chapter 22

965 62 0
                                    


❄️❄️❄️❄️❄️
*KARSHAN WAHALA*
                     ❄️❄️❄️❄️❄️❄️

*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*💥
_(THE STARS THAT SHINE IN THE WORLD OF WRITER'S)_

https://mobile.facebook.com/Taurari-Writers-Association-109116734087974/?ref=opera_speed_dial

         *T. W. A✍🏻*






*STORY*

&

*WRITING*

*By*

*SAFNAH ALIYU JAWABI*

2️⃣2️⃣➖2️⃣3️⃣

*BISSMILLAHI RAHAMANIR RAHIM*

,,,,,"Kinga my sweet afeeya mutafi kinga ina da test,cikin sauri na wuce na  barsu atsaye,saidai ina shiga class na kifa kaina saman kujera na saki wani marayar kuka  duk ƴan ajin tsayawa sukayi suna kallon na.

Saida nayi mai isar ta sannan na dago kai anyi sa'a kuwa babu wani malamin daya shigo cikin ajin,ina daga kai na ga gabaki dayan yan ajin sun zuba min na mujiya.

Da sauri na shiga share hawayan dake zarya a kunci  na,babu Wanda yamin magana acikin su sai wata yarinya wace tunda muke ajin ban taba jin tayi koda magana dawani ba, asalima ban taba jin koda  muyar taba.

Zuwa tayi ta dafe ni tace," baiwar ALLAH ke kuwa meke damun ki kike kuka haka?

kakalo murmushi nayi nace," babu Komai kawai kaina ne kemin ciwo.

Ita dinma martanin murmushi ta mayar min tace,"shine kike kuka haka?gaskiya mummy ta shagwaba ki da yawa.

Murmushi nayi nace,"nagode sosai da nuna kolawar ki agareni.

,"Babu komai ai yiwa kaine,ni sunana nusaiba aliyu kefa?

"Safnah aliyu.

Murmushi taye tace la kinga sunan dadyn mu daya dake awace unguwa kike?

Atakaice na bata amsa," tirkaniya tashar na Magi.

,"ALLAH sarki muna da dan nisa ni kuma kinga abarnawa nake layin kotu.

,"ALLAH sarki nace na kama bakina nayi shiru.

Ganin nayi shiru yasa tace,"bara na barki ma karasa maganar anjima karna da meki da surutu.

Tsayawa nayi ina kallon ta dan maganar ta bakaramar ma'maki yabani ba matar da maganar nata ma bawani fitowa take sosai ba, idan bakasa hankali bama ba Lailai bane ma kaji  abinda take faɗa.

,"Too kawai nace mata.

Muna zaune malam dazai mana test ya shigo,cikin sa'a muka gama muka fito da niyar wucewa gida,saidai mee kaf naduba Jameel babu shi babu alamun shi, cikin dube dube na,na hangeshi can nisa dani.

Ajiyar zuciya na sake dan rashin ganin shi bakaramar tayar minda hankali yayi ba,cikin sauri na nufi inda yake tsaya jin antsaya agaba na yasa naja na tsaya,nusaiba ce atsaya tana murmushi tace,"shikenan safnah daga tashi kuma saina nime ke na rasa?

KARSHAN WAHALA 2019Where stories live. Discover now