chapter 41

728 68 5
                                    

🍇KARSHAN WAHALA🍇

🍇By🍇

🍇Safnah aliyu jawabi🍇

🍇 (B*H*W*A)🍇

🍇BRIGHTEST HOPES WRITERS🍇 🍇ASSOCIATION🍇

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
🍇🍇🍇🍇
🍇🍇
🍇
Bismillahi rahamanin Rahim

Jameel kuwa kallon su yake cike da ma'maki ganin wannan matar asume cikin sauri ya nimu ruwa ya yayyafa mata.

Da salati abakin ta, ta farka tana mutsuka ido harta bude su baki daya.ganin Jameel kusa da ita yasa ta miki cikin sauri tana cewa,"bawan ALLAH daga Ina? suwaye iyayan ka?awani gari kake?

Duk ajere tayi mishi tambayoyin,Saida ya daidaita natsuwar sa sannan yace,"Ni daga kaduna nake,iyaye na nazo nima agar...

Bai karasa maganar Saba matar ta janyo shi jikin ta, rungume Shi tayi da karfi kamar za'a kwace mata sannan ta fashe da kuka tana cewa,"ALLAH nagode maka daka baiyanar min da gudan jini na, ALLAH sarki malam Ina kake kaga jauro da idonka.ALLAH ya jikan ka nan dai ta kuma fashewa da kuka.

Jameel kuwa mannewa yayi ajikin ta Yana Jin wani irin natsuwa Wacce baita Jin makamanciyar sa ba.

Sauran mutanan kuwa zuba musu ido sukayi sai asannan ta tuna da akwai mutane agurin kuma Jameel shine danta na fari aibashiri ta ture shi ta fita waje da gudu.

Hakan kuwa ba karamar ma'maki ya bashi ba nan dai suka shigar tambayar sa yanda akayi yasan garin.

Labari ya basu riryan tiryan sukuwa Banda murna da farin ciki babu abinda suke.

Abla ya kira ya dauke shi amashin sannan ya sama musu Suma suka hau.

Tafiyar mintina talatin sukayi kafin sukai,rugace Mai yalwar mutane gwanin sha'awa ga ni'imantacan kamshi.

Shakar iskar garin yayi Yana murmushi kallon abla yayi yace,"Amma kamar bamu shigo garin nan bako?

Murmushi abla yayi yace,"bamu shigo ba.

,"Ikon ALLAH.

Karasawa cikin gidan sukayi, mutane daga kowani bangare na garin suka rinka zuwa ganin Jameel, mahaifiyar sa kuwa tunda ta mishi magana a asibiti Bata kara Masa magana ba ko da gaishe ta yayi saidai ta amsa da Kai asalima Bata fiya kallon sa ba.

Mafi yawan cin lokuta Yakan kamata tana satar kallon sa ,daya juya sai tayi saurin kawar da kai, murmushi kawai yake Dan shi wannan Al,'adar tana matukar bashi ma'maki.

Yau dai ya kudiri aniyar sai yaji muryar mahaifiyar sa kota wace hali.

Cikin dare ya tashi ya nufi dakin ta lokacin tana zaune tana lazumi da sallama yashiga Jin muryar sa yasa ta miki cikin sauri tace,"Kai lafiya?

Murmushi yayi ya samu guri ya zaune yace,"babu komai umma Ina so muyi magana ne.

Bata Musa ba Dan dama itama tana da bukatar hakan Zama tayi Dan nisa dashi tace,"Ina jinka.

KARSHAN WAHALA 2019Where stories live. Discover now