chapter 45

1.2K 74 5
                                    

❄️❄️❄️❄️❄️
*KARSHAN WAHALA*
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*💥
_(THE STARS THAT SHINE IN THE WORLD OF WRITER'S)_

https://mobile.facebook.com/Taurari-Writers-Association-109116734087974/?ref=opera_speed_dial

*T. W. A✍🏻*

*STORY*

&

*WRITING*

*By*

3️⃣5️⃣

*SAfNAH ALIYU JAWABI*

*BISSMILLAHI RAHAMANIR RAHIM*

,,,,Fitowa Jameel yayi Dan ganin masu sallamar,aikuwa ido hudu yayi da *SAFNAH* kasa dauke idonsa yayi daga kanta, ita dinma haka saidai akasar zuciyar ta ma'makin ganin sa agarin take, tunda a iya sanin ta dai bata taba fada mishi sunan garin ba.

Ganin sun tsaya suna kallon juna babu Wanda yayi wa wani magana yasa inna tace,"Kai jauro lafiya?ko kasan tane?

Sunkuyar da Kai yayi yace,"bismillahi KU shigo.

Shiga gidan sukayi Jameel ya dauko ta barma ya shimfida musu ita dai *SAFNAH*Banda binsa da ido babu abinda take.

Fadawa innar sa zuwan nasu yayi, sannan ya nufi dakin da aka sauke afeeya,Yana zuwa ya ganta kwance kamar Mai barci, Amma ba barci take ba da alamu tayi zurfi cikin tunani,tafa hannayan sa yayi ,sannan ta dawo daga duniyar tunani data shilla.

Murmushi ta sakarmai tana cewa," SOUL MATE ka tashi lafiya?

Murmushi ya mayar Mata yace,"taso Ina da albishir agare ki.

Tashi tayi cike da zumudi tabi Bayan sa,bai tsaya ko ina ba sai inda*SAFNAH*take zaune lokacin it kuwa kanta akasa tayi zurfi cikin tunani.

Jin tsayuwar mutum agabanta yasa ta dago Kai cikin sauri Dan duk atunanin ta Jameel ne,suna hada ido *SAFNAH*tashi tsaye tayi tana kallon ta gabaki daya sun kasa magana kowa Kuma sai kallon su yake musamman ma *NASIR*da tun zuwan su yaji jikin sa yayi sanyi ga wani irin faduwar gaba da yake fama da ita.

Rungume juna sukayi suna kuka na tsayin lokaci, sannan suka sake juna share hawayan afeeya tayi tace ,"bara na kira mummy.

Fitowa sukayi atare harda daddy baki bude suke kallon ta cike da ma'maki.

Innar Jameel da Yan uwan ta kuwa gabaki daya sun rasa gane abinda ke faruwa Dan haka suka tsaya suna kallon juna.

*NASIR*kuwa ganin kuwa yayi shiru Amma *SAFNAH*kamar cewa ake ta kara,kallon ta yayi yace,"ya Isa ki daina kuka kar kanki yayi ciwo,su wayannan su waye Dan Naga basuyi Kama da Yan garin ba?

Tsagaita kukan ta tayi tace,"wannan itace afeeeya da iyayan ta dana Baku labari , Wannan Kuma shine Jameel.

,"Ikon ALLAH.

"Haka ALLAH yake lamarin sa duk inada yaso babu Mai hanawa.

Inna maimuna da iyayan Jameel kasa magana sukayi Dan basusan abinda ke faruwa ba ganin an gindayar dasu yasa*SAFNAH*mikewa tsaye ta fara basu labari dalla dallah babu Wanda ta buye musu.

KARSHAN WAHALA 2019Where stories live. Discover now