chapter 44

854 67 5
                                    

🥀KARSHAN🥀

🥀WAHALA🥀

🥀By🥀

🥀SAFNAH ALIYU JAWABI🥀

(B🥀H🥀W🥀A)

🎄🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🎄🎄🎄🎄🎄🥀🥀🥀🎄🎄🎄🎄🎄
🎄🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
🎄🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🎄
🎄🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🎄
🎄🥀🥀🥀🥀🥀🥀🎄
🎄🥀🥀🥀🥀🎄
🎄🎄

Innalillahi wainna ilaihi raji'un
ALLAH yayiwa kanina Muhammad sani rasuwa,jiya akayi addu'ar uku Ina cikin alhinin Haka Kuma sai ga wata rasuwa wacce girgizar da nayi baxata misaltu ba, kawata asabe Ina rokon ALLAH ya gafarta Miki duk kannin zunuban ki ya sada ki da duk kannin alkairi zamu hadu IN SHA ALLAH agida Mai cike da ni'ima wato gidan aljanna zanyi kyawar ki harzuwa KARSHAN numfashi na miss you.

Bismillahi rahamanin

Da ma'maki lantana ke Kallon laure Dan ta fuskanci daga jikin ta warin ke fitowa.

Ganin lantana na niman Bata Mata lokaci yasa asabe ta cakumo wuyar rigar lantana shake ta tayi da duk karfinta tana cewa,"ke ballagaza abincin Yan cirani Ina Kika kai min yarinya?

Zazzaro ido lantana ta shigayi Dan tun ba yau ba ta dade tana Jin labarin karfi irin na asabe, Dan kuwa maza ma Haka suka ganta suka barta.

"dabara ce ta fado mata, murmushi tayi tace,"ke kuwa ALLAH yayi Mara wayau ni Ina Nan Ina tunanin yanda zan tallafawa rayuwar ki Amma ke kina Nan kina shashanci dallah sakar min riga.

Sakin ta asabe tayi tana jiran jin abinda zata fada mata.

Kujera lantana ta jawo dama da ragowar kudi cikin jakar ta Wanda hajiya ta bata dubu talatin ne yayi saura,dubu goma ta zaro ta mikawa asabe,jiki na rawa asabe tasa hannun ta karba tana murmushi.

Kallon banza lantana tayi Mata tace, wallahi kinyi da Mai yi bazan Kuma kawa Miki kudi ko sako ba koda kuwa basira ta aiko ni.

Da sauri asabe ta shiga Bata hakuri Saida taja  Mata aji sannan ta nuna ta hakuri Amma cikin ranta tsoro ne fal.

Da murmushi akan fuskar laure tace,"kawar Ina nawa Kinga dai halin da nake ciki abincin cima  gagarata yake.

Tsawa lantana ta daka mata tana cewa,"ke dalla rufa Mana baki Ina ruwa na da halin da kika tsinci kanki aciki, nice na saka ki acikin halin ko kuwa?

Baki bude laure ke kallon lantana Dan Bata taba zatton Haka daga gare taba,Haka tanaji tana gani suka fice daga gidan suna tafawa.

Kuka laure ta sake tana data sanin halin data saka kanta duk adalilin hudubar lantana.

In takaice Miki yanzu laure saidai Wanda yaga ALLAH da (annabi)ya dauka ya bata.

Lantana kuwa tun daga lokacin Bata kuma waiwayar garin Nan ba.

Ajiyar zuciya*SAFNAH*ta sauke hawaye ke bin  fuskar ta idon ta kuwa duk sun canza kala,lallashinta mom ta shigayi  da kyar suka samu ta kwanta tayi barci,dakin mahaifin maimuna aka Kai *NASIR*da kannan mahaifin sa, maimuna kuwa babu yanda innar ta Bata yiba kanta tafi gida inyaso gobe ta dawo.

KARSHAN WAHALA 2019Where stories live. Discover now