page 18

1K 86 1
                                    

*KARSHAN
WAHALA*

~By safnah aliyu jawabi*
(JAWABI)

~Brightest hope wirtter ass*

Don't be silent friends please tell me what you all think about my novel*

Please
Follow
Comment
Vote
And
Shere
With
Your
Friends

Love you all friends 🖤🖤🖤🖤🖤🖤

Bismillahi rahamanin Rahim

Jameel nagani rike da liltatafai ahannun shi wasu zafafan hawaye suka fara bin kuncina.jinnayi shiru yasa afeeya saurin juyowa da ma'maki karara akan fuskar ta tafara tambaya ta,"meya faru safnah meke damunki?

kasa rike kukan nayi dasauri na nufi get din makarantar nayi sa'a kuwa phrepet Basu Fara kama let ba Dan idan suka fara to kokai Dan gidan waye bazasu Bari kafita daga makarantar ba.

Gudu nake inah kuka da duk kannin karfi na, afeeya kuwa bina take tana Kiran sunana Kiran da takemin ne yajawo hankalin malam makarantar harda dalibai cikin malaman kuwa harda Jameel wanda lokaci daya yashiga damuwar da shi kanshi baisan dalili ba, take ya yanki shawarar Bina Dan jin abinda yake faruwa.

sannan yasa aka tsayar da afeeya,zuwa lokacin kuwa harna karaso baking titi Dan babu nisa tsakanin titi da makarantar,anyi sa'a kuwa inah zuwa nasamu nappep bantsaya wata wata ba nafada mishi inda zaikai ni.

muna barin wurin Jameel da sauran daliban da suke biye dashi suka karaso inah kallon yanda yaka hada zufa saboda gudun da sukayi, nantake na fasa kuka maiban tausayi Dan nikadai nasan yanda nakeji game dashi saidai Kash anyi rashin sa'a domin kuwa shine Wanda afeeya ta dade tana mafarkin mallaka.

Kuka nakeyi harmai adaidai sahun Saida ya tausayamin duk da yayi yayi na fada mishi matsala ta nace bakomai,inah sauka namika mishi kudin da daddy yake bamu kullum idan zamu tafi makaranta Amma samyaki karba haka nashiga gida Yana daga min hannun.

Inah bude get muka hada ido da mummy Dan idan banmantaba tafada Mana cewa bazata fita da wuri ba.
Tana ganin na dasauri ta rikoni tana tambayata dalilin dawowa na gida awannan lokacin.

sambata lura da yanda idanuwa na suka chanza launi ba sai alokacin cikin sauri ta sa hannu ta dago habbata tana tambaya ta,"meke damunki safnah inah afeeya? Hadiye kuka daya tasomin nayi sannan nabata amsa "mummy tana makaranta nidinma kainane kemin ciwo shiyasa na dawo.

Kallon tausayi tamin sannan tace"assha sannun kishiga ciki ki sha magani ki kwanta kinji Yar'mummy.

Nod da Kai kawai nayi harzan wuci naji ta rikoni sannan tasa hannun ta dukka biyu ta riko kunnuwana cikin sigar wasa tace"Yar'mummy kidaina kuka idan wani Abu Yana Miki ciwo kinji bakisan kin girma ba Nanda Dan wani lokaci Zan aurar daku Gabaki daya IN SHA ALLAH .

tana gama fadin Haka ta jawoni jikin ta tarungume sannan tace nashiga gida sauri sauri gudu gudu nashiga gida Dan kuka yagama cin karfi na
*******
Shikuwa Jameel sauke ajiyar zuciya yayi sannan ya juyo danufin komawa makaranta ganin Haka yasa sauran daliban suma suka juya kowa da abinda yaka tunani gameda abinda yafaru cikin su kuwa Jameel yafi kowa shiga damuwa .

Dan shikadai yasan irin abinda yakeji idan yaga yarinyar Haka Yarinka kallon ta jiya saidube dube take yarasa metake Nima kodai wani take Nima kodai tana da saurayi ne dasauri ya kawar da wanna mumunar hasashan daga zuciyar shi.

KARSHAN WAHALA 2019Where stories live. Discover now