chapter 5

1.3K 81 2
                                    


❄️❄️❄️❄️❄️
KARSHAN WAHALA
                      ❄️❄️❄️❄️❄️❄️

*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*💥
_(THE STARS THAT SHINE IN THE WORLD OF WRITER'S)_

https://mobile.facebook.com/Taurari-Writers-Association-109116734087974/?ref=opera_speed_dial

         *T. W. A✍🏻

STORY
&
WRITING

BY

SAFNAH ALIYU JAWABI

Dedicated to ya Muhammad karim

BISSMILLAHI RAHAMANIR RAHIM

0️⃣➖5️⃣

,,,,Hajiya Fatima itama saboda sanin hali irin na aunty ummi shiyasa ta dan yi murmushi tace," kawar suwaiba ce.

aunty ummi tace," ALLAH sarki me
ya sameta naga duk fuskar ta bandej?

  ƙosawa da tambayar ummi Hajiya Fatima tace," atsari ta samu ne wallahi .

,"ALLAH yakiyaye nagaba ana cikin haka ikram ta fara hamma alamar barci take ji.

nan take aunty ummi tace,"yar mama tashi kije ki kwanta kinsan gobe, tunda safe zamu bar garin nan.

Marairaice fuska  ikram tayi  tace,"to mum, aunty saida safe.

kallon  suwaiba Hajiya Fatima tayi tace,"ke kuma ku tashi koje ku kwanta.

Lokaci ɗaya suka mike suka nufi daki, ganin haka yasa
Nasir shima  ya miƙe yanufi nashi bangaran cike da farin ciki, domin kuwa yaji dadin tafiyar dasu aunty ummi zasuyi gobe.

*****

Tun misalin karfi goma aunty ummi
da ikram suka nufi hanyar abuja hakan bakaramar dadi yayiwa nasir ba ,domin kuwa ta haka ne kawai zasu samu damar
Jin labarin wannan yarinyar.

agurin suwaiba da hajiya Fatima abin bai sake zani ba ,domin suma akage suke da son jin labarin SAFNAH.

Bayan tafiyar aunty ummi, hajiya takira suwaiba tace," little jike kira min son da wannan yarinyar
Ciki mintina bayar duk kansu suka hallara a cikin falon donamsa Kiran hajiya.

hajiya Fatima takai duban ta ga SAFNAH tace,"to baiwar ALLAH kamar yanda mukayi alkawari zaki fada mana dalilin daya sa kikace bakida kowa shiya tara mu anan ga baki dayan mu muna sauraran ki.

Lokaci idanuwan ta suka canza kala zuwa ja hawaye ke kwaranya kamar an ansaki pp ,gabaki ɗaya tausanyin ta yagama lulluɓe ruhi da gangar jikin su,amma dole suka hakura don kuwa jin labarin ta shine kawai mafita agunsu.

Ɗago kai tayi tace,"Da farko sunana SAFNAH, ni ƴar asalin jahar Niger state ce karamar hukumar izom, mahaifina bafulatanin kauyan izom ne, sunan sa ALIYU amma ana kiran shida malam jauro.

"Mahaifina yakasance yanada mata daya sunan ta laure, sunshafe tsawan shekaru goma sha uku da aure, amma laure ko batan wata bata taba yiba,
Hakan baitaba damun malam jauro ba.

,"Asalima baitaba magana akan hakan ba,domin koda laure ta zomai da maganar yakan ce mata,"laure ki kwantar da hankalin ki,ni banga abin damuwa anan ba, domin kowa
ALLAH shiyake bayar wa a duk lokacin da yaso.

"Idan da rabon zamu rike dan mu da hannun mu,"
Idan kuma ba muda rabo ALLAH yasa haka shiya fi zama alkairi, ki daina saka damuwa aranki kinji laure ta?

"Akowani lokaci idan laure da malam jauro sukayi hira irin wannan takan jinjina imani irin na malam jauro
Sannan ta kanyi farin ciki da ALLAH ya azurtata da miji Mai kaunar ta.

,"Ana cikin haka wata rana malam jauro ya fita kasuwa,suna zaune da abokin sa maisuna dantani, dantani yace" dama kuwa jauro inaso na baka wata shawara amma inah jin tsoro.

murmushi malam jauro yayi yace,"haba aboki na meyasa zakaji tsoron bani shawara karfa kaman ta tun muna yara muke abota.

sauke nannauyar ajiyar zuciya yayi ,"yace to dama bawani abu bani illa dama so nake na baka shawara game da karin aure.

Nantake annurin dake fuskar malam jauro ya bace,yace,"dakata dantani
Ni banida niyar kara aure,domin kuwa babu abinda laure tarage ni dashi ,duk abinda nake so tana kokarin taga tamin.

Gyara zama dantani yayi  yace,"
jauro shin baka ganin yanda lokaci yake tafiya? shin Kai baka bukatar kaga gudan jinin ka aduniyar nan ne?

,"Haba gaskiya kayi tunani.

murmushi malam jauro yayi yace," dantani kasani shi samu da rashi duk daga ALLAH yake, sannan ina girmama soyayar ka agareni domin masoyin kane yaka fada maka gaskiya don haka karka damu nayi maka   zanyi shawara akai.

nantake dantani ya fadada murmushi akan fuskar sa danshi baizacci malam jauro zai dauki shawara shi da sauri haka ba.

Ahaka dai suka rabu kowa yakama hanyar zuwa gida kasancewar magriba ta gabato

*"****"****
Ko da malam jauro yakoma gida baisanar da Laure yanda sukayi da dantani ba saidai maganar tanayi mishi yawo azuciya,
cikin dare ma kasa barci yayi, Yana tunin yanda zai bulluwa al'amarin ta yanda laure bazata dauka yayi mata cin fuska ba ,da haka har barci barawo yadauke shi.

Koda safiya tayi malam jauro yafita kasuwa, dantani yatare shi da tambayar,saikawai malam yace ya amince da batun karin auran.

nantake,dantani yayiwa ANNABI salati yasanar da ubangijin sa sannan yace,"malam jauro,ni kuwa idan ba zakace nayi maka shishigi ba dana baka Maryam.

cike da ma'maki malam jauro yace," wace maryam?

Murmushi dantani yayi yace," Maryam yar waje na man...

tun kafin dantani yakarasa maganar sa malam jauro ya  dakatar dashi 🖐️🖐️yace," haba dantani wannan wace iriyar magana ce? ,"gaskiya bazan iya auran yarinyar da take kallon na a matsayin uba ba gaskiya ka canza shawara.

Murmushi dantani yayi akaro na biyu yace," karka manta sayidina abubakar ( radiyal lahu ta'ala anuhu)ya aura wa ANNABI MUHAMMAD (S A W) nana AISHA ,to menene danna baka Maryam zakace a a saidai kace baka so ka hada zuri'a dani.

,"Ciki sauri malam jauro yariki hannun dantani yace," ba haka bane aminina ,kawai dai bana so atauye wa yarinyar hakkin tane shiyasa nace haka," amma idan kana ga babu matsala to na aminci ALLAH ya sa haka shiyafi zama alkairi.

Sosai dantani ya nuna tsantsar farin cikin sa daji amincewar babban Aminin sa  yace ,"dayar dar ALLAH babu wata matsala.

da haka kowa ya wuce gida dan fara shirye shirye.

shikuwa malam jauro babu abinda ya
Tsaya mishi arai ilah, dawace fuskar zai fuskan ci laure ya fada mata zancen karin auran nashi🤔🤔🤔🤔.

Please Don forgot to comment

LOVE YOU ALL

KARSHAN WAHALA 2019Where stories live. Discover now