chapter 26

937 57 1
                                    

*KARSHAN WAHALA*

*STORY*

&

*WRITING*

*BY*

*SAFNAH ALIYU JAWABI*

*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*💥
_(THE STARS THAT SHINE IN THE WORLD OF WRITER'S)_

https://mobile.facebook.com/Taurari-Writers-Association-109116734087974/?ref=opera_speed_dial

         *T. W. A✍🏻*

2️⃣6️⃣➖2️⃣7️⃣


*BISSMILLAHI RAHAMANIR RAHIM*

Nusaiba ce rike da kugu tana huci kamar wacce tayi tsiren gudu.

Cike da ma'maki muke kallon ta dan sam bamuji zuwan taba.

Kallon na tayi tace,"bazai taba yauwa ba, kan mee zaki sadaukar da abinda kike so saboda wata can?

Murmushi nayi wanda iyakar ta fatar baki nace,"bazaki gane bane nusaiba, afeeya ta min halalcin da babu abinda bazan iya sadaukar mata dashi ba,itace ta zama sanadiyar farin cikin da nake ciki ayanzun.

"To yanzu mekike nufi?

Nidai alfarma daya nake so kumin,
Dan ALLAH kar wanda ya fada wa Jameel halin da nake ciki gamee dashi, dan ALLAH mu hada kai domin samun biyan bukatar afeeya karike maganar nayi ina kuka wanda daka jita zakasan daga kasar zuciya ta take fitowa.

Shirune ya dan ratsa gurin Mustafa ne yace,"ki daina kuka IN SHA ALLAH zanyi iya bakin kokari na dan janyo hankalin shi zuwa gareta idan yaso daga baya sai musan abinyi .

Murmushi nayi nace,," babu abinda zan iya biyan ka dashi mustafa ALLAH ya  saka maka da alkairi,daga ido da zanyi na hango afeeya cikin sauri na shiga goge hawayan dake kan fuska ta.tana kara sowa cikin dakewa tace,"shine kika wani zo kika zauna anan ni inacan inata nemanki ko?

,"Aiya kiyi hakuri wallahi kina cikin raina,tashi nayi mukayi musu sallama muka nufi gida.

Muna shiga toilet na fada nayi kuka na har sada na gode ALLAH, sannan nafito idona duk ta canza kala kwanciya nayi babu dadewa barci ya dauke ni ban farkaba saida naji ana ta kiran sallar magrib, da addu'ar tashi abarci abakina na tashi toilet na fada nayi alwala sannan na gabatar da sallah.

Addu'a nayi tayi domin ALLAH yacire min son Jameel azuciyata ,idan bazai zama alkairi agare ni ba.

Tabbas addu'a itace makamin mumini, domin kuwa kaso hamsin cikin dari yaragu na yanda nake ji game da shi
Hamdala nayi sannan na nufi falo dan naji ciki na yafara kiran ciroma,abinci na diba wanda zai ishine ci, na zauna na fara ci jin tsayuwar mutum nayi abaya na juyawa nayi cikin sauri dan ganin waye.

Tashi nayi cikin sauri har ina kware wa daddy ne tsaye yana kallo na wanda gabaki daya kamar ma ba'ahaiyacin sa yake ba yace,"wallahi kinkusa zuwa hannu na kwanan nan kinji na fada miki ki zauna cikin shiri yana kaiwa nan yayi ficewar sa batare da ya kuma cewa komai ba,nima kuma Haka addu'a nayi na koma naci gaba da cin abinci na.

KARSHAN WAHALA 2019Where stories live. Discover now