Jameel kuwa banda kiran layin Mustafa babu abinda yake yi ringing take yi amma ba'a dauka ganin bashi da wata mafita face zuwa gidan da Mustafa yake,dan adaidai ta ya tsare cikin mintina kalilan suka isa, sauka yayi ya mika wa dan adaidaita kudin batare da yatsaya karbar canjin saba ya shigewarsa cikin gidan.

Yana shiga daidai lokacin Mustafa ya fito daga wanka ko sallama baiyi ba ya shige cikin dakin, ganin shi cikin wannan yanayin ba karamar tsoro abin ya bashi ba, tambayar shi ya shiga yi amma ina Jameel babu bakin magana janyu jallabiyar sa mustafa yayi ya saka ai Jameel jiyayi kamar an sakar masa baki.

Tashi yayi ya ca kume Mustafa yana zazzaro ido yace,"Mustafa kafada min gaskiyar abinda safnah ta fada maka awancan ranar kafada min.

"Kamar ya? sakarmin riga.

Kin sakewa Jameel yayi ganin abin bana wasa bane yasa Mustafa ya cire hannun Jameel ajikin sa sannan ya zaunar dashi, bashi labarin yanda sukayi ya shiga yi ai Mustafa baika ga karasa zancan saba Jameel ya fashe da kuka yana cewa,"ka cuceni Mustafa ka cuce ni.

Kasa fahimtar inda zancan Jameel ya nufa yayi.

Saidai duk yanda akayi yasan da wata akasa.

Tashi yayi ya dauko wata jallabiyar ya saka dan wancan bazata sahu ba,hannun Jameel ya rike da niyar su tafi asibiti ayita ta kare amma saidai gabaki daya jikin Jameel yayi wani irin zafi cikin sauri Mustafa ya cire hannuwan sa kallon Jameel yayi yace,"baka da lafiya ne Jameel?

Jameel dai yana zaune baice komai ba,ruwa Mustafa ya debo ya mika wa Jameel hada da magani da farko kin karba yayi Saida Mustafa yayi mishi jan ido sannan yasa hannu ya karba,yana gama sha ya kwanta.

Mustafa safnah ta kamu da ciwan zuciya kuma ina da tabbacin dalilin soyayar da take min ne, menayi maka dana cancanci irin wannan hukuncin eye?

Shiru Mustafa yayi dan gaskiya shi kanshi ba karamar kaduwa yayi dajin Wannan labarin ba saidai ya nuna jarumta dan kar ya karyawa abokin sa gwaiwa dakewa yayi yace,"

Karka damu Jameel haryanzu da sauran lokaci zamu iya gyara komai ta hanyar afeeya domin kuwa yanzu ita kadai ce matsalar.

Cikin sauri Jameel ya mike kamar bashi bane yanzu cikin wani irin yanayi ba,jin an ambaci da akwai mafita,dafe kafadar Mustafa yayi yace,"to me muke jira mutafi asibiti tun yanzu ba'sai anjima ba.

Cire hannu wanshi yayi cikin wasa yace,"babu inda zan tafi bayan yanzu ka gama cimin mutunci me kuma zanje na maka acan.

Hakuri yabashi sukayi dariya lokaci daya.
💖💖💖💖💖💖💖💖💖

Safnah aliyu jawabi

💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖

Basi tana fitowa daga toilet kasa hada ido da sumaiya tayi ita kuwa tana ganin fitowar ta cikin sauri ta rungume ta tana shin shinar ta saida ta gama sannan ita ma ta fada toilet tayi wanka saida suka gama shirin su tsaf harzasu fita wayar basi yafara ringing dauka tayi number mai buhun kudi ce cikin kasha murya suka fara magana cewa yake,"kiyi hakuri kinji ni shiru ko?

Wallahi ina fita aka min waya oga na yana son ganina a lagos shine na tafi amma kiyi hakuri ki shirya ki tafi duk yanda ake ciki saiki sanar dani.

KARSHAN WAHALA 2019Where stories live. Discover now