chapter 13

1K 94 1
                                    

KARSHAN WAHALA
By
Safnah aliyu jawabi
♒♒♒♒♒♒♒♒♒♒♒♒♒♒♒♒♒♒♒♒♒♒♒♒♒♒♒
♒♒♒♒♒♒♒♒♒♒♒  ♒  ♒ 
 
         Bismillahi rahamanin Rahim
     
nah fita na tarar da motar da zata fitar damu baban titi aikuwa Koda nashiga babu abinda nakeyi sai aikin kuka lokaci zuwa lokaci nakan daga kai Naga inda muke kasancewar bantaba fita daga kauyan muba,muna isowa bakin titin Naga mutane natai kaiwai da komuwa ma'maki ne ciki falcikin zuciya ta Dan banzata akwai mutane dayawa aduniyar Nan haka ba..

ba'dau lokaci ba muka samu motar da zatai kaimu acikin motar ma babu abinda nakiyi saikalle kalle alokacin ne basira yarinyar innata asabe tace,"kalle kallen me kike da bakince bazaki zoba,ashe dama gulmace.

Kasancewar ta girmemin shiyasa ban amsataba nacigaba da kalle kallen na duk da kasancewar inah taganin bukkuki irin namu, saidai wayan Nan suna da yawa haka daimuka cigaba da tafiya ba'adau wani lokaci maitsayi ba muka sauka, inah ji direbar motar nacewa,"hajiya mum iso dikko.

Cikin gadara lantana tace,"cemaka akayi bamu sani bane ko kauyawa ne mu?

Shima baiyi wata wata ba yafara Bata amsa kankace rikici yabarke agurin. direbar motar harda Mari yayiwa lantana nikowa inah gefe inaji wasu mutane suna cewa ," Kano kaduna zariya.

Bayan fadan talafa ne lantana tace mukwasu kayan mubita gurin mutanan nan ta nufa tana zuwa tace musu kaduna Nan take aka saka kayan mu amota kamar dama musuke jira muna shiga motar tafara tafiya,

nikuwa Wanda bantaba shiga mota ba muna shiga barci ya daukeni bansake farkawa ba sai danaji  basira ta bakamin duka tana cewa ,"kitashi munkai.

Afirgice na tashi inah salati nafito aikuwa inaganin gidaje masu tsayi dasauri na nufi bayan basira inah cewa ,"waiyo yaya zasufado Mana akai kitaimakini bana so na mutu nabar maimuna nasan zatayi kuka so sai..
Aikuwa banma kaida karasa maganar ba naji anbakamin duka,dasauri najuya Dan harnamance da lantana agurin.

Ciki da masifa take magana,"ki mahaukaciyar inane ?sokike kitara Mana mutane?tana cikin magana karamar wayan dake hannun tane yayi Kara da murmushi afuskar ta tadaga kamar ba'ita bace taketa masifa yanzu tace"barkanki da warhaka hajiya yanzu muka sauka, gamu Mai motar yasauke mu a I b b I yanzu zamu tari adaidai ta.

cikin mintina kadan tagama wayan sannan ta tare Mai adaidai ta tace," yakaimu tashar na Maggi.

Ba'adau lokaci Mai tsawo ba  muka sauka abakin wani tangamemen get.
Tsayawa fada muku yanda na tsaya inah kallon get din gidan ma bata lokaci ne,

abinda Baku sani ba shine har sunshige ciki karar motar da tazo wucewa ne yadawo da hankalina aicikin sauri na bi bayan su.
Muna isah akashigar damu cikin Fallon gidan gaskiya gida ne Mai tsananin kyau tsaya kwatanta muku kyawun gidan bata lokaci ne,muna zaune saiga wata mata tafito daga wata daki dake cikin falon, da fara'a tazo tazauna duk kanmu muka gaishe ta ciki da kulawa ta amsa tana kallon lantana tace,

"lantana wacece daga cikin su?

aikuwa batayi wata wata ba tanunani .
Nikuwa ganin annunani yasa nafara bari Dan dama atsorace nake.
Jinaya matar tana cewa,

" aikuwa tamin ya sunan ta?

Lantana tace,"safnah.

ciki da ma'maki ta kalli Ni tace,"Kai Amma nayi ma'maki ashe akwai kyawawa a kauyan naku haka, gasunan ta gunin dadi.

Lantana wace tunda akafara yabona taketa murmushi dantasan bakaramar kudi zata samu ba tace,"aisamun irin su safnah ko'abirni sai anduba.

Haka dai sukayita hirar su har yamma tayi lantana tamike tsaya tace,"to Ni zantafi Dan daga nan unguwar rimi zantafi.

Hajiya yanda naji lantana tana kiranta tamike tsaya tace,"Ina zuwa.
Ba'afi mintina biyar ba tadawo hannun ta rike da rafar dari biyar biyar ta mikawa lantana.cikin rawa jiki ta karba tana mata godiya.
Inah zaune naji lantana tana cewa,

" to safnah kiyi biyaya nadai fada Miki idan Kuma kika bari naji kinyi wani Abu narashin kyautawa wallahi saina lahira yafiki Jin dadi kindai ji nafada miki.

Cikin Rashin fahimtar inda maganar ta amsa da to.

Ta zaune taga lantana da basira sunnufi hanyar fita daga gidan,dasauri ta tashi tana binsu abaya hajiyar ce tace,"inah Kuma Zaki  safnah?

Jin tambayar yasa lantana juyawa aikuwa sukayi ido👀hudu da lantana cikin tsawa tace,

"inah Zaki ?

dasauri na amsa "Naga kunfitane shiyasa na biyoku,kibiyo mu kimana me aike kinzo kenan Nan gidan Zaki zauna .
Kankace me hawaye 😭 ne suke zuba babu kakkautawa tace,"Dan ALLAH innah lantana karku tafi kubarni anan Dan girman ALLAH.

gan lantana ku kallon inda nake batayi ba yasa na nufi basira nafara magana cikin kuka,"karki tafi kubarni kindai sancewa Ni yar'uwar kice ko,Kinga banida kuwa sai ku baki tunanin wayan Nan mutanan zasu'iya cutar miki da yar'uwa.

saukar Mari da naji ne ya hanani karasa maganar lantana nagani ta sake daga hannu da nufin kara Mari na.hajiyar ce tazo da sauri tarike hannun ta tana cewa,"kanme Zaki rinka Marin ta,sake hannun lantana tayi.
Ta nufo gurina tana rairashina tace,"kidaina kukan safnah babu abinda zaisameki anan nayi Miki alkawari zanrike ki tamkar yar'dana haifa acikin ciki na,sannan zakiyi karatu Kuma duk KARSHAN wata zankaiki kiga Innar ki.

dasauri na dago Kai na kalle ta jinayi tamin kurjini sannan da alamu bazatayi karya ba.
Haka dai inah kallo suka tafi ,mukuma muka koma cikin gida.

Muna shiga tarike hannuna ta kaini wani daki da alamu mamallakiyar dakin buduwar wace domin kuwa ko inah ka kalla hoton tane amanne sannan suna da kama da wannan matar ko ba'a fada maka ba kasan diyar tace.

Wani kofa Naga tabude tashiga sannan tace Nima nashiga, inah shiga Naga komai na wurin fari ne ga ruwa na zuba tawani karamar abu, ma'maki na baikare ba Saida Naga ta Murda wani abu nantake ruwa yafara zoba tasa hannu saida taga ruwan yayi daidai na wanka sannan tace ,

"kishiga kiyi wanka zanjira ki awaje, cike da razana nakalle ta nace,"wallahi hajiya bansan yanda zanyi ba Dan bantaba ganin rafi haka ba.duk da tasu rike dariyar Amma inah saida tayi Dan maganar yazo mata abazata tace,

"ba Rafi bane safnah kishiga kiyi wanka inah jiran ki Saida tanuna mata yanda zatayi sannan ta fita.
Aikuwa bayan fitan samun guri nayi nazauna Saida takara lekowa tac,"aubakiyi wankan ba?to kuwa nasauke alkawarin Dana miki tunda bazakiyi wanka ba.

Nandanan nashiga nafara wankan duk atsorace nake.
Banfi mintina biyar ba nafito duk da bawata wankan kirki nayi ba Amma Naga nayi haskee saka makon sabulu da nayi wanka dashi,Ina fitowa Tamika min wata doguwar riga baka sannan tace ,

"ga kayan kulliya can kidauka ki shafa sannan kifito kici abinci,Saida tanuna min yanda ake amfani dashi sannan tafita.tana fita nadauko rigar nasaka power kadan na murza afuskata sannan nabi hanyar da mukabi nafito,

tunkan nakarasa nakejin muryar su,inah saukowa ido kawai yake Bina dashi harna karaso gurin inah zuwa na,suguna harkasa nagaishisu sannan nakoma can bakin kofa na zauna.

haryanzu Ni yake kallo sannan yace,"binta wacece wannan? cikin murmushi tace,"honey itace yar'akin danace maka lantana zata zo Mana da itah.

cikie da ma'maki yake kallo na, azuciyar sa kiwa cewa yayi"Kai wannan tafi kama da matar gida bamai aiki ba.....

SAFNAH ALIYU JAWABI
(JAWABI)

Please don't forget to vote and comment dat...

*_If a relationship last longer than 10
"Years, is not just friends but family that  what  u  are*MAIMUNAT*
I  dedicated this whole page to you my dear friend.

*"ALLAH yasauki ki lafiya.yaraya Mana affan

KARSHAN WAHALA 2019Where stories live. Discover now