chapter 30

898 63 2
                                    

🌵KARSHAN WAHALA 🌾

🌲WRITING BY SAFNAH ALIYU 🌲
🌲JAWABI 🌲

♒♒♒♒♒ ♒♒
♒♒♒♒♒♒♒
KARSHAN ♒♒♒♒♒♒♒
♒♒♒♒♒♒♒
WAHALA ♒♒♒♒♒♒♒♒
♒♒♒♒♒♒♒♒

Follow Istagram official safnah aliyu

Watpad Safnah aliyu jawabi

👩‍❤️‍👩WhatAPp group keep your number

Facebook safnah aliyu jawabi
👩‍👩‍👦‍👦Facebook group Safnah aliyu jawabi fan
🐉🐉🐉🐉🐉🐉🐉🐉🐉

Bismillahi rahamanin Rahim

Jini ne ke bin baki na akedime afeeya ta rike ni tana kuka ni kuwa tuni na dade da fita ahaiyaci na Jameel kuwa fita yayi da gudu dan kiran likita.

Ko cikakkiyar mintina biyu baiye ba saiga shi sun dawo a tare da likitan
Ganin halin da nake ciki yasa ya kira sauran likitocin dan su taimaka mishi.

Suna zuwa suka umarci Jameel da afeeya da su tsaya awaje,badan sun so ba suka fita afeeya kasa tsayuwa tayi dan gabaki daya gurin koma wa yayi kamar duhu baya tayi zata fadi cikin sauri Jameel ya riko ta,mannata da jikin shi yayi,wani irin shok sukaji atare saurin cire ta yayi daga jikin shi yace,"karki saka damuwa aranki afeeya IN SHA ALLAH babu abinda zai faru da safnah kinji.

Nod dakai kawai tayi ta samu guri ta zauna.

Saida likitocin suka kwashe tsawan awanni biyu akaina sannan suka samu komai ya koma normal, sannu ahankali suka fara fita daya bayan daya harya rage mutum daya,yana fitowa cikin sauri Jameel ya nufi shi yana tambayar shi jikin nawa.

Baice komai ba saima nuni da yayi mishi kan ya same shi a office.

Binshi yayi abaya ita kuwa afeeya tuni harta dade da shiga inda nake barci nake wanda kana gani kasan barcin wahala ne kawai rungume ni tayi tana kuka tana cewa,"wannan wani irin abune meyasa daddy zai zama silar rushewar farin ciki na, shin baisan ke din ta daban bace arayuwa ta.

Turo kofar da Jameel yayi ne yasa tayi saurin barin jiki na ta koma dabda shi tana tambayar shi abinda likitan yace?

Shiru yayi nadan mintina sannan yace,"dan ALLAH afeeya zan tambaye ki, shin safnah ta taba fada miki wani abunda ke damun ta ko da akwai wani abunda take so wanda take ganin baxata samu ba,da yasa ta cikin damuwa har yake niman haifar mata da ciwon zuciya?

Dafe kirji tayi nandanan saiga hawaye
Cikin kuka tace,"nidai bansan komai ba sai dai anyi wani lokacin da idan na tashi da daddare saina ganta saman sallaya tana kuka tana kaiwa ALLAH kukan ta wani lokacin naji tana cewa ALLAH yasa yasonta kamar yarda take sonshi.

Ranar babu irin tambayar da ban mata ba amma Bata fada min ba.

Duban ta yake cike da ma'maki yace,"shin da akwai wanda safnah ta ke zance da shine?

A a

To bayan ni akwai wanda kukayi sabo dashi kamar yanda muke ayanzu.

A a gaskiya babu bayan ni saika saikuma nusaiba da rukkaiya kawai safnah ta sani agarin nan bayan daddy da mummy.

Tashi tsaye yayi cikin sauri ya fita ita kuwa afeeya rudani iya rudani ta shige ta mattuka, domin kuwa ta taba ji alabari cewan duk wanda ya kamu da ciwan zuciya to samun saukin sa abu daya ne asama masa abinda yake so,indai haka ne kuwa tashiga uku awani duniyar zata samarwa safnah abinda take so idan ya kasance kan wannan saurayin ta fada cikin wannan halin ba.

KARSHAN WAHALA 2019Where stories live. Discover now