chapter 35

820 64 3
                                    

💖KARSHAN WAHALA 💖

💖By💖

💖Safnah aliyu jawabi 💖

💖Brightess hope write association 💖

💖Wannan chapter naku ne masoya 💖

*Maimuna aliyu*

*Shafa'atu said *

*My second self suwaiba said*

*Hajara umar*

*Fatima Umar*

*Amina umar*

*Aisha umar*

*Safiya umar*

*Ameera Hassan*

*Sani Hassan*

*Amir Ibrahim*

*Abbul kair *

*Aslam Ibrahim*

Ina godiya sosai da nuna soyayar ku agare ni Ina alfahari daku (love you all)

Bismillahi rahamanin Rahim

Da sauri mom ta nufo gurin sukuwa jin yanda suwaiba take ihun Kiran mom yasa suka dawo cikin haiyacin su kallon ta suke ciki da ma'maki.

Cikin sauri mom ta karaso gurin ganin su atsaye yasa ta bata Rai tana tambayar suwaiba dalilin kiran"meya faru kike min irin wannan kiran?

Shiru tayi Dantama rasa ta inda zata fara, dago ido tayi aikuwa suka hada ido da tsaka tselle daya tayi sai gata jikin *NASIR*ta makalkale shi girgiza ta yake yana tambayar,ta Dan zuwa lokacin sun dauka wani abinne yasa meta, nuna mishi tsakan tayi da hannun jikin ta har rawa yake.

Cikin sauri ya mannata jikin *SAFNAH*sannan ya ciro takalmin shi duka daya yayiwa tsakan ko motsi bata kumayi ba,dauka yayi ya jifar sannan yadawo kusa da ita Yana zolayar ta,ita kuwa mom ganin bashida niyar kyale mata yar'utar ta yasa ta jinye ta suka shige daki.

Binsu abaya*SAFNAH*tayi tana murmushi, shikuwa dama aiki zai fita baitsaya bata lokaci ba yafita da kewar ta cike far cikin ransa ,wannan kenan

Ina ganin haka*NI SAFNAH ALIYU JAWABI nayi sauri na dauko gyale na na nufi bangaran Jameel da afeeya su rukkaiya da nusaiba anko to dafan masu karatu Basu manta da suba muje zuwa...

Cikin sauri Jameel ya juyo Yana bin bayan mota da kallo Dan shidai inba idonsa ke masa gizo ba, to tabbas yaga fuskar*SAFNAH*acikin motar can,gani ya tsaya Yana bin mota da kallo yasa mustafa yace"yadai?

"Wancan motar data fita Naga mai kama da*SAFNAH* aciki.

Dariya mustafa keyi harda rike ciki ganin Raina masa hankali mustafa ke son yi yasa Kai yafara tafiya, cikin sauri Mustafa yasha gaban shi yana cewa,"haba abokina me kuma abin fushi anan.

Cigaba da tafiya yayi batare da ya kula shiba, shikuma sai faman magiya yake har suka isa dakin,kallon dakin yake kirjinsa na dukan uku uku, cikin sauri ya nufin wata Norse daya gani tsaye ta juya baya,baya iya ganin fuskar ta, sallama yayi mata dake tana sanye da farar hijab hakan ne ya tabbatar mishi cewa musulma ce.

KARSHAN WAHALA 2019Where stories live. Discover now