chapter 37

783 64 1
                                    

KARSHAN WAHALA

By
Safnah aliyu jawabi

🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲
🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲
🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲

Bismillahi rahamanin Rahim

"Yana fita bai tsaya koina ba sai gidan basi, hon yake kamar zai tashi sama,cikin sauri Mai gadin ya bude ko gyara parking baiyi ba ya fita da gudu ya karasa cikin falon Dan yanda yake jin kaunar yarinyar babu abinda bazai yiba.

Kiran sunan basi yake cikin daga murya,barci take Taji ana kwalla mata kira babu shiri ta miki cikin sauri.

Tana ganin shi cikin sauri ta koma zata rufe kofar,figo ta yayi batare da bata lokaci ba ya wanke ta da Mari masu lafiya har guda biyu.

Tsungun nawa tayi agurin tana kuka.

"Ina *SAFNAH*take?

Dago kai tayi tana kallon shi ganin yanayin da yake ciki ta san komai na iya faruwa yasa tayi saurin cewa,"na kore ta Dan bazan iya Zama da Maci Aman...

Sake wanke ta da Mari yayi sannan yace,"har kina da bakin Kiran wata Maci Amana? kin mace kema haka kikayi wa hajiya wato harki na da bakin Kiran wata Maci Amana ko?to bara kiji na rantse idan kika bari wani Abu yasa mi yarinyar nan wallahi sai nayi ajalin ki, banza karuwa.

Bai tsaya jin abinda zata fadaba yayi ficewar sa.

Ita kuwa kuka Mai karfi ta fashe dashi tana cewa,"wallahi kafin kayi ajalina saina fara ajalin ta.

"tashi tayi ta shiga ciki ko wanka bata tsaya yi ba, ta fito bata tsaya ko ina ba sai gidan sumaiya da kuka ta shiga gidan tana zuwa ta fada jikin ta tana kuka Mai tsuma rai.

Hankali tashe sumaiya ke tambayar ta abinda ya same ta,zaiya na mata abinda ya faru tayi.

wata muguwar ashar sumaiya ta saki tana cewa,"Wallahi uban kuturo ma yayi kadan wallahi saidai mu muga bayan sa, kwantar da hankalin ki tawan babu abinda ya isa yayi miki indai ina da Rai.

Ahankali sumaiya ta shiga kwantar mata da hankali harta samu tayi shiru daga Nan suka lula duniyar su wacce su kadai suka san dadin ta.

*******

Hajiya kuwa hankali akwance take rayuwar ta tunda aganin ta yanzu babu basi adoron kasa,tana kwance adaki ganin babu abinda take ,yasa ta yanke shawarar fita ta dan zaga gari.

SYde resort ta nufa guri ne Wanda manyan masu kudi suke zuwa domin shan iska zama tayi tasa aka kawo mata feiroz,ahankali take baza idanuwan ta lungo da sako na wurin.

Kwarewa tayi sakamakon ganin basi da tayi zaune tare da sumaiya suna Shan shisha hankali akwance.

Tashi tayi cikin kunan zuci ta nufi gidan ladi,akofar gidan tayi parking.
Tun daga kofar gidan take kwalla mata kira,Jin Kiran tayi daga sama da sauri tafito aikuwa babu bata lokaci hajiya ta cakumi wuyar rigar ta,tana. Cewa,"ALLAH ya tona asiriki munafuka algunguma wato ni Zaki cewa dun duniya ko?

Fin cekar rigar ta tayi tace,"dallah malama kimin uzuri so kike adalilin aikin ki na banza da wofe na rasa raina? To idan ma da hadin bakin ki aciki to ta ALLAH bataki ba.

KARSHAN WAHALA 2019Where stories live. Discover now