti Dan izuwa lokacin bashi da inda za isamo kudi Dan dare yayi sosai kusan Sha daya ne lokacin.

Bayan fitar Mustafa iyayan afeeya suka nimi jin abinda ke faruwa, likitan bai buye musu komai ba, kuka afeeya keyi kamar zata sake ganin haka yasa hankalin iyayan ta,tashi riko ta daddy yayi yace,"ki daina kuka yanzu ki fada min me kike so ayi?

Dago kai tayi tana kallon shi cike da ma'maki tace,"daddy abiya kudin dan ALLAH.

Murmushi yayi yace,"to  shikenan daina kuka haka.

Shiga yayi gurin likitan suka gama maganar yanda za'ayi, daddy ya biya duk kudin da ake bukata har zuwa ranar da za'a sallame su.

Kallo daya zakayi wa afeeya kasan cike fal take da ma'maki lokacin da taji daddy ya biya duk kudadan da akeda bukata da gudu ta fada jikin sa tana hawayen murna, bubbuga bayan ta yashiga yi alamar rarrashi,suna cikin haka Mustafa ya shigo duk fatan idon sa sun ajame da alamu bakaramar kuka yayi ba.

Afeeya na ganin Mustafa ta sake daddy shikuwa suna hada ido ya sunkuyar da kansa kasa, Dan gabaki daya kunya yake ji Dan ganin yakasa taimakon aminin sa.

Ita kuwa murmushi tayi tace,"Mustafa ka daina damuwa yanzu addu'ar mu kawai yake da bukata...nandai ta fada mishi duk yanda abin ya kasance bayan tafiyar sa.

Sujjada Mustafa yayi yana godiya ga ALLAH daya kawo musu dauki saidai fatan ALLAH yasa adace.

Daddy ne ya kalli mummy da afeeya wacce harta fara gengedi yace,"innaga ya kama ta KU tashi na kaiku gida inyaso saina dawo,ba Haka afeeya taso ba amma babu yanda ta iya Haka ta tashi daddy ya kaisu gida  bayan ya kaisu sannan ya dawo suna jiran fitowar likitan"

Koda afeeya ta kwanta kasa barci tayi, ganin kwanciyar bata da wani amfani yasa ta tashi ta dauro alwala ta gabatar   da nafila,baya ta idar ta zauna tana addu'a ba'ita ta tashi ba saida tayi sallar asuba sannan ta Dan kwanta aikuwa barci bai mata da sauki ba Dan saida takai 12 kafin ta farka.

afirgice ta farka tana kallon agogo cikin sauri ta fada toilet batafi 15minit ba ta shirya cikin riga da siket na jar atamfa, farar hijabi ta saka koda tafito bata tarar da mummyn taba, tana fita Mai gadi ke sanar da ita cewa mummy tace," idan ta tashi ta sameta asibiti.

Aikuwa cikin sauri ta fita Mai adaidaita ta tsayar ta fada mishi inda zai kaita,suna isa da sauri ta karasa cikin dakin, mummy ta gani tana zaune Mustafa yana tsaye daga gefa.

KARSHAN WAHALA 2019Where stories live. Discover now