chapter 28

854 66 2
                                    

❄️❄️❄️❄️❄️
*KARSHAN WAHALA*
                     ❄️❄️❄️❄️❄️❄️

*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*💥
_(THE STARS THAT SHINE IN THE WORLD OF WRITER'S)_

https://mobile.facebook.com/Taurari-Writers-Association-109116734087974/?ref=opera_speed_dial

         *T. W. A✍🏻*

*STORY*
&

*WRITING*

*BY*

*SAFNAH ALIYU JAWABI*

*Dedicated to ya Muhammad karim &baby Eeeshart*

2
2

️⃣8️⃣

*BISSMILLAHI RAHAMANIR RAHIM*

,,,Gari na waye wa afeeya ta shirya cikin shirin ta na makaranta ta, aranar ko tsayawa taci abinci batayi ba,ta nufi   makaranta tana zuwa harzata wuce taga akwai bukatar ta fadawa nusaiba rashin lafiya ta.

Shiga ajin mu tayi aikuwa ta hango nusaiba murmushi suka sakarwa juna, alama afeeya tayi wa nusaiba da tazo  cikin sauri ta ije takardun  dake hannun ta, ta tashi tafito  kallon ta nusaiba tayi tace,"ina kika baro safnah?

Murmushi afeeya tayi tace,"ke dai kin cika hanzari dama abinda nazo na fada miki kenan," safnah bata jin dadi yanzu haka ma tana asibitin sanjarat.

Salati nusaiba tayi cikin kidima "me yasame ta?meyasa aka kaita sanjarat? gaskiya bazai taba sabuwa ba bara na kira daddy akaita giwa aiwanna cin zali ne,dan kawai yarinya Bata da gata sai a dauke ta akaita sanjarat?

Binta da kallo kawai afeeya keyi dan gabaki daya rasa bakin magana tayi, saida taga da gaske nusaiba kiran daddyn zatayi, cikin sauri ta dakatar da ita tace,"ke wai me haka ne?kinfini son tane?ko kinsan dalilin da yasa aka kaita can.

Girgiza kai nusaiba tayi zuwa lokacin kuwa hawaye gangara yake babu alamar tsayuwa tace,"kiyi hakuri kawai na shiga ruɗu ne.

,"Babu komai yanzu ki shiga ki zana jarabawar ki nima zanshaga aji idan muka fito saimu tafi kinji.

Nod da kai kawai tayi ta shige aji zuciyar ta cike da tunanin abinda ya same ni kamar jiya haka ta rubuta nata sannan ta rubuta nawa,cikin kankanin lokaci ta kammala kasancewar ta yarinya mai haza ce.

Saida ta zauna ta jira fitowar afeeya, sannan suka nufi asibiti,abakin gate suka jira mummy tazo suka karasa ciki.

Ina zaune naji muryar mummy kamar daga sama da sauri na tashi na rungume ta ina kuka sam bamma lura da wanzuwar nusaiba agun ba,bubbuga baya na ta shigayi harna samu nayi shiru sannan nace,"kimin aikin gafara mummy nasan laifi nayi miki yasa kika min hukuncin daya dace dani, kiyi hakuri domin fushin ki  babbar matsala ne agare ni.

Shiiii tace ganin mutane sun ciki dakin ansamu atsakiya tace,"nikam baki yimin komai ba ƴata koma ki kwanta kinga baki gama watsakewa ba.

Komawa nayi na kwanta ina sauke ajiyar zuciya dan sam har cikin zuciyata ban kullaci mummy ba, dan inada tabbacin wani makircin daddy ya shirya min agunta.

KARSHAN WAHALA 2019Where stories live. Discover now