chapter 24

808 62 1
                                    

KARSHAN WAHALA

By

Safnah aliyu jawabi

🌲💖🌲💖🌲🌲💖🌲🌲💖
💖🌲💖💖🌲💖💖
🌲💚💖💚💖💚 💖 🌲
💖💖💖💖
🌲 💖💖💖🌲
🌲🌲

Bismillahi rahamanin Rahim

Tashi tayi ta shiga ciki tana shiga ciki ta fada kan katifar dakin kwanciya tayi ta rinka risgar kuka iya karfi ta,saida tayi mai isa ta sannan ta tashi ta fada toilet,tana fitowa ta samu suwaiba azaune da alama ita take jira ta isa bakin gadon ,suwaiba tace,"ina mai baki hakuri kan abinda yaya yayi miki dazu.

Kama hannuwan ta tayi tace,"kinga ni kam babu abinda yaya ya yimin.

To shikenan tunda haka kika ce amma kisani tausayi ne ya hana shi barinki ki karasa labari...

Sallamar da akayi shiya hanata karasa maganar.

Cikin sauri ta nufi kofar ta bude nasir ne atsaye ya hade hannun sa guri guda,batare da yace da ita uffan ba ya karasa shigowa dakin, sunkuyar da kanta safnah tayi batace dashi uffan ba,ganin ba zatayi magana ba yasa yayi gyarar murya yace,"kiyi hakuri.

ni kaina bansan abinda yasa na kasa jure jin karshan labarin ki ba,amma ki sani aduk atsayin rayuwa ta bantajin labari makamancin nake ba,idan bazaki damu ba zanso jin karshan labarin ki,ina jiran ki afalo.

Baitsaya jin abinda zata fada ba yasa kai yayi ficewar sa.

Dago kai tayi tana kallon yanda yake tafiya jiki asanyaye,haka dai tayi sauri ta saka kayan da suwaiba ta zabar mata ta nufi falo dan amsa gaiyatar nasir.

Tana karasawa ta tarar da duk kansu aguri daya Saidai babu mai yiwa wani magana acikin su,karasawa tayi tayi musu sallama bayan sun amsa ta samu guri ta zaune nisa dasu kadan.

Dubanta mum c tayi tace,"kiyi hakuri kinji safnah halin yayan naku ne sai hakuri idan bazaki damu ba muna sauraron ki.

Batare da bata lokaci ba ta cigaba da basu labari kamar haka...

Kwanciya yayi saman jiki na, nandanan muka fara ko kawa,ganin zan Bata masa lokaci yasa yayi amfani da karfin sa ya janyo zanin gadon dake dakin ya daure min hannuwa na dasu sannan ya fisgo dan kwalin dake kaina ya rufe min baki dashi.

Ina ji ina gani ya rabani da rigar dake jiki na yana kokarin cire min zanin da na daura na jiyo muryar rukkaya tana koda sallama,saidai shi ko kadan baiji muryar taba abinda yake muradi kawai yake kokarin cimma.

Karar data kwalla ne ya dawo dashi cikin haiyacin shi cikin sauri ya shiga gyara zep din wandon shi da tuni ya zage ta.

Da gudu ta fita tana ihun niman taimako dan ita sambata ma gane daddy bane tsabar rudu data shiga.

Cikin sauri ya nufi dakin shi ya rufe.

Ni kuwa cikin sauri na shiga kukarin kwance daurin da yayi min,ina cikin haka nafara jiyo hayaniyar mutane kara harama nayi dan gyara rigar dake jiki na cikin ikon ALLAH na samu na kwance daurin hannu daya harna gyara rigata sannan saiga yaiyin rukkaya sun bankado kofar.

Da gudu rukkaya ta zo ta kwance ni sanna suka fara tambaya ta yanda abin ya kasance harwani ya shigo cikin gidan batare da Mai gadi ya ga shigowar sa ba.

KARSHAN WAHALA 2019Where stories live. Discover now