chapter 20

992 76 1
                                    

Karshan wahala

Brightest hope ass🌸🌸💮

SAFNAH ALIYU JAWABI

"So let my enemies say what they want.becouse my sin are many,and perhaps because of their backbiting and slender my sins will be lightened and instead fell upon your shoulder."

Cike da tsoro take tambaya ta ,"tace baby safnah meya faru?kasa Bata amsa nayi domin kuwa ko giyar wake nasha bazan iyah fada Mata abinda kunnuwa na suka jiye min ba.

Sai alokacin ta lura bama itah nake kallon ba juyawa tayi domin ganin abinda ya dauke min hankali tana juyowa sukayi ido hudu Dan tsabar rudewa ma bata Lura da wanzuwar shi agurin ba sai yanzu cike da mamaki take kallon shi saidai dake namijin duniya ne sai ya sakar Mata murmushi sannna yace,

"sweet heart meya samu diyar taki?
Ba'itah ba harni Saida na sauki wata boyayyiyar ajiyar zuciya duban shi tayi sannan ta dawo da dubar ta kaina tace"wallahi precious bansan meki damun baby safnah ba, babu irin tambayar da banmata ba Amma taki fadamin juyowa ta karayi ta kalle Ni sannan tace"kodai kinajin kewar gida ne?

Cikin sauri nace"eh wallahi mummy inah so naje Naga innah laure da kawata maimun kuka dayaci karfi nane ya hanani karasa maganar.

Rungume Ni mummy tayi tana Dan bubbuga baya na alamar rarrashi tace"karki damu yata nayi miki alkawarin Kuna samun hutu zansaka driver ya kai ku kinji?nod da Kai kawai nayi hawaye naci gaba da zuba. domin dai ALLAH shine shaida bazan iyah cigaba da Zaman agidan nan ba.

Fita nayi daga kichen din na nufi dakin mu inah zuwa na tarar haryan afeeya barci take saidai lokaci zuwa lokaci tana sauke ajiyar zuciya. tsayawa nayi inah kallon ta arainn kuwa inah jimamin rabuwa ta da afeeya motsin datayi ne yasa nayi saurin shigewa toilet.

Saida na Bata lokaci Mai tsawo sannan na fito,inah fitowa mukayi ido hudu da afeeya da murmushi na karasa inda take zaune.

"Sweet afeeya harkin tashi?
Nod da Kai kawai tayi sannan ta tashi tayi shegewar ta toilet Bata Jima ba saigata ta fito fuskar ta dai babu yabo ba fallasa.

Da murmushi nace barka da fitowa gimbiya agidan Jameel.

Nanda Nan kuwa tasa dariya tace,"kedai bakida dama wato idan kika yiwa mutum laifi kinsan hanyar da Zaki gyara laifin ki ko?

Nidin ma murmushi nayi sannan nace,"haba aizuwa yanzu yakai ace nasan duk wani Hali naki afeeya ta.

Atare muyi dariya sannan muku tafa Haka dai muna Hira itah Kuma tana saka kaya har ta gama duk da dai bawani kulliya tayi ba Amma tayi kyau.

Kallon ta nayi sannan nace"nidai kizo muje inah da kyauta Mai kyau dazan miki.
Ciki da zumudin son ganin abin ta ja hannun muka fito falo muna zuwa bamu tsaya ku inah ba sai dinning table muna zuwa tunkafin na fara bude abinci harta rigane ihu tayi tace,"wow bansan Dame zansaka Miki ba my sweet safnah inah alfahari dake.
Fadan hakan kuwa yayi daidai da fitowar daddy da mummy daga daki saiji mukayi an amsa da
cewa,"itah ma tana alfahari dake.

Juyawa duk kanmu mukayi da ma'maki Amma sai ganin su mukayi suna dariya,muma mukayi murmushi atare muka fara cin abincin ciki da kaunar juna saidai fa Ni ko cokali daya na kasa kaiwa baki na.

Lura da hakan da mummy tayi yasa ta dago tana tambaya ta"baby safnah ya naga baki cin abincin?

Murmushin karfin halin nayi sannan nace,"wallahi kuwa mummy gabaki daya ciki na ya kulle.

Juyawa tayi gun afeeya tace"baby kiyi sauri ki gama ku leka bakin dogo baxata rasa abinda zata siya ba ko Kuma kushiga gidan hajiya tasayo waina, kinsan wainar ta akwai dadi.

Cikin sauri nace,"yauwa mummy wallahi kamar kinsan abinda nake Jin ci kenan.

Afeeya ce ta Karbi maganar cikin shagwaba tace,"wato mummy da duk kannin alamu kinfi son safnah akaina,Dan harwani sauri ki kecewa nayi sanadin na shake.

Nidin ma kwaikoyar maganar ta nayi nace,"gaskiya nidai mummy kifada mata ta daina gasa Dani.

Duk kanmu mukayi dariya atare.
Zama nayi harsuka gama cin abinci daddy baice komai ba saima satar kallo na da Yake, Dana lura da Haka nayi saurin miki wa nace,"Kinga mummy idan na biye wa afeeya harsai wainar ta kare,cikin sauri na shige daki na dauko Mana hijaban mu.

Afeeya na ganina tace,"Kai safnah Nan da Nan ma saimun saka wata uwar hijabi?
Murmushi nayi sannan naja
hannun ta mukayi waje sai abakin kofa muka karasa saka hijabin.

Koda muka shiga cikin gidan wata budurwa muka gani dagani bazata wuce sa'armu ba,Mika Mata kudin mukayi ta zuba Mana harzamu wuce cikin sauri ta Miki tana cewa,"Dan ALLAH idan bazaki damu ba inah so nayi magana dake, ta nuno Ni .

Cikin hazama afeeya tace,"inah dai fata lafiya ko?

Nod da Kai tayi haryanzu dai fuskar ta dauke yake da murmushi.

Nidinma. murmushi nake,sabanin afeeya wace ta hada girar sama da na kasa guri daya,Ni abin nata ma dariya yabani sannan nace,"inah jinki saidai kiyi sauri Kinga ankusa Kiran sallar magrib.

Murmushi takuma yi sannan tace,"dama ba wani Abu bane inah dai so muyi kawance n....

Dakatar da itah da hannu afeeya tayi sannan tace,"ki Haka akeyi agarin ku? daga ganin yarinya sai kice kina Santa da khawa kin santane?dallah mutafi.

Tsayawa nayi inah kallon ta itah kuwa afeeya tsayawa tayi tana kallo na tana wuci kamar wace tayi gudu.
Sauke ajiyar zuciya nayi sannan nace,"kiyi hakuri afeeya ta bara naji dalilin ta.
Bantsaya jiran jin abinda afeeya zata ceba na juya nace,"baiwar ALLAH ko zaki iyah fadamin dalilin daya sa kike so muyi kawance bayan baki taba ganina ba?

Murmushi takuma yi nikuwa azuciya ta nace itah kuwa wannan murmushin baya Mata wahala.itah kuwa cewa tayi,"bayau na fara ganin ki ba saidai bantaba gigin Miki magana ba Dan bansan yazaki dauki lamarin ba,Amma ki yarda dani tun ranar Dana Fara ganin ki har Rana Mai kaman ta yau bantaba gajiya da zuwa kofar gidan kuba kullum sai Naga tafiyar ku makaranta sannan hankalina yake kwanciya.

sannan da zarar lokacin dawowar ku yayi nake tsayuwa abakin titin Nan harsai Naga dawowar ku,yauma da naga yar'uwar ki itah kadai ta dawo bayan tare kuka tafi makaran ta,ba karamar tashin hankali na shiga ba,haka dai nayi hakuri da yimiki fatan alkairi,sai gashi inah zaune ALLAH ya jefo ku cikin gidan mu shine naga yadace nayi miki magana.

Duk kanmu binta muke da ido cike da ma'maki har ta gama maganar sannan nace,"nagode sosai da nuna soyayar ki agare ni saidai kisani bani da ikon yin wata ma'amala dawani ko wata batare da izinin mummy na ba,saidai nayi miki alkawarin duk yanda mukayi da itah zansanar da ke.

Sannan sunana safnah itah Kuma afeeya kefa?

Murmushi tayi Wanda da alamu yazami mata al'ada tace," rukkaya sa'id sunana.

Sallama muka Mata sannan muka nufi gida kowa da abinda yake aiyanawa aranshi.....

Love you all friends

KARSHAN WAHALA 2019Where stories live. Discover now