chapter 12

1K 86 1
                                    

Inah fita ban tsaya ko inah ba Inna fitowa da tallar muka hadu da maimuna, cike da ma'maki take tambaya ta"kekuwa ina zaki kai wannan abincin?
Girgiza mata Kai kawai nayi nace"yazanyi da jarabbatar da ALLAH ya doramin.

"Bangane ba.
"Inna ce tace naje nasayar kuma karna sake nadawo da ko daya,cikin kuka nakefada mata.

"Kinga karki damu, kizo mutafi gidan mu zanyiwa inna ta magana, taje tasame ta gaskiya, wannan tallar bazai yuba.

"Karki damu zantafi, nasan wannan itace kaddarar da ALLAH ya doramin, nidai abinda nakeso kitayini dashi shine addu'a. Ina gama fada mata banjira Jin abinda maimuna xata fada ba,tunda nafara tafiya ban waigo ba harnabacewa ganin maimuna.

Haka dai nayi ta yawo, bansan inda zantafi ba, gashi magriba ta gabato, haka dai na hakura na nufi gida.

Laure naganin shigowa ta, ta mike tsay tana jiran in karaso aikuwa tana ganin abincin, da alamu ko daya ba'asaya ba tasauke abincin kasa ta rufini da matsanan cin duka, tun ina ihun niman agaji harna sadakar,

saida tagaji sannan ta ,yarda bulalar tukunana,"yanda kika saka nayi asara wallahi kuwa hakanan Zaki kwana da yunwa, shashasha.

Haka na kwana Ina murkususu Ni kadai, adakina yunwa taci karfi na haka dai nayi tayi inah Shan ruwa hargari yawaye,

Inah ji anakiran sallah nararafa domin nayi sauri natafi gidan su maimuna killah nasamo wani abun nasa aciki na,inah fita nacikaru da laure tana gani na tace,

"yauwa dama kuwa yanzun nake tunanin naje natashe ki ashe kin tashi,to maza dauki tulun canki jeki debo ruwa,Dan ko ruwan alwala babu agidan nan.

"Wallahi Inna yunwa nake ji duk....kafin nakarasa naji kaman anbuga min Abu akai wanni azababban zafi naji yaziyar ci kaina inasa hannu naga jini aibansan lokacin da na kwalla kara ba."Zaki tashi kitafi ko saina Kara miki shashasha.

hakai dai natashi jini nazuba harkan fuskata ,ina tafiya na hangi maimuna zata wuce islamiyar da muke zuwa da asuba, dasauri na nufeta Dan kamar mabata gane nice ba, dantasan bana zuwa Rafi da asuba,cikin ma'maki take kallona."safnah Rafi Zaki da asuban Nan ke ko tsoro bakyaji.

Shirun danayi ne yasa ta kalli fuskan ta dakyau aikuwa tana ganin jini tasa sallati tana tambaya ta"meyasa meki safnah waya miki wannan ta'addancin?
Cikin kuka nace," Inna.

"Mekika mata?

"Babu komai wallahi ,kema kinsan babu abinda zanmata haka dainafada mata abinda yafaru tunjiya.

"Shikenan yanzun kizomuje gidan mu saikici abinci Inna tazata saka mike magani.

"Tsoro nakeji.

"Tsoron mee?

"Ruwan fa, dakin bari naji nadibo mata ruwan sainazo.

"Karki damu zansa Sadiq zaidebo saiki kaimata.

Haka muka nufi gidan su maimuna muna isah tayi wa Innan ta bayani,nandanan aka kawo min abinci naci,inah gamawa nayi wanka maimuna tabani sabbin kayanta, Innar su tasamin magani tayimin nasiha,Dan zaman danayi agidan kamar karna Koma .

Tundaga waje nakejin shewar Inna laure, azuciya ta nace,"to innah laure kome aka samu Kuma oho,dan idan kaji tana irin wannan shewar to wani abin arzikin tasamu.

Dasallama nashiga, inah shiga saida zuciya ta takusan bugawa, Dan ganin wannan matan ba alkairi bane ,Dan da alamu itah take zuga Inna laure.

Suka amsa gaba daya,innah laure cikin fara'a tace,"yar'albarka kindawo?

Haka naji abin yamin banbara kwai wai namiji da sunan hajara ,haka dai na amsa.

"To zoki zauna muyi shawara.
Nazauna naji wata shawara za'ayi dani, lantana ce tafara magana,"
Dama bawani abubane kinsan dai Innar ki ita ce ke kula dake ko?

"Eh.
"To shine muka yanke shawarar Zaki bini birni domin kiyi karatu kizama bab'ba cikin kawayenki.

Cikin farin ciki nake tambayar ta,"Dan ALLAH dagaski ne innah ta?

"Kinji shashasha wake wasa dake.

"To kiyi hakuri kawai dai nakasa yarda wai Ni SAFNAR gidan innah laure zatayi karatu.

To saikije kishirya gobe zaku tafi.
Cikin sauri na tashi nayi gidan su maimuna ta,Dan nafada mata abin arziki daya sameni...

Don't forget to vote and comment love you all.lol😋😋😋😋

KARSHAN WAHALA 2019Where stories live. Discover now