chapter 31

809 68 5
                                    

*KARSHAN WAHALA*

*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*💥
_(THE STARS THAT SHINE IN THE WORLD OF WRITER'S)_

https://mobile.facebook.com/Taurari-Writers-Association-109116734087974/?ref=opera_speed_dial

         *T. W. A✍🏻*

*STORY*

&

*WRITING*

By

*SAFNAH ALIYU JAWABI*

*"there are moments in life when you will miss someone so much that you just want to peek them form your dreams and hug them for real I miss you so much mother*.


3️⃣1️⃣

*BISSMILLAHI RAHAMANIR RAHIM*



,,,,Har muka fita daga asibitin  ban dago kai ba, saida mukayi nisa, sannan na waiga zafafan hawaye ne suka cigaba da bin kunci na,  dan ALLAH kadai yasan yanda nake matsanan cin son Jameel,share hawaye nayi  nace," ko babu komai afeeya zata samu biyan bukatar ta.

Gudu sumaiya ke shararawa har muka isa asibitin giwa dan haka naga sun rubuta asaman ginin.

Muna shiga sumaiya ta samu guri tayi parking bude kofar da nake zaune basi tayi tace,"sauko mun iso asibitin"

A hankali muke tafiya har muka karasa cikin asibitin, wata kujera sumaiya ta nuna wa basi,dauko wa basi tayi ta ije min,Zama nayi  akan kujerar ita kuwa sumaiya shiga ciki tayi bata fi mintina biyu ba sai gasu sunfito ita da wata ma'aikaciyar asibitin.

Ciki ta shigar dani gurin liktan dan tambayoyin yayi min ina bashi amsa Saida ya kammala rubuce rubucan sa sannan ya umarci malamar asibitin da ta shigar Dani  dakin hutu.

Ruwa aka juna min ahannu aka min allurar ko minti daya bankara ba barci yayi awan gaba dani, barci mai ciki da mafarkai kala kala kuma duk akan Jameel.

Saida muka kwashe tsawan kwanaki uku ,sannan aka sallame mu likita ya bini da shawarwari da dama duk dai akan nacire tunani acikin zuciya ta.

Daga asibitin gida muka wuce, wacce ta kasance mallakin basira lokacin da muka shiga tsayawa nayi ina kallon gida dan abin ma'maki yake bani wani aiki basira keyi haka cikin kankanin lokaci harta mallaki gida irin wannan?

Tambayar da ta fado raina kenan daidai lokacin.

"Adda basira dake haka muke kiran ta wani aiki kike yi haka kika tara kudi hark...

"Ke dai haryanzu kinanan da kauyanci aiki nawa ke garin nan da harsai kin tsaya kina min tambayoyi "

"Shiga ciki kiyi wanka sannan ki fito kici abinci"

Batare da bata lokaci ba na shige inda ta nunamin amatsayin daki na, wanka nayi kafin na fito na aske harta dauko min kayan da zansaka, duguwar riga ce maroon ko ni kaina nasan regar tayi min kyau fita nayi na same su suna cin abinci kujerar na jawo na zauna basira ta diba min abinci muka zauna muna ci.

KARSHAN WAHALA 2019Where stories live. Discover now