chapter 34

830 69 1
                                    

*KARSHAN WAHALA*

By

*Safnah aliyu jawabi*

*Facebook safnah aliyu jawabi*

*Istagram official safnah aliyu*

*WhatsAPP group keep your number*

Bismillahi rahamanin Rahim
✍️✍️✍️✍️✍🏼✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍🏼✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

Sauke ajiyar zuciya *nasir* yayi sabanin mum c da share hawaye take wani na gangaro wa, suwaiba kuwa tashi tayi ta rungume *safnah*ta sake kuka Mai sauti atare suke kuka karfin hali mum c tayi ta janye suwaiba daga jikin* safnah* ta fara magana kamar haka,

"munji labarin ki* safnah* kuma mun jajanta miki ALLAH yabi miki hakkin ki akan wayan da suka cutar dake sannan ina mai tabbatar miki zamu rike ki abisa yarda, da amana ALLAH yasa ke ma zaki rike mu da amana.

Wani kayatacan murmushi *NASIR*yay sakamakon jin *SAFNAH*
Zata zauna agidan su.

"IN SHA ALLAH nayi muku alkawari ba zaku taba samuna da cin amanar kuba"

"Alhamdulillah suwaiba tace,shikuwa gogan kasa magana yayi banda murmushi babu abinda yake lura da hakan yasa mom c kallon inda yake cikin sauri ta dan zungure shi ganin kallon da yake yiwa *SAFNAH*cikin sauri ya daidata natsuwar shi,tashi yayi cike da kunya yace"mom bara na shiga ciki Kinga yanma ta gabato ya kamata na watsa ruwa nazo na leka ashraf.

"Murmushi mom tayi dan ta gama gano Dan nata tace" to maza ku tashi kuyi haramar daura girki Dan yamma ta gabato kunji yan matan mommy.

Tashi sukayi suka nufi kitchen Basu dauki lokaci Mai tsayi ba suka kammala daki suka shige
Danyin wanka *SAFNAH*ce ta fara shiga toilet ko kafin ta fito suwaiba ta fitar mata da kayan da zata saka duguwar rigace baka mara hannu da yar karamar veil fara Mai duwatsu.

Sai bayan ta saka sannan take ganin rashin dacewar shigar domin kuwa ana iya hango na shanun ta har zata cire taji suwaiba tana cewa"meyasa zaki cire wallahi karki cire bakaramar kyau tayi miki ba"

Murmushi*SAFNAH*tayi tace"gaskiya bazan iya fita da kayan nan ba.

"Saboda mee?

"Kinga tana nuna jiki shiyasa"

Kallon ta suwaiba tayi taga da gaske ne, murmushi tayi ta bude sip ta dauko mata farar abaya,karba tayi ta saka.

Saida suka gama kimtsawa sannan suka fito, mom suka samu zaune tana kallon arewa 24.

Da murmushi mom take kallon su tace"Kai yam matan mommy kunyi kyau.

Murmushi sukayi gabaki dayan su sannan suka nime guri suka zauna kallo suka cigaba dayi saida su kaji ana kiran sallar magrib sannan kuwacce ta tashi domin gabatar da sallah.

Basu fito ba saida akayi sallar isha'i bayan sun idar suka fito falo domin cin abinci mom ce ta kalle suwaiba tace"kinga yayan ki haryan zu bai fito ba maza jeki ki kira shi.

KARSHAN WAHALA 2019Where stories live. Discover now