chapter 32

741 69 5
                                    

KARSHAN WAHALA

By

Safnah

Aliyu jawabi
🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎
🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎
🌏🌏🌏🌏🌏🌏🌏🌏🌏
🌐🌐🌐🌐🌐🌐
🌍🌍🌍🌍🌏

Bismillahi rahamanin Rahim

Ku santo ni yake ina ja da baya harya karaso inda nake janyo ni yayi na fada kan katifar harzai kai hannu jiki na daya daga cikin su yace,"amin afuwa oga sai nake ganin kamar baita bace"

Kallo na yayi na dan mintina sannan yace"miko min hotun nan"

Miko masa yayi sannan ya kalli fuska ta da kyau ya kuma kallon hotun tsaki yaja ban'ankara ba saijin saukar mari nayi wani kara na sake lokacin daya kuma na gimtse baki na sakamakon wani farin haske daya gilma ta ido na.

Daga nan bansake sanin abinda ke faruwa ba saidai kawai tashi nayi na ganni kwance agadon asibiti wannan likitan dai shine kuma akaina yane min sannu.

Cikin mintina kalilan duk abubuwan da suka faru suka dawo cikin memory dina ai afirgice na zare ruwan dake hannu na, mikewa tsaye nayi likitan na komar dani amma ina banda hawaye babu abinda ke zarya afuska ta,da kyar dai ya samu na kwanta allura ya dauko yamin ko cikakkiyar mintina biyu ban kara ba barci yayi awan gaba dani.

Kuda na tashi babu kowa adakin tunanin rayuwa da halin da na tsinci kaina aciki nake bansan adadin lokacin dana dauka cikin duniyar tunanin ba sai tsinkayar sallama nayi daga sama,adda basira ce tare da wani mutum kato baki bashi da ko kyaun gani ga idanuwan shi ga tumbin kato,kawar da kaina nayi dan bana kaunar sake hada ido dashi.

"Ya jikin nake" naji ance juyowa nayi kadan nace"da sauki"
"To ALLAH ya kiyaye na gaba ki kwantar da hankalin ki babu abinda zai kuma faruwa makamanciyar wannan"

"To kawai nace"

Fita sukayi waje ni kuma na koma barci.

Saida mukayi kwana hudu asibitin sannan aka sallame mu acikin kwanakin nan kuwa gata babu irin wacce bangani ba agun wannan mutumin da suke kira mai buhun kudi.

Cike da ma'maki nake kallon gidan dan baiyi kama da wancan gidan ba shiru nayi ina kallon ikon ALLAH saida muka shiga ciki yaga ina ta kalle kalle cikin saken fuska yace"my sis" dake Haka yake kira na,

Dago kai nayi da murmushi nace"na'am big Bros"

"Kinga bawancan gidan muka zo bako?

"Eh" kawai nace.

"Na canza muku gida ne dan ganin wancan babu tsaro shiyasa"

"An gode kawai nace"

Nayi shige wata daki na barsu suna hira.

Koda na shiga dakin sai naga komai da komai wannan gidan tafi wancan murmushi nayi na gode wa ALLAH daya kubutar dani daga hannun azzaluman mutanan nan.

🗾🗾🗾🗾🗾🗾🗾🗾

Shiru shiru hajiya babu labarin mutuwar basi babu labarin goje tana kwance tana sakar zuci sai jin sallama tayi daga sama,dago kai da zatayi sai ganin lantana tayi atsaye tana wangale baki,cike da bacin rai hajiya ta daka mata tsawa tace"mekika zo yi gida na?

KARSHAN WAHALA 2019Where stories live. Discover now