chapter 9

979 65 0
                                    

Tana isowa inda yake zaune tasamu guri tazauna tace,"sannu dazuwa malam."
yauwa sannu yagida?"

lafiya kalau,
ina ya'ya naki?

tana ciki"

Shidai yalura kamar akui abinda takeson fada mishi, Dan bata taba riga Laure fitowa ba, koda kuwa tariga ta ganin shiguwar shi.

Yadube ta yace "koda matsala ne Maryam kifada min meke damunke naga duk kin fada.

Kamar dama jira take ya tambayi ta aikuwa saiganin hawayi yayi sunan binjuna ganin haka yasa yanufi dakinta tana biye dashi suna shiga ya kalleta yace

"Kiwa ALLAH kifadamin damuwar ki Maryam

"Nantake tafada mishi duk abubuwan da suke faruwa harda zuwan lantana da ciwon cikin da laure tarinka yi dan taraba su.

Malam Yana Jin haka "yayi mata nasiha tare da karfafa mata guiwa akan kara hakuri da laure saidai daga ranar ya hanata cin komai daga hannun laure.

Jin shiru shiru da laure taji malam baidawo bane yasa tafita kofar gida tana lekawa.

Daidai lokacin Yana dawowa daga masalaci laure tana ganin jauro, tanufu shida sauri tana murmushi tace
"Sannu dazuwa malam.
"Yauwa sannu laure ya gida?
"Lafiya Lau bari nadauko maka abinci. Cikin sauri yace"kinga bar....

abincin nan akoshe nake wallahi,nabiya gidan dantani ance baiji dadin jikin shi ba, acan naci abinci.

"To ai ko kadan ne kadan kara.
"A a kibarshi gobe idan ALLAH yakaimu kwaci.

"To malam.harzata huce malam yace
"Nikuwa laure meke da munki naga fuskar ki tadan fada?

"A a wallahi bakomai malam kawai dai yanayin garin ne."to babu matsala ALLAH ya kyauta yakuma kara mana imani.

"Ameen malam.cikin saure tashige daki. Shikuwa ya nufi dakin maryam

****
Cikin dari Maryam ta tashi da wata masiffiyar ciwon ciki tun tana daurewa ,harya kai sada ta tashi malam.

Yana tashi yaganta sai zufa take cikin sauri yatashi Yana tambayar ta.
"Maryam lafiya?
Kawai nune tayi mishi da cikin
dan Alokacin ko magana bata iyawa .

Dasauri yanufi dakin laure tana budiwa "yafada mata Maryam tana nakuda, Nanda nan ta nufi dakin

shikuma ya tsaya awaje yanata kaiwa da komuwa yana ardu'a ALLAH ya fida Maryam, da abinda ke cikin ta lafiya.

Ba'afi mintina talatin da biyar ba malam yafara jiyu kukan jariri nandana yayi hamdala ga ALLAH,
daya azurtasu da abinda suka dade suna nima.

Cikin dakin kuwa bayan Maryam ta haihu Laure taga abinda ta haifa, kawai sai tunanin maganar da lantana ta mata ya fado zuciyar ta, aikuwa batayi wata wata ba tasa fello ta rufe mata hanci bata cire ba saida taga tadaina numfashi.

Nandanan tasa kuka tana cewa,
Innahlillahi wa'inna ilaihi raju'un, maryam ALLAH yajikan ki yasa mutuwa hutu ce ga mumini.

Jin haka yasa yashego dakin dasaure yanason gasgata maganar.

Yana zuwa ya nufi gurin da Maryam ke kwance babu alamar rai atatare da ita.
Nanya yanke jiki yafadi ko mutsi bayayi,
Waiyo jama'a ataimake ni ALLAH yayiwa malam da Maryam rasuwa.

Kankace mee jama'a suncika gida
Nandanan aka saftace gawar Maryam.
Sannan aka tabbatar malam jauro yana raye duguwar suma yayi.

Karfi tara na safe aka sallace gawar Maryam aka sadata da gidan ta na gaskiya. Har lokacin malam jauro baisan inda yake ba,Saida

Yamman ranar ya farfado tare da taimakon malam dantani,Dan tunda aka dawo daga makabartar yake zaune Yana mishi ardu'a Yana shafa mishi harya farfado.
Bayan ya farfado yake tambayar dantani

"Shinda gaski ne Maryam ta rasu? cikin kuka yake tambayar

Nandanan ya tabbatar
Mishi da gaskiya ne tarasu sannan yayi mishi nasiha Mai ratsa jijiyuyun ji.
****
Haka dai rayuwa taci gaba da tafiya tun bayan suna yarinya taci sunan mahaifiyar malam jauro,safina Amma ana kiran ta SAFNAH

aka barwa laure jaririyar tana bata madara tun tana kuka har tasaba
Shikuwa malam jauro haka dai yake tafiya yau ciwo gobe lafiya,

Safnah takasance yarinya mai farin Jini agurin jama'ar gari, kasancewar ta fara kekkewar gaski.
tun tana da wata shidda ta gane mahaifinta, kasan cewar idan Yana gida to tana gurin shi kuda fita zaiyi saidai yayi sanda,Dan karta ganshi

Ahaka hartakai shakara hudu cikin wanna shikarun kuwa ,taga abubuwa da dama na wahala dangin su duka yunwa.

Ahaka wata rana laure nazune taga bera tahuce ta gabanta harsaida ta tsora ta.
Aikuwa zanyi maganin ku,bari na saka muku magani kuci ku mutu Kona samu sauki, ta dauko farantin da take zubawa safnah abinci ta zuba maganin aciki sannan ta tura shi karkashin gadon ta tafito tana barar agushi.

Ba'afi mintina biyar da fitowar taba SAFNAH ta tashi daga barci tana saukowa daga kan gadon taga abincin aikuwa ta dauka tafara ci dama ga yunwa na damunta Bata idah cinye abincin ba cikin ta yafara juyawa tana Kiran umma umma.

Laure dake waje tana jinkiran tayi kamar bata jiba tana cewa,sai kiyi ai yarinya sai shaggubar tsiya,saiki jira uban nake idan yadawo yazu yasaukar dake.

Kafin kace mee tuni harta sume kunfa na fita daga bakin ta.

Bayan malam jauro yadawo yaga baiganta atsakiyar gida ba kuma baiji mutsinta taba.

"Waini kuwa ina yar baba naji ta shiru?

"Tana ciki tana barci

Kai laure kidaina barin ta tana barcin magrib,bashi da kyau saikiga yasakar mata zazzabi,
Malam jauro yana shiga yaji kafar sa tadan daki abu aikuwa Yana dubawa yaga safnah ko motsi batayi babu alamun Rai ajikin ta ga kunfa na fitowa daga bakin ta.

Ai malam baisan lokacin da ya sunkuce ta yayi hanyar waje da ita ba yana Kiran Laure ta mutu ki taimakeni

SAFNAR KU HARKULLUM 🍡🍡🍡🍡🍡🍡🍪🍪🍪


KARSHAN WAHALA 2019Where stories live. Discover now