chapter 21

921 70 3
                                    

💗💗💗Karshan wahala 💗💗💗 💗
By

Safnah aliyu jawabi

Brightest hope ass 🌸💮

Most man hate their father for getting another woman after their mother's but they're actually heading in the same direction..
Deting 3girls at the same time..
                                         
Bismillahi rahamanin Rahim

Shigewa gida mukayi kuwa da abinda yake tunani game da lamarin rukkaya sa'id kamar yanda ta fada Mana sunan ta.

Afeeya daki ta shige nikuwa afalo na zauna na ci abinci na ina gamawa na dauki kular na shigar dashi kitchen sannan Nima na haura saman akwance na Sami afeeya harta Soma barci  da kamar na tayar da itah saidai nabar ta kawai Dan tasamu ta huta..
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

Itah kuwa basi  bayan ta farka daga nannauyar barcin daya dauke ta Mai buhun kudi tagani zaune Yana  Kari Mata kallon sunkuyar da kanta kasa tayi Dan gabaki daya wani nauyin shi ta keji ni kuwa nace daga baya kenan lol😜😜😜😜  .

shikuwa cikin sauri ya nufi gurin ta Yana tambayar ta ko akwai abinda take da bukata girgiza Kai tayi alamar aa haka dai suka kasance duk wani motsi da tayi saiya tambaye ta abinda take da bukata.

Ganin hakan ta yacimma ruwa ta Kara marairaicewa tace"ninini dai gaskiya bana son komawa gidan hajiya.

Kara matse ta yayi kamar za'asace Masa ita yace"meyasa?
Baki tunanin zatace anyi Mata ba daidai ba?

Shiru tayi na Dan lokaci  sannan takara marairaicewa tace"shikenan tunda so kake mutane surinka Gane maka Ni.

Girgiza Kai yashiga Yi sannan yace"Lailai baby sai yanzu na Kara yarda kina masifar so na,to indai Haka nee  akwai bukatar asaya Miki gida domin bazan iya shering dinki da kuwa ba.

Kara shigewa jikin sa Taya tana bin kowani lungu da sako na jikin shi tana lasa.

Nan danan kuwa ya amshi sakon da take son aika Mishi,Saida suka kusan awa daya suna Abu daya daga bisani yaso so Lula birnin masar saidai Sam Taki amincewa Dan haryanzu ba karamar azaba take jiba kawai daurewa take,Dan samun biyar bukatar ta.

Babu Bata lokaci yakira yabada umarnin anima Masa gida daga yau zuwa gobe.

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

Itah kuwa hajiya tun wayewar garin take niman layin basi Amma Bata shiga gashi babu halin Kiran Mai buhun kudi,Haka dai ta hakura ta zauna zaman jiran ta .

Tana zaune saiga sallamar lantana cike da sakin fuska ta amsa Mata  bakaramar ma'maki abin yabata ba Dan idan kaga hajiya tana maka irin wannan murmushin to tabbas ta samu.

Cikin girmamawa suka gaisa lantana ce ta fara cewa"hajiya ya mutumiyar taki?

Washe baki tayi kamar gonar audiga tace"kidai Bari yarinya irin arziki irin albarka.
Nandanan ta kwashe labarin abubuwa da ta samu asanadiyar basi harda gida wace Mai buhun kudi ya Bata.

Banda zufa babu abinda lantana takeyi ayanzu bata da wani buri  daya wuce ganin basira itama ta kwashi rabon ta.

Muskutawa tayi sannan tace"to hajiya akiramin basirar mu gaisa Dan dama cewa nayi Bari nazo na karbi abinda tasamu na aikawa mahaifiyar ta Dan kwana kin baya harcewa tayi idan ba'asamun kudi adawo Mata da diyar...

Dakatar da ita hajiya taye tana cewa in banda abinki lantana ke kuma sai ki fadawa basi wannan zancan?ai saiki kashe Mana hanyar cin abinci.

Murmushi mugun ta lantana tayi tana aiyana lokacin rabuwar basi da hajiya yayi Dan bazata taba yarda hajiya taci arzikin itah kadai ba.

Mikewa hajiya tayi ta shiga ciki ba'afi mintina biyar ba saigata tafito dauke da rafar dubu dubu ta mikawa lantana.

Garin sauri hannun lantana har rawa yake,godiya tayi sannan tace"to hajiya zantafi idan basira ta dawo afada Mata nazo bansame taba.

To kawai tace acikin ranta kuwa tunanin yanda zata raba basi da lantana take.
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

Washa garin mukayi Shirin makaranta atsanake kamar yanda muka Saba saidai yau malam idi NE zaikaimu Dan daddy sammako yayi,hakan ba karamar dadi yayi minba Dan Sam bana kaunar hada ido dashi.

Muna fita muka tarar malam idi mukawai yake jira atare muka shiga motar muna fita daga get na tsinci kaina da dube duben Dan son na gasgata maganar rukkaya nacewa kowanni safe tana zuwa dubani.

Aikuwa Ina juyawa muka hada ido daga min hannun tayi Nima na daga Mata, ganin na daga hannun yasa afeeya abin hannun nawa da ido aikuwa tana ganin rukkaya ta gallama Mata wata uwar harara.

Dasauri ta sauke hannun ta nan take na tsinci kaina da Rashin jin dadin hakan,saidai bance Mata komai ba Dan haryanzu ban mance da matsayi na agidan ba.

Har muka Kai makaran ta babu Wanda yasake yiwa wani magana fita nayi da niyar wucewa aji saidai me Jameel nagani agaba na Yana murmushi nidan ma mayar Mishi da martanin murmushi nayi sannan yace"ina kwana sarkin gudu.

Sunkuyar da kaina nayi Ina wasa da yatsun hannu na sannan nace"kayi hakuri good morning sir.

Amsawa yayi sannan yace kozan iya sanin dalilin kukan da kikayi jiya?

Tambayar tazo min abazata shiyasa nayi shiru Dan ban tanadi amsar da zanbashi ba.

Ganin shirun yayi yawa yasa yace"to shikenan tunda bazaki fadamin yanzu ba Amma kimin alkawarin bayan antashi Zaki fadamin.

Nabude baki da niyar magana naji ance karka damu Ni zanfada maka tunda bataso kasani.

Duk kanmu juyawa mukayi cikin sauri ,ganin afeeya atsaya ta hada hannun ta yasa na tsinci kaina da faduwar gaba kirjina sai dukan uku uku yake cikin karfin hali nace.....

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

Kuyi hakuri kasancewar Kun jini shiru kwana biyu wallahi abubuwa ne sukamin yawa Ina fata zaku gafarce Ni ..INAh YIN KU IRIN TOTALLY..

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
Saidai gaskiya bana ganin vote comment follow dinko kusani yin hakan shine zai bani kwarin guiwa  love you all ❤️❤️❤️❤️❤️❤️

R I P mother 🙏🙏

KARSHAN WAHALA 2019Where stories live. Discover now