chapter 3

1.6K 130 2
                                    

*KARSHAN WAHALA*

*Writing*

*BY*

*SAFNAH ALIYU JAWABI*

Follow me up in whattpad

(@jawabi)

0️⃣➖3️⃣

*Duk da yanzu kaddara ta rabani da ku ƙawayan arziki,ina alfahari da soyayyar ku gare ni,domin kuwa ɗan halasa baya mance halaci,mance halacci sai butulu don haka kuna raina ,baby bintu,autar manya,Allah yaja kwana,son so fisabillah muke wa juna*

Dedecat this whole novel to you Muhammad karim Allah yabar ƙauna.

*Betwed to* _you dear hibbatulla for sure am proud of you_

,,,Nasir yana kara sowa gurin mum c yace,"gaskiya naji dadin ganin ki mum c.

Hararar sahajiya Fatima tayi tace,",nidai banason surutu muje ka kaini, sauri nake kasan daga nan zantafi airport na dauko su.

Nasir yana gaba hajiya Fatima tana biye dashi har suka karaso dakin da suke,hajiya Fatima cikin tausayawa tace ",ya jikin naki?

cikin natsuwa tace," da sauki hajiya.

hajiya Fatima tace," ALLAH yakara sauki juya tayi tace," nasir inafata dai iyayan ta sun san halin da take ciki?

  kallon ta yayi yace," mum c maganar da mu keyi da ita kenan naga kiran ki.

Nan take hajiya Fatima tafara yiwa nasir fada,"wannan wani irin sakarcine son?," yarinya tana cikin wannan halin ace ba'asanar da kuwa nata ba?" baka tunanin rashin ganin ta,Zai saka su cikin damuwa?

juyuwa tayi tana kallon ta tace," baiwar ALLAH kiyi hakuri kinji ina ne anguwar taku?,"don yaje ya sanar dasu ko ki bada number wani daga cikin dangin ki akira su.

Jin haka yasa nasir yace,"mum c dama dr yabada sallama yace," adawo bayan kwana uku akwance mata, shine na cewa little ta taimaka mata ne su shirya kafin na dauka ki.

mum c tace," to ku shirya mutafi kunsan nifa sauri nake, nantake suwaiba ta mike tafara harhada kayan magungunar dake gurin.

juyuwar dazat ayi,saigani tayi hawaye😭😭 na zuba daga afuskar ta,batayi wata wata ba tafara tambayar ta.

,"Baiwar Allah meya same ki?

tambayar da tayi mata ne, ya dawo da hankalin nasir da hajiya Fatima duk kansu kanta,cikin ma'maki suka hada baki lokaci daya suna tambayar ta.

hajiya Fatima tace ,"baiwar ALLAH,ko akwai inda ke miki ciwo ?nasir yace," mum c barina kira likitan,cikin hanzari ta dago ido tace," a a wlh babu inda kemin ciwo.

Cike da mamaki hajiya Fatima ta matsa kusa da ita zama tayi a bakin gadon tace," baiwar ALLAH, idan akwai abinda ke miki ciwo kiyi magana kinji?,"mu riga mun zama daya,sannan ina mai baki hakuri kinji idan ma kina tunanin abinda zaki fadawa iyayan kine, karki damu tare zamu je gidan.

,"Ina sha Allah zamuyi musu bayanin yarda abin yakasan ce.

cikin kuka tace," wallah hajiya ba haka bane.

Kara kallon ta hajiya Fatima tayi azuciyar ta tana aiyana anya yarinyar nan bata samu matsala a kanta ba kuwa,karfin hali tayi tace,"  to menene matsalar?

cikin kuka tace," hajiya ni bani da kuwa asalima bansan inda zannufa ba daga nan.

,"Hajiya Bansan yaushe nene KARSHAN WAHALA ta zatazo ba.

Duk kansu kallon juna sukayi  cike da mamaki,hajiya fatima tace," kamar ya?ai kuwani mutum dakika gani aduniyar nan Yana da asali.

nasir wanda tunda tafara magana yake kallon ta cikin mamaki,sai asannan ne yasamu damar yin magana yace," mun c karki damu.

,"yanzu dai mutafi gida kinga gasu aunty ummi sunkusa karasowa, sannan anbamu sallama tun dazu koma menene
Idan muka kai gida saita fada mana, suwaiba dake zaune har tafara hawaye cikin sauri tace," gaskiyar ka ne, ya'ya.

,"Mum c mutafi gida da ita koma menene saita fada mana.

Sauke ajiyar zuciya Hajiya Fatima tayi  tace," toh.

cikin mintina biyar suwaiba ta hada magungunar dake gurin suka fito kowa da abinda yake tunanin acikin zuciyar sa suka shiga mota suka nufi gida.

*SAFNAHR kuce har kullum*

*please don't forget to vote comment &share with your friends*

🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

KARSHAN WAHALA 2019Where stories live. Discover now