Sai asannan ta tuna da bakin dake jiran ta, ai cikin sauri ta zai yana mata halin da ake ciki da kuma yanda ta shiga ta same inna laure.

Daure fuska maimuna tayi tace,"kedai bazaki taba canzawa ba Ni matsamin.

Daki ta shiga ta dauko ta barma Mai kyau ta shimfida sannan ta debo ruwa Mai sanyi cikin kwarya ta ije samar tabarmsr.

Ajiyar zuciya ta sake tace,"sai kije ki shigo dasu kafinnan in dama musu fura.

Murmushi tayi tace,"Ina alfahari dake,kice mutum na farko dake Sona domin ALLAH cikin duniyar nan.

Murmushi maimuna tayi tace,"idan kin gama dadin bakin nake saiki tafi.

Tuno dramar su ta dazo yasa *SAFNAH*ta fashe da dariya tana cewa,"lallai dole ki samu bakin magana yanzu ai dazu kuka kike jikin ki kuwa kamar mazari Dan tsoro.

Rarumar takalmin ta tayi ta jifeta dashi,da gudu *SAFNAH*ta fita tana dariya harda rike ciki,ahaka harta karasa gunsu mom.

Ganin ta ahaka bakaramar faranta ran su yayi ba,iso tayi musu zuwa cikin gidan,suna shiga gidan mom ta sauke ajiyar zuciya Danko babu komai gidan ya burgeta ga gidan tsaftsaf da alama masu gidan suna da tsafta.

Da fara'a maimuna take musu sannun da zuwa harsuka zauna.

Cup Mai kyau da tsafta ta dauko ta ije saman kwaryan tana cewa,"bismillahi.

Suwaiba ce ta fara diba tashi tace,"Kai Kai mom ruwan kamar ruwan fanfo,Kuna da fanfo ne a kauyan Nan?

Tambayar ta zowa maimuna abazata shiyasa ta danyi jinkirin amsawa dan agaskiya bataji dadin maganar ba musamman ma*SAFNAH*

Tsawa mom ta daka mata tace,"ke ki kiyaye ni da wannan shigen surutun tsaya da kika saba,Kai kallon ta gun da maimuna da *SAFNAH*suke tayi tace kuyi hakuri, ke*SAFNAH*kinsan halin ta bawai ta fada da wata manufa bane.

Murmushi maimuna tayi tace,"Wallahi babu komai mom yanda taji*SAFNAH*ke kiran ta.

Hakan kuwa yayiwa mom dadi Dan ita akwaita akwai son yara.

Adaidai lokacin maimuna ta gama Dama furan ta mika wa*SAFNAH*ita kuwa ta ije musu kowa da kwaryan sa.

Mom ce tafara Sha wanna karon tana kaiwa maki taji wani irin gardi hade da dadi sun mamaye ilahirin bakin ta.

Murmushi tayi tana cewa,"godiya Mai tarin yawa my daughter furan Nan yayi dadi.

Ga ma'makin ta sai taji maimuna ta amsa da cewa,"Thanks alot mom.

Kallon ta duk suke cike da ma'maki Dan Basu taba tunanin akwai Wanda yayi makaranta cikin wannan kauyan ba.

Saida suka sha sukayi nak sannan*SAFNAH*ta gabatar da maimuna agare su Suma ta gabatar dasu daya bayan daya.

Ganin haryanzu babu wani babba daya fito daga cikin dakin da suke zatton fitowar mace ko namiji yasa mom tayi gyarar murya tace,"maimuna my daughter mama ta fita ne?

Sosa Kai tayi tace," ooo kuyi hakuri Dan ALLAH zumudin ganin tane yasa na mance tun safe Inna ta tafi gidan suna Amma Ina kyautata zatton tana hanya yanzu IN SHA ALLAH.

KARSHAN WAHALA 2019Where stories live. Discover now