chapter 23

818 47 3
                                    

🌴KARSHAN WAHALA🌲

💖By

💖Safnah aliyu jawabi 💖

🌲Mrs ABDULLAH IN SHA ALLAH🌳
💖💖💖💖💖💖
🌲💖    🌲    💖🌲🌲
🌲     💖 💖  🌲  💖  💖🌲
🌲🌲💞💞💞💞💞💞🌲
🌲🌺🌺🌺🌲🌺🌺🌺🌲
  🌲                🌲
🌲

Bismillahi rahamanin Rahim

Idan zaki aure ni babu abinda bazan miki ba zan wadata ki zanyi miki sutura zanfifita ki akan kuwa, zan....

Dakatar dashi nayi da hannun ina jin yanda zuciyata take yimin kuna da suya, cikin kakkausar muryar wace ni kaina bansan ina da ita ba nace,"kaga malam bankasance daya daga cikin mutane masu butulci ba kuma bana fatan canzawa saboda mulki ko wata dukiya.

Kasani babu wata dukiya da zaka bani wanda zai rufemin ido yasa nakasa ganin tsantsar halalcin da mummy da afeeya sukayi min, sannan wayan cen da kake gani ALLAH yasan da zaman su,koda baka taimaka musu ba ALLAH zai kawo musu mafita KU....

Saukar mari naji akunci na wanda zaida naga farin taurare sun gifta ta idona bude idanuwa na nayi wanda zuwa yanzu suka rine.

Nunani yayi yace,"shashasha danma kin gode ance za'a aure ki shine kike fadawa mutane zancan banza to kisani nine nake da mallakin wannan gida da kike sheke ayar ki aciki harkike tunanin ke wata abace,ayanzu basai anjima ba zan'iya korar ki  daga gidan nan kuma babu mahalukin daya isa ya Hana.

Ni kam bana takama ko tutiya da gidan nan amma kasani aiki ne ya kawo ni bacin amana ba .

Bantsaya jin abinda zaice ba na shige cikin gida da gudu ina shiga na tarar da afeeya azaune ta harde kafa tana girgizawa, ko kallon ta bankuma yiba na hawaura wata daki,kifa kaina nayi na fashi da kuka azuciyata ina tunanin ranar da KARSHAN WAHALA ta zata zo.

Haka nayi ta kuka babu mai rarrashi na,daga karshi na bawa kaina hakuri natashi na gabatar da sallolin da ake bina.

Can falo kuwa mummy ce take tambayar afeeya inda nashiga bata ganni ba.

Shiru tayi maimakon bada amsa saita fashe da kuka duk kansu hankalin su bakaramar tashi yayi ba musamman daddy wanda duk atunanin shi na fadawa afeeya abinda ya guda na atsakanin mu.

Tambayar ta  suka shigayi saida ta gama kukan ta sanna tace,"wallahi mummy zata rabani da safnah ta, kuma wallahi idan babu ita acikin rayuwa ta  mutuwa zan ...

Daddy ne yayi saurin rufe mata baki yace,"kiji shashashar yarinya Dama kinsan tane ? ko tare aka haife ku?

Karna kuma jin wannan maganar kinji na fada miki mtssss yaja tsaki ya haura dakin Shi.

Ita kuwa mummy rarrashin ta tayi harta samu ta shawo kanta, ta bata labarin rukkaiya da yanda na shigo gida ina kuka,kara Bata hakuri tayi sannan tace,"inbanda yaranta irin nake afeeya,"kanmee zakice bazaki iya rayuwa babu safnah ba kokin manta wata rana zaki yi aure ki zauna gidan mijin ki?

Mummy ni kam rana daya zamuyi aure da sweet safnah ta kuma gida daya zamu zauna.

Rike baki mummy tayi tace," nikam naga ta kaina kenan miji daya zaku aura ke da  ita?

KARSHAN WAHALA 2019Where stories live. Discover now