chapter 43

804 65 2
                                    

❄️KARSHAN WAHALA❄️

❄️By❄️

❄️SAFNAH ALIYU JAWABI❄️
(B*H*W*A)
❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️ SAFNAH
❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️
ALIYU❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️
❄️❄️ JAWABI

❄️Bismillahi rahamanin Rahim❄️

Daga cikin garin izom Saida sukayi tafiyar mintina talatan kafin so Isa rugar.

Cike da farin ciki *SAFNAH*take kallon garin duk Wanda ya kalle ta alokacin yasan tana cike da farin cikin sake saka kafarta a mahaifarta.

Ganin sabuwar mota Kal yasa yaran garin suka taru suna taba motar.

kallon juna suwaiba da
*NASIR*sukayi duk yanda yaso ya rike dariyar sa ina Saida yadan dara Dan kam gaskiya baitaba ganin yara suna haka ba saidai ya halakanta hakan da kasancewar garin kauye ne.

Ita kuwa gogan da gudu ta shige gida tana Kiran Inna nadawo Inna ina kike?

Jin shiru babu amsa yasa ta shiga dakin tana dube dube,can gife ta same ta kwance duk jikin ta ya baci da bayan gida, ga wani irin wari da ke tashi ta kowani lungo da sako na dakin,toshe hancinta tayi cikin sauri tsabar wari har wani jiri take gani.

Tuna cewa tabar mutane awaje yasa ta yanke shawarar daukar su zuwa gidan su maimuna, tunuwa da tayi da Hakan yasa ta fita da gudu ko kallon ida suke batayi ba ta nufi gidan.

Kallon *NASIR*mom tayi tace,"to Kai kuma yau anbawa matar ka aikin gudu.

Duk dariya sukayi atare.

Ita kuwa da gudun ta tashiga gidan tana cewa,"maimuna ta Ina kike inna kufito nadawo.

Anyi sa'a lokacin maimuna tazo ganin gida Dan ta dade dayin aure tun bayan kammala o level ta samu wani karamar makaranta tana koyarwa bayan auran ta da shekara ta haifo diyarta mace kyakyawa Rana suna maimuna ta cire kunya tace itafa saidai asaka wa yarinyar sunnan kawarta, Da Haka yarinya taci sunan *SAFNAH*

Don ita duk atunanin ta tadade da rasuwa shiyasa akoda yaushe take saka ta cikin addu'ar ta.

Da gudu ta fito daga dakin Dan son gasgata muryar da take ji ,aitana ganin ta saita fara jada baya taba cewa,"kiyi hakuri karki cutar Dani Wallahi banyi Miki komai ba lokacin da kike raye kema sanin kankine ban taba cutar dake ba.

Ma'maki ne zaune samar fuskar ta Dan gabaki daya ta kasa
Gane inda maganar ta dosa,ganin tana da niyar arcewa yasa ta daka mata tsawa tana karasowa inda take,ita kuwa har sakin fitsari tayi agurin.

Ahankali take taku harta isa gari ta rungume ta tayi tana kuka Mai tsuma zuciya,ganin ta rungume ta batare da sun bace ba yasa itama ta rungume ta, kuka suke kamar ALLAH ya Aiko su Saida sukayi Mai isarsu sannan cikin karfin hali maimuna ta janye jikin ta tana kare mata kallon Dan sai yanzu taga canje canjen da aka samu atattare da ita.

Rungume ta tayi akaro na biyu tana cewa,"Ina Kika shiga?meyasa baki dawo gida ko sau daya ba?abubuwa da yawa sun faro bayan tafiyar ki.

KARSHAN WAHALA 2019Where stories live. Discover now