Jin sallama yasa ta juya tare da amsa sallaman,ganin Jameel yasa tayi murmushi tace"a a harka iso kaman kuwa kasan KU kawai nake jira.

Cikin rashin fahimta yake kallon ta yama kasa cewa komai,gani haka yasa ta shiga ciki ta dauko mishi fararan wasikar da *SAFNAH*ta umarce ta data basu.

Kallon ta yake yakasa karban takardan sai binta da kallo yake,gani. Haka yasa tayi murmushi tana cewa,"malam Jameel ka karba mara lafiyar kuce tace na baka kaida afeeya.

Karba yayi jiki asanyaye jingina yayi da bango Ciro takardan yayi wacce ke dauki da sunan sa yafara karantawa kamar haka..yaya jameel Ina Mai baka hakuri akan hukuncin Dana dauka batare danayi la'akari da halin dazaka tsince kanka aciki ba,kasani Ina kaunar ka, kaunar ka tafara ne tun daga ran farko Dana fara ganin ka arayuwa ta kuma Ina Mai tabbatar maka da sonka zan koma ga mahalilci na,Amma kasani Ina mattukar son afeeya domin tamin hallalci Wanda bazan iya saka mata da butulci ba, kayi hakuri kayi hakuri sannan karka damu da inda nake domin kuwa ina tare da yar'uwar ta wacce muka zo garin tari ma'asalam .

Sulalewa yayi agun jikake dam akasa kansa ya bugu da wata kujera dake gurin karar faduwar Abu da Mustafa yaji ne yasa ya fito daga dakin cikin sauri Dan gabaki daya bai dauka wani abu bane yake faruwa rashin ganin *SAFNAH*adakin kuwa baisa yayi tunanin komai ba ya dauka ta Dan fita ne shiyasa daya ji shi shiru bai leka ba,Yana ganin Jameel kwanci ko alamar Rai babu ajikin shi, cikin sauri da taimakon ma'aikatan asibitin aka dauke shi sai gurin likitan.

Saida suka shafe kusan awanni biyar akansa sannan suka fito dashi zuwa dakin hutu izuwa lokacin kuwa ya hallara cikin asibitin cike harda afeeya da iyayan ta harda daddy domin kuwa ya gane kuran sa yazo kenan daniyar rokun gafarar ta shine yaji wannan mummunar labarin.

Nusaiba matare suke da ummin ta, rukkaya da aunty Khadija duk suna gurin duk wacce ka kalla kasan suna ciki tashin hankali musamman ma afeeya, wacce take ganin ta rasa kawa aminiya kuma yar'uwa, ga kuma saurayi Yana ciki halin rayuwa da mutuwa

Kara fashewa da kuka tayi tana cewa," my sweet*SAFNAH*ki dawo domin ni (Dan ALLAH)kinsan kece sirri na duk wani abu daya dangance Ni tare mu keyin abinmu,mu birne batarda wani ko wata sun sani ba,shine yanzu Zaki tafi kibarni,kin min adalci kenan?

Rarrashin ta mummy take yi ganin abin nata yana niman huce gona da iri (NI KUWA SAFNAH ALIYU JAWABI ina daga gefe nace"kedai bari mummy bazaki gane bane harda kukan sirikin ki afeeya keyi bana safnah kawai bane lol 🤣🤣 🤣)

Likita ne ya fito cikin sauri "Mustafa yatare shi yana tambayar shi jikin Jameel"

"To alhamdulillah likitan "yace tunda mun samu komai yadawo daidai, wanda ayanzu baza mugane ko dawata matsalar ba saiya farfado wacce bama fatan samu da yardar (ALLAH)

Alhamdulillah suka ce atare sannan suka nime dasu shiga suganshi, dakatar dasu likitan yayi yace" su bari saidan anjima, saboda anfiso ya farka da kanshi gudun samuwar wata matsala.

"Gefe daya suka samu zuka zauna, ummi nusaiba ce tafara tafiya tare da fatan samuwar sauki ga Jameel,sanna. Rukkaya da aunty Khadija Suma suka tafi da alkawarin dawowa gobe su duba shi.

Bayan tafitar su yarage daga Mustafa sai afeeya da iyayan ta suna zaune suna jirar farfadowar shi,gani har anyi sallar isha'i bai farfado ba yasa likitan ya kara duba shi tare da mishi wasu allurar.

Cikin ikon ALLAH ko cikakkiyar mintina biyu ba'ayi ba yafara juye juye ta sowa sukayi suna mishi sannu ahankali yafara bude idon sa harya bude gabaki daya,kallon dakin yake yana tunanin dalilin ganin kansa anan.

Kiran sunan shi da Mustafa yayi ne yasa yadawo da kallon sa kansu Yana binsu da kallo.

Jameel Mustafa yakara Kiran sunan sa akaro na biyu, Amma babu alamun amsa saima binsu da kallo daya yi makar bai sansu ba,ganin haka yasa Mustafa Kiran likatan.

Atare suka shigo da likitan dubashi yashiga tare da mishi tambayoyi akan yanda yake jin jikin shi,maimakon amsa saiya jawo hannun likitan Yana tambayar shi dalilin zuwan sa asibitin, sannan su waye wayannan mutanan dake zagaye dashi.

Jin kalaman Jameel yasa afeeys ta fashe da wani kuka Mai sauti,ganin haka yasa likitan yace"suje waje za suyi aiki.

Mustafa ne kawai aka bari acikin,cikin dabara likitan yace,"malam Jameel dake haka yaji suna Kiran shi yace"shin ko kaga ne wannan?tare da nuna Mustafa.

Girgiza kai yayi tare da cewa,"likita na fada maka cewa duk kansu babu wanda na sani wallahi Jin hakan bakaramar tayar wa Mustafa da hankali yayi ba Dan har kwalla ya zubar Amma ba Mai sauti ba.

"Likitan ne ya tabbatar mishi da akwai matsala gaskiya sai an kaishi dakin daza'a duba lafiyar kwalkwalur sa Dan gane inda matsalar take,amma saidai gaskiya akwai kashe kudi dayawa.

Tashin hankali iya tashin hankali mustafa yashiga Dan baisan inda zai samu wannan ma kudan kudin da likitan yake da bukata ba amma saida daure yace"likita harnawa ake da bukata?

To agaskiya zai kai kamar dubu dari biyu, domin kuwa yanda naga yake yi da alama yayi loosen memory nashi amma idan muka duba muka gane za musan abinyi tunda atsarin baidade da faruwa ba.

Zufane ya fara karyowa mustafa, nan danan yayi hanyar fita batare da ya kuma cewa komai ba, koda yafita afeeya take tambayar sa ce mata kawai yayi yana zuwa. .

Shin;me hakan ke nufi shin niman kudi Mustafa yafita ko kuwa guduwa yayi ganin bashi da halin biyan wannan ma kudan kudin da ake bukata?

Waye Jameel ya matsayin Mustafa agun Jameel.

Wani taimako afeeya zata baiwa masoyin ta?

Ya kuke ganin taraiyar *SAFNAH*da *NASIR*?

Ya labarin Mai buhun kudi da wacce*SAFNAH take kira Inna?

Ya al'amarin sumaiya da basi?
Hajiya da kawarta larai.

To KU kwantar da hankalin ku, don jin yanda zata kasance muhadu ashafi na gaba LOVE YOU all




KARSHAN WAHALA 2019Where stories live. Discover now