Shiru nayi dan sai alokacin na fahimci rukkaya bata gane daddy ba,godiya ga ALLAH nayi dan dama tunani na bai wuce yanda afeeya da mummy zasu dauki al'amarin ba,karya nayi musu kancewa niman bansan yanda akayi ya shigo ba sai ganin shi kawai nayi.

Ana cikin haka saiga afeeya da mummy sun shigo cikin dakin kallo daya za kayi musu ka fahimci tashin hankalin da suka shiga,da gudu na rungume afeeya ina kuka,ita dinma kuka take tace,"ya akayi haka ta faru?muje asibiti kinji safnah ta.

Girgiza mata kai nashiga yi sannan nace,"babu abinda yasame ni ALLAH ya tsare ni da tsarewar sa.

Godiya sukayi wa ALLAH sannan suka yi godiya ga mutanen da suka kawo musu agaji.

💖🌺💖💖🌺💖💖
🌲🌲💮🌲🌲💮🌲🌲
💖💖
💞🌲💞💞🌲💞💞🌲💞💞
💖💖💖💖💖💖💖💖💖
🌲🌲🌲🌲🌲
💮💖💮💮💖💮💮💖💮💮
💝💝🌺💝💝🌺💝💝🌺💝💝
💖🖤🌲🖤🖤🌲🖤💖
🌲💖💖🌲

KARSHAN WAHALA
By
Safnah
Aliyu
Jawabi

Mrs ABDULLAH IN SHA ALLAH🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲

Lamarin Jameel kuwa abu ya ta'azzara domin kuwa dauriya iya dauriya yayi akai na amma ina abin yaci tura,yau ma zaune yake yayi shiru babu abinda yake tunani illa safnar sa.

Shigowar da mustafa abokin Jameel yayi ne ya katsa masa tunanin da yake,mika mishi hannu mustafa yayi sukayi musabaha sannan yace,"kai malam lafiya naga ka nimi guri ka zauna kai kadai?

Girgiza kai Jameel yayi yace,"kai dai bari kawai aboki na wallahi na hadu da jarabawar rayuwa.

Da ma'maki afuskar sa yace,"kamar ya bangane ba?

Wallahi kuwa abokina wata yarinya na hadu da ita amma wallahi kwata kwata na kasa fada mata irin matsanan cin son da nake mata.

Dariya mustafa ya fashe dashi lokacin da Jameel yagama bashi labarin haduwar sa dani sannan yace,"amma anyi sakarai kai yanzu d girman ka da waye war ka amma ka kasa fada wa mace kana sonta.

Sauke ajiyar zuciya Jameel yayi sannna yace,"kai dai bari wallahi yarinyar akwai shegen kwarjini,shiyasa na kasa fada mata amma tunda gaka yanzu saika fada min yanda za'ayi na shawo kanta.

Murmushi yayi sannan yace,"bakace tana da aminai ba?

Eh.

To ta hannun su yakama ta mubi dan ganin hakanmu yacinma ruwa.

To saida ba'anan gizo ke saka ba aminan su biyu ne,aciki waya kaga ya dace mu yiwa zancan?

Ajiyar zuciya Jameel yayi sannan yace,"ina ga mu fadawa afeeya dan sunfi ku sada juna.

To babu matsala gobe idan zaka tafi makarantar sai mutafi tare ko angon safnah.

Duka Jameel yakai mishi cikin wasa yace,dadi na dakai zulaya wato tunma bata amsa ba harna zama ango ko?

Kai kuwa kama daina saka kukunto acikin ranka domin ina mai tabbatar maka babu wata mace da zaka ce kana sonta ta ki amincewa da bukatar ka.

Kaiya domin wannan ko a cikin mata ina mai tabbatar maka tabanban ta.

"KO to ALLAH yakai mu na ganewa idona.

Haka dai suka cigaba da hira duk dai akaina.

💞💞💞💞💞💞💞

Al'amarin basi kuwa tun bayan faruwan wannan al'amarin, ta shiga taka tsantsan da mai buhun kudi duk abinda yake idonta na kai dan tun daga wannan ranar ta daukar wa kanta alkawarin rabuwa dashi dan ita kam bazata yarda ta salawantar da rayuwar ta adalilin sa ba.

Tana zaune taji mai gadi ya wankale kofar gidan get din gidan cikin sauri ta gyara kwanciyar ta sanin cewa babu wanda ke zuwa gidan sai shi.

Saidai mee karar tsinin takalmin da ya karade gidan yasa taye saurin mikewa kirjinta na dukan uku uku.

Mamallakiyar takalmin na hango duguwace sosai launen fatar ta fara ce tana da kananun ido da faffadal hanci kanta kuwa yasha gyara ansaka mata gashin doki sai sheki take.

Cikin gadara da nuna isa ta karaso gaban basi ta tsaya ganin tsayuwar bazai wadatar da ita ba yasa ta fara zagaye ta tana taunar cingam.

Bakaramar karfin hali basi tayi ba tace,"malama lafiya kika shigowa mutane gida,wacece k..

Saukar mari data jine ya hanata karasa maganar,rike kuncin ta taye, sannan ta daga hannuwan ta da niyar ramawa saidai tune sumaiya ta rike hannun ta juya tana cewa,"ko ubanki bai isa yayi jayaiya dani agarin nan ya kwana lafiya ba bare ke karamar alhaki,gargadin ki nazo nayi akaro na farko,kar ki yarda na kara ganin ki tare da mai buhun kudi idan ba haka ba duk abinda ya biyu baya kiyi kuka da kanki.

Tana kaiwa nan ta miki tayi gaba tana sake jaddada mata gargadin da tayi mata.

ajiyar zuciya basi tayi okacin da taji fitar motar sumaiya daga gidan sannan tafara tunanin mafita.

Ita kuwa sumaiya tana fita daga gidan ta samu guri abakin hanya tayi parking,ji tayi kanta na sara mata dan gabaki daya bakaramar dimauta ta surar basi yayi ba,gabaki daya jitake bazata iya kai kanta gida ba,cikin tsaki ta Ciro wayar ta ta danna layin naima kawar ta.

cikin mintinan da basu wuce goma zuwa sha biyar ba,naga wata zazzafar yarinya ta sauko daga adaidai ta sahu,fara ce sal da ita bata fiya tsayi ba sannan baza'a sakata asahun gaje ru ba.

Motar sumaiya ta nufa tana zuwa ta bude farfin motar ta shiga, bude idonta sumaiya tayi wanda ayanzu suka kada sukayi jajir tana ganin ta ta janyo ta jikin ta wani irin kiss take mata wanda daga gani kasan amatsanan cin bukace take ita dinma mayar mata da martanin take ta yanda duk su biyu din cikin mintina kalilan suka fita data daga cikin haiyacin su.

Naima ce tayi karfin halin cire bakin ta daga nata sannan tayi mata nuni da abakin hanya suke.

Fisgar motar tayi suka bar gurin ,suka nufi gida.

Kuyi hakuri da wannan babu yawa
Love you all.

KARSHAN WAHALA 2019Where stories live. Discover now