chapter 7

1K 90 0
                                    

Haka dai zaman lafiya taci gaba da wanzuwa acikin gidan malam jauro,

tunda Maryam tazo gidan, tadauke wa laure aiyukan gidan kabaki daya, dazarar laure tafito zatayi aiki sai Maryam ta fito ta karba,

hakan ba karamar dadi yakewa laure ba,hakanan takejin kaunar yarinyar a zuciyar ta ,

Ranar da Maryam ta shiga wata uku agidan tana zaune cikin dakin ta taji laure tana cewa, Maryam ni wallahi bana son zaman dakin nan dakike Yi kirinka fitowa muna hira,

Maryam tafito cikin murmushi tace, kiyi hakuri ya'ya.to samu guri kizauna bari nadako furar dana dama tundazu nakeso nasha barci yayi awan gaba dani.

laure tashiga tadauko furar tazauna kusa da Maryam tace,dauko ludayi kizo kizauna musha kafin malam yayo Mana aike,

nandanan Maryam tadauko ludayi ta diba furar daniyar kaiwa baki aikuwa kamshin furar yadaki hancin ta,

laure saiganin Maryam tayi rike da baki dagudu tayi hanyan bayi tana kwarara amai kamar zata amayar da hanjin cikin ta,cikin sauri ta nufi gurin tana yi mata sannu saida tagama sannan Laure ta dube ta cikin son sanin abinda yasata amai tace,

Maryam bakida lafiya ne baki fadamin ba? Maryam tace lafiya ta kalau ya'ya nima bansan meke faruwa ba duk abinda naci saina amayar dashi, cikin son ta gasgata abinda take zargi tace, Maryam tun yaushe rabunda kiga al'adar ki?

maryam ta tsaita kai kasa cikin kunya tace gaskiya na manta, tunkafin Maryam ta karasa maganar laure tafara yiwa

(ANNABI)salati tare da yiwa (ALLAH) godiya. itadai Maryam saibinta da kallo take tana ma'maki dama ana murna idan mutum baiga al'adar saba
Kamar laure tasan abinda take tunani ta dube ta cikin murmushi tace,

ALLAH ya amsa addu'ar mu ya azurta ki da samun juna biyu.maryam najin haka ta tashi tanufi daki cikin jin kunyar Laure,

Bayan malam jauro yadawo daga kasuwa laure ta kawo mishi abinci sai murmushi take,malam jauro ya dube ta yace niko laure naga sai murna kike ko dai tasamu ne kikawo muyi raba daidai kamar yanda muka saba.

Aikuwa laure kamar jira take malam ya tambayi ta tace,ba dole nayi murna ba malam abinda muka dade muna nima to ALLAH ya amsa addu'ar mu domin kuwa Maryam tana dauke da juna biyu. Tsabar rudewa saida malam jauro ya mike tsaye

Yayi hamdala ga ALLAH sannan yadube laure saiyaga kamar ma tafishi murna da samuwar cikin ganin haka , yasa bainuna zumudin son ganin Maryam aranar ba kasancewar girkin laure ne.

saidai harkasa barci yayi saboda tsabar murnah.

Da asuba bayan yadawo daga masalaci bainufi ko inah ba saidakin maryam yana isa ya ganta a kwance tana ta barci, baiyi kokarin tashin taba, ya tsaya yana kallon ta, saida yakare mata kallo sannan yayi mata addu'a sannan yanufi dakin laure.

Yana fita Maryam ta daga kanta kadan tana lekar sa kasancewar dama ba barci take yiba motsinsa da tajine tasa ta kwanta tay kamar tana barci domin itah harga ALLAH bazata iya hada ido dashi ba,

Washa gari laure har makota tarinka zagawa tana fada musu abin alkairi daya samesu, kowa agarin yana yabawa da imani irin na laure,

wasu suce sudai baxasu iyaba wasu kuma suce bata San ciwon kanta bane,

Tun daga ranar da Laure tasan cewa Maryam tana dauke da juna biyu bata kuma bari Maryam tayi aiki acikin gidan ba,duk da naci irin na maryam,

Suna zaune ranar wata laraba lokacin cikin maryam yakai wata shidda zuwa bakkwai, laure tana wanki itah kuma maryam tana daga bakin kofa tana Taya ta hira,

Suna cikin hira saisuka ji anyi sallama daga kofar gida, suka amsa laure ta tashi da saure tanufi matar tana cewa maraba lalai lantana yaushe agari?matar ta amsa cikin murmushi tace,zuwa na kenane nace bari na duba ki kawar,

kinga yanda kikayi kyau kuwa, laure tace dadina dake kinciki zolaya wallahi nidai shiga daki bari na dabo miki ruwa.

Sai asannan Maryam ta gaisheta saida ta tsaya kadan tana yimata kallon ma'maki sannan ta amsa zuciyar ta ciki da son sanin wacece itah,

aikuwa kamar jira take Laure tashigo tace, kawar wata yarinya nagani harda tsohon ciki agidan nan wacece itah? Laure tayi murmushi tace,banyi ma'maki ba idan kikace bakisan cewa malam yakara aure ba,

Cikin ma'maki lantana tace bansani ba,amma kuma shine naji har hira kukeyi da itah.laure ta kalle ta cikin rashin fahimta tace bangane ba to menene aciki dan munyi hira,

Lantana tace dadina dake wautarki laure, bakida tunani wani lokacin,to inbanda rashin hankali irin nake haryaushe zanzauna da kishiya, harna Bari ta zota mallaki gida,

Cikin rashin fahimtar inda zancan lantana yadosa tace,banfahim ce kiba. Lantana tace,kina ganin idan ALLAH yasa ta haifi da namiji,sanan aka wayi gari malam jauro ya bar duniya kina tunanin duk abinda ya mallaka baizama nata ba,

ke saidai abarki da abinda baikai yakawo ba,Dan haka inzaki tashi tsaye ki tashi inba haka ba kizama yar kallo,nidai kinga tafiya ta. tamike cikin saure laure tace,

to ni yakike so nayi yanzu,cikin nuna ko inkula tanime guri tazauna sannan ta fara yimata magana cikin kunne.

WANDA NI (S JAWABI)BANJI
MESUKE CEWA BA,SAIDAI,NACE MAI GASKIYA DAI YANA TARE DA (ALLAH) Lol😋😋😋😋

KARSHAN WAHALA 2019Where stories live. Discover now